Sakonnin Masu Karatu (2016) (15)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

183

Salaamun alaikum, don Allah yaya zan yi karatu “online” na kwamfuta ba tare da na je ko ina ba? Sannan ta yaya ake gina gidan yanar sadarwa, wato: Web Site? – Mubarak Sani: mubaraksanicmp15109@gmail.com  

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Mubarak Sani, da fatan kai ma kana lafiya.  Lallai akwai shafuka ko ince “Makarantun” koyon ilimin kwamfuta kyauta a Intanet.  Wadannan makarantu ko wurare dai sun kasu kashi-kashi; akwai na kudi, akwai na kyauta, akwai wadanda bayanan a rubuce suke – sai ka karanta – sannan akwai wadanda suke dauke da bayanan bidiyo ne tsantsa.  Sai dai wani abu kuma, galibinsu, kashi 90 cikin 100, duk da harshen Turance suke.  A wasu shafukan kuma, dole ne kayi rajista kafin ka fara daukan darasi.  Wasu shafukan na bayar da takardar shedar gama karatu, wasu kuma ba su bayarwa.  Wasu na dauke da wuraren gwaji, wasu kuma ba su da wuraren gwaji, sai dai kayi amfani da kwamfutarka.

Duk da ba dai ban san wani bangare kake son koyo ba, shafin da yafi kowanne shahara kuma yake baiwa masu bukatar koyon nau’ukan ilimi daban-daban (ba wai na kwamfuta kadai ba), shi ne shafi mai take: “Tutorials Point.”  Wannan shafi ko makaranta tana dauke ne da rubutattun darussa da suka shafi fannoni daban-daban na ilimi.   Duk wani fanni na kimiyya da kere-kere za ka iya koyonsu a wannan shafi kyauta.  Kusan dukkan fannonin ilimin kwamfuta za ka iya koyonsu a wanan shafi.  Sannan shafi ne dake koyar da kai a tsarin mataki-mataki; daga farko har zuwa karshe.  Adireshin wannan shafi dai shi ne: www.tutorialspoint.com.  Kana hawa shafin daga sama sai ka matsa: “Tutorials Library,” don zaban fannin da kake son koyo.  Ko kuma ka gangara can kasa, za ka wani dogon jadawali mai dauke da dukkan fannonin da za ka iya koyo a wannan makaranta.  Duk na nuna cewa makaratar na dauke ne da rubutattun darussa, sai dai akwai bangaren darussan cikin bidiyo, sannan akwai bangaren kwatanta abin da ka koyo, idan ilimi ne mai dauke da koyo a aikace.  Misali, idan bangaren gidan shafin yanar Intanet kake son koyo (Web Design), akwai bangaren da za ka je ka kwatanta abin da ka koya a aikace, ba sai kana da kwamfuta ta kashin kanka ba.  Kana iya samun wannan wuri a shafin farko daga sama, can bangaren dama, mai take: “Coding Background.”

Idan kana son kuma inda zaka koyo nau’ukan kwamfuta musamman yadda ake gina manhajar kwamfuta ne (Programming) ne kai tsaye, daga farko har zuwa karshe, tare da takardar shedar karatu (Certificate), duk a kyauta, sai kaje shafi mai take: “Solo Learn.”  Wannan makaranta na daga cikin makarantu dake karantar da ilimi cikin sauki, tare da hanyar kwatanta karatun, cikin sauki.  Ba ma wannan kadai ba, ana karantar dakai ne mataki-mataki, cikin tsari mai dauke da nishadantarwa da saukin fahimta.  Ba a cika ka da tarin bayanai.  Rubutattun bayanai kadan ne, sai misalai birjik.  Cikin kankanin lokaci za ka koyi ilimi mai yawa, wanda ke dauka da dabbakawa.  Idan ka gama karatun nan take za a aiko maka da takardar sheda ta adireshin Imel dinka.

Amma dole sai ka yi rajista kafin ka fara daukan darasi.  Idan nace rajista ban nufin biyan kudi.  A a.  ina nufin za ka bude “account” ne.  Idan kuma ba ka son bude wani “account”, kana iya hawa da adireshinka na “Facebook” ko “Gmail,” kai tsaye, a duk sadda ka tashi shiga.  Bayan dukkan wannan, kana iya saukar da manhajar wannan makaranta a wayarka daga cibiyar “PlayStore” na wayoyin Adroid, sai dai kuma dole ne sai kana da Intanet za ka iya hawa a kowane lokaci.  Adireshin wannan shafi yana:  www.sololearn.com.

A daya bangaren kuma, akwai shafukan koyon ilimi ta hanyar bayanan bidiyo, su ma kyauta.  Wannan na samuwa ta hanyar shafin “Youtube” na kamfanin Google.  Wannan shafi na Youtube dai wata duniyar ilimi ce, mai dauke da kusan “kowane” nau’in ilimi kake bukata ko abin da ya dangance shi.  Jakar magori ce!  Idan kana da wayar salula irin ta zamani mai iya mu’amala da fasahar Intanet, to lallai baza ka rasa samun manhajar Youtube a kan wayar ba.  Ko dai ya zama wanda wayar tazo dashi ne (musamman idan Android ce), ko kuma ka same ta a cibiyar Play Store ko Store, idan nau’in “Windows Phone” kake amfani da ita.

- Adv -

Idan kuma da kwamfuta kake son hawa shafin, kana iya shigar da: www.youtube.com.  Da zarar ka hau, a sama daga tsakiya akwai inda aka tanada don yin “tambaya” (Search) kan nau’in ilimi ko bayanan da kake bukata.  Kada ka mance, galibin ire-iren wadannan ilimi dai cikin harshen turanci suke.  Don haka, duk tambayar da za ka yi ta zama cikin harshen turanci ce, kan wani fanni na ilimin kwamfuta kake son koyo.  Kana tambayowa kuma za a baka amsa bila-adadin.

Wadannan su ne wadanda zan iya baka shawarar ka lazimta a halin yanzu.  Ba wai iyakansu ba kenan, a a, suna da yawa.  Aika maka dandazonsu zai rikitar da kai, har ka kasa tabbatuwa a kan guda daya.  Idan ka lazimci wadannan, ka fa’idantu, da kanka za ka nemo kari, ba sai ka sake tambayar wani ba.  Allah sa a dace, amin.


Salaamun alaikum, da fatan kana lafiya.  Don Allah ina so a sanar da ni hanyoyin da zan bi wajen koyon ilimin hada alaka tsakanin kwamfutoci, wato: “Networking”, dan Allah Baban Sadik.  Na gode.  Sharhabil Aliyu: saliyudan11@gmail.com

Wa alaikumus salam, Malam Sharahbil da fatan kana lafiya.  Ina kara baka hakuri sanadiyyar yawan tuntubata da kake yi kan amsar tambayarka.  A yau dai Allah Ya yi; ga amsar tambayarka nan a sama, kamar yadda in har ka karanta wannan shafi a yau, na san ka samu bayanan.  Kana iya bin wadancan hanyoyi da nayi bayaninsu a tambayar dake sama, don cinma burinka a wannan fanni da kake son koyo.  Bayan haka, ka duba akwatin Imel dinka, na cillo maka wannan bayani daga farkonsa zuwa karshe, don ka samu dubawa cikin natsuwa.  Ina maka fatan alheri a ko ina kake.


Sunana Badamasi Alhassan Shanono. Wato na yi kwakwar na sameka fuska da fuska mu gaisa amma hakan ya ci tura.  Amma har gobe ina nan a kan hakan sabo da idan har Allah ya hada ni da kai, to, na tabbata zan yi karuwar da tafi wacca nake yi ta kafar sadarwa.  Daga Elbass Zuba – elbassian@gmail.com

Malam Badamasi barka ka dai.  Ina fatan Allah ya hada fuskokinmu da alheri.  A hankali watarana Allah zai hada mu.  Kana iya turo mini sakon tes ta lambar wayar dake wannan shafi, in yaso ta nan sai mu tattauna mu ga abin da zai yiwu.  Ina godiya da kyakkyawar zaton da kake mini.  Allah sa mu dace baki daya, amin.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.