Sakonnin Masu Karatu (2020) (15)

Alakar Fasahar 5G da Cutar COVID-19

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 23 ga watan Oktoba, 2020.

262

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan an yi sallah lafiya. Allah ya tabbatar da alheri duniya da lahira.  Wani labari ne cewa wai Bill Gates yana da hannu wajen kirkirar cutar COVID-19, don yayi amfani fasahar 5G.  To ban ja musu ba akai, nace to zan turo tambayar gareka don samun waraka.  Daga dalibinka Ahmad Brigade, Kano. Na gode.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ahmad.  Malam Ahmad wannan zancen ya dade yana yawo, kuma bayani a takaice bazai gamsar dakai ko duk wani wanda tuni wannan jita-jitar ta ratsa kwakwalwarsa ba.  Shi yasa muka fara bayani tiryan-tiryan kan ma’ana, da asali, da fa’idoji, da illoli, da kuma jita-jitar dake kunshe cikin fasahar 5G.  Mun dakata a kashi na 10 ne in ban mance ba.  Da zarar mun gama amsa tambayoyin dake jakar wasikunmu nan da makonni uku masu zuwa, za mu ci gaba da bayani kan fasahar 5G.

Kafin wannan lokacin, bazan so ince komai kan hakan ba.  Amma a cikin kashi na 12 ko 13, in Allah yaso za a samu gamsassun bayanai kan wadannan jita-jitan; yaushe suka faro?  Wa ya fara kawo su?  Wa ya alakanta su da cutar COVID-19?  Meye siyasar dake cikin wadannan jita-jitan?  Sannan, su kansu masu wadannan karerayi, zai dace mai karatu ya sani, suna da nasu boyayyar manufar da suke son cin mawa.  A cikin bayananmu in Allah Ya yarda duk zan yi wannan fashin bakin.

Don haka ayi hakuri a saurare ni.  Ina nan tafe in Allah Ya so.  Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya.  Dalibinka ne na shafin jarida.  Yanzu ban samunta (Jaridar AMINIYA) saboda dokar COVID-19.  Tambayata ita ce: ina neman karin haske ne dangane da shafin Youtube – duk abin da na dora a tasha ta, shin, zai yiwu duk mai hawa dandalin Facebook ya iya gani?  Kuma masu rajista (Subscribers) nawa ake bukata mutum ya samu kafin ya fara amfana da tsarin biyan kudi? Sannan kuma ko akwai wasu hanyoyi da ake bi a samu masu rajista da tasha cikin sauki, wato Subscribers? Daga Abubakar Muhammad, Brigade, Kano.

- Adv -

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Ahmad.  Babu alaka ta kai tsaye tsakanin sakonnin bidiyo ko na sauti da kake dorawa a tasharka ta Youtube da shafinka dake Dandalin Facebook.  Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, idan ka wallafa bayanai a tashar Youtube, sai wanda ya hau tasharka ke iya gani.  Amma idan kana son wadanda kake abota dasu a Dandalin Facebook su rika ganin sakonnin da kake wallafawa, sai dai ka rika nakalto adireshin rariyar dake dauke da bidiyon a Youtube, zuwa shafinka dake Facebook.  Duk wanda ya gani, idan ya matsa rariyar (link), kai tsaye sai a zarce dashi tasharka dake Youtube, daidai inda bidiyon yake.  Kana iya kwafan adireshin bidiyon daga gurbin adireshin manhajar lilo (Browser) da kake amfani da ita, idan ta browser ne.  Idan kuma kana amfani da manhajar Youtube ne dake wayar salula, idan ka budo bidiyon da kake son yadawa, a kasa za ka ga tambarin kibiya da yayi sama, a kasansa an rubuta: “Share”.  Da zarar ka matsa za a kai ka inda za ka iya kwafan adireshin kai tsaye, ko ka latsa tambarin Manhajar da kake son yada bidiyon a kai – akwai Facebook, da Whatsapp da sauran manhajoji.

Dangane da yawan masu rajista a shafin Youtube kafin a fara dora maka tallace-tallace a bidiyon da kake sanyawa don samun taro da sisi, kamfanin Google sun shardanta samun masu rajista 4,000 ne.  Don haka, idan kana bukatar samun rajista don kasuwantar da bidiyon da kake dorawa a shafinka, sai ka samu masu rajista, wato: “Subscribers” kenan, guda 4,000.  Sannan kamfanin zai tantance hakikaninka, ma’ana: dole su san da was uke mu’amala, ta hanyar maka wasu tambayoyi da kuma wasu bayanai da za ka bayar.  Ba wannan bane sharadin, da zarar an fara dora maka tallace-tallace, wajibi ne ka kiyaye; idan ka kuskura ka rika matsa wadannan tallace-tallace da kanka, za su gane.  Kuma idan suka gane za su kore ka.

Tambayarka ta karshe kuma kan wasu hanyoyi za ka bi wajen samun masu rajista a Youtube?  Wannan abu ne mai sauki, amma yana bukatar hakuri.  Da yawa cikin matasanmu da ke shiga cikin wannan harka, sun dauka da zarar sun bude tasha sun fara zuba bidiyo shikenan kawai sai kudade su fara shigowa.  Ba haka lamarin yake ba.  Shi tsarin kasuwanci na gaskiya yana daukan lokaci kafin a fara amfanuwa dashi. Sai an masa hidima.  Daga cikin hidimar da za ka yi wa tasharka kuwa akwai bin ka’idojin Google wajen bude shafin, da bin ka’ida wajen dora bidiyo.  Dole ne ya zama bidiyon da ba a taba dorawa a shafin Youtube bane.  Idan ka nakalto bidiyon wani, in dai an taba dora shi a Youtube, za su gane.  Sannan dole ka tanadi adadin masu rajista 4,000, kamar yadda na fada a sama.  Hanyar yin hakan kuwa ya danganci kudurarka ne.  Amma hanya mafi sauki ita ce: idan kana da shafi a Facebook, kana iya gayyatar abokanka su ziyarci shafin, sannan su matsa alamar: “Subscribe”.  Haka a cikin bidiyon da kake dorawa, ka rika sanya bayanin yadda masu ziyara za su rika yin rajista.  Sannan ka bibiyi tashoshi irin naka dake Youtube, don ganin yadda suke tafiyar da nasu shafin.  Wannan zai kara maka fahimta kan yadda abin yake, da yadda ake samun tagomashi cikin lamarin.

Wannan shi ne dan abin da ya samu.  Da fatan ka gamsu.  Na gode.

Assalamu alaikum Baban Sadik, Barka da yammaci. Ni ma’abocin karatun shafinka ne a jaridar AMINIYA.  Kuma dalibi mai karantar sashen aikin jarida, kuma ma’abocin rubutu cikin harshen Hausa. Ina son na kware a bangaren rubuce-rubuce da kuma sanin ka’idojin rubutun Hausa.  Ko za ka taimaka ka hada ni da wanda zai rika koya mini ta kafar intanet ko kafar sada zumunta? Musamman wajen tace rubuce-rubucena?

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Na yada da kokarinka da kuma kwazon ganin ka ci gaba ta hanyar inganta kudurarka ta ilimi da kwarewa.  In Allah Ya so zan bincika.  Idan na samu wanda zai taimaka, zan hada ka dashi.  Ni kam ba ni da kwarewa a bangaren rubutun Hausa, don haka ba lale bane in iya taimakawa ta wannan bangare.  Sannan ko da ina da shi ma, yanayin aikina ba zai ba ni damar gamsar da bukatarka ba.  Allah sa a dace.  A dakace ni.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.