Tsaga a Jikin Wata: Mu’jiza ko Yawan Shekaru? (2)

Ga kashi na na kasidar dake mana bayani kan tsaga a jikin wata. A wannan mako mun yi bincike ne kan asalin hoton dake yawo a Intanet. A sha karatu lafiya.

240

Daga Ina Wannan Hoto Ya Fito?

Bayan takaitaccen bayanin da muka samu kan Wata, ya kamata mu dawo kan wannan hoto da ke ta yawo a Intanet, da kuma alakarsa da mu’jizar tsagewar Wata a lokacin Manzon Allah a Makka.  Daga ina wannan hoto ya fito?  A iya bincike na, ban samu wata alama da ke nuna cewa wannan hoto ya samo asali ne daga Hukumar NASA ba.  Na shiga gidan yanar sadarwar hukumar na tsawon lokaci, amma ban samu wani bayani makamancin hakan ba.  Labarin da na samo a wasu gidajen yanar sadarwa, mai kokarin  hada alaka a tsakanin hukumar NASA ko masu binciken da suka yi wannan tafiya, da wannan hoto, shi ne wanda wani bawan Allah dan kasar Ingila mai suna Dawood Mousa Biskok, shugaban Jam’iyyar Islama ta Burtaniya, (wato British Islamic Party), ya bayar lokacin da wani babban malami masanin Kimiyyar Sararin Samaniya dan kasar Masar ya kai ziyara Ingila.

Wannnan bawan Allah yace ya dade yana ta bincike kan addinan duniya, da neman wanda zai bi.  Yana cikin hakan ne wata rana wani musulmi ya bashi kyautar Kur’ani mai tarjamar turanci, don ya karanta.  Budewarsa ke da wuya, sai yayi arba da shafin da ke dauke da ayoyin da ke tabbatar da tsagewar Wata (a farkon suratul Kamar).  Yace bayan ya karanta wannan shafi, sai yace: “kai, duk wannan tatsuniyoyi ne”.  Yace “sai na jefar da littafin kawai, na kama sabga na.”  “Wata rana ina zaune ina kallon wani shiri mai nasaba da fannin kimiyyar Sararin Samaniya a talabijin BBC, cikin shekarar 1978, inda mai gabatar da shirin ya gabatar da wasu masana kan wannan fanni daga kasar Amurka, sai lamarin ya sake dawowa.

- Adv -

A cikin hirar da yake yi dasu ne har bayani ya fado kan ziyarar da hukumar NASA na kasar Amurka ta shirya don kai ziyara a shekarar 1969.”  Wannan bawan Allah yaci gaba da cewa: “sai mai gabatar da shirin ke tambayarsu cewa, ‘shin ba almubazzaranci bane a ce hukumar Amurka ta kashe dala biliyan dari don wannan bincike, a yayin da akwai miliyoyin mutane masu kwana da yunwa da cututtuka a duniya?’”  Yace sai daya daga cikin wadannan masana yace masa ba al’mubazzaranci bane.  Idan an ga yawan kudin, a cewarsa, to ya kamata a san cewa a daya bangaren kuma, hukumar ta ci nasarar gabatar da binciken da ya gasgata hasashen da aka dade ana yi.  Wannan sakamakon bincike kuwa, inji su, shi ne, sanadiyyar wannan tafiya ko ziyara da aka kai zuwa duniyar Wata, an gano cewa lallai a wasu lokuta ko shekaru masu yawa da suka wuce, Wata ya taba rabewa gida biyu, sannan ya sake hadewa.  Suka ce an gano hakan ne kuwa ta hanyar alamar tsaga da ke jikin Watan.

“Ina jin haka”, a cewar Dawood Mousa Biskok, “sai kawai nayi maza na dauko Kur’anin da aka taba bani kyauta, na budo shafin da na taba karantawa.  Nan take, sai naga tabbacin abin da wadannan mutane suka binciko.  Ga shi Allah ya tilasta Amurka ta kashe biliyoyin daloli don gabatar da binciken da ke tabbatar da gaskiyar littafin Musulmai.  Wannan yasa na musulunta.”   Har zuwa lokacin da nake wannan rubutu, Dawood Mousa Biskok na raye, kuma har yanzu shi ne jagorar Jam’iyyar Islama da ke kasar Burtaniya.  Wannan labari, kamar yadda mai karatu ya gani, bai rasa alaka da samuwar wannan hoto a Intanet tsawon shekarun da suka gabata.

Amma kamar yadda na sanar, ban samu bayanai na hakika masu nuna alakar da ke tsakanin hoton da hukumar NASA ba.  Amma na dada fadada bincike kan halittar Wata baki dayanta, ban samu bayanin da ke nuna cewa wannan alamar tsaga (da ma wasu masu yawa da suka fi wanda ke jikin hoton nan), alama ce da ke nuna cewa Wata ya taba tsagewa sannan ya koma yadda yake ba.  To amma tunda hukumar NASA bata taba fitowa fili ta karyata wannan labari ko hoto da ake ta yadawa ba, sannan kuma ga wannan labari na shugaban Jam’iyyar Musulunci da ke Burtaniya ya shahara sosai, shi ma ban samu bayanai da ke nuna ta karyata ba, shi yasa wasu ke ganin akwai alaka mai karfi a tsakanin hoton da abin da ake riyawa.  Amma kafin mu yanke hukunci, zai dace mu duba wasu ka’idoji ko al’amura guda uku masu nasaba da fannin kimiyya da mu’jiza.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.