Kimiyya da Fasaha a Kasashen Musulmi (4)

Abubuwan Dake Kawo Tsaiko Ga Ci Gaban Musulmai A Kimiyya Da Fasaha A Yau

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 3 ga watan Disamba, 2021.

295

Kamar makonnin baya, za mu ci gaba da fassarar maqalar Farfesa Jim Al-Khalili, wanda qwararre ne a fannin nazarin kimiyyar Fiziyar Nukiliya (Theoritical Nuclear Physics) a Jami’ar Surrey dake qasar Burtaniya.  Mai fassara shi ne Malam Muddassir S. Abdullahi, kamar yadda bayani ya gabata a makonnin baya.  A sha karatu lafiya.

Abubuwan Dake Kawo Tsaiko Ga Ci Gaban Musulmai A Kimiyya Da Fasaha A Yau

Xaya daga cikin tazgaron dake haifar da wannan matsalar ya haxa da yadda wani sashi na Musulmai da yawa ke xaukar Ilimin kimiyya da fasaha da qere-qere a matsayin bokoko (Secular), ko kuma ma na arna ne kaxai, ko kuma na Turawan Yamma ne kawai; kai ka ce Musulman dake da wannan ra’ayin basu bibiyi tarihin yawan ci gaba da bincike na kimiyya da fasaha da sauransu da al’ummar Musulmai suka samar wa da duniya yayin da ludayinsu ke kan dawo a fannin ilimi da ci gaban xan adam a fitattun qarnonin baya ba. A tsakankanin waxannan qarnoni ne duniya tayi gamo-da-katar xin cin moriyar ci gaban da Musulmai suka samar a vangarori daban-daban ko ma ka ce a komai; kama daga Ilimin lissafi (Mathematics), da Ilimin kimiyyar sararin samaniya (Astronomy), da Ilimin likitanci (Medicine), da Ilimin fiziyya (Physics), da kuma Ilimin Sinadarai (Chemistry).

- Adv -

Sannnan ka gangaro ga Ilimin Kere-kere, da kuma Ilimin falsafa (Philosophy)…kai da sauran vangarorin ilimai da nazarce-nazarce da suka kawo sauyi ga duniyar ilimi da ci gaban duniyar wancan lokacin; suka kuma yi geza har zuwa duniyarmu ta yau. Waxannan fararen xaruruwan shekaru da ake wa laqabi da shekarun qololuwar xaukaka, wato golden ages sun samu ne sanadiyyar xabi’ar qwaqwa ta haqqaqe nazarce-nazarce da nazariyyoyi (Theories) na ilimi da al’ummomin Musulmai ke da shi a wancan lokacin; a yayin da yankin Turai ke cikin duhun kai ta vangaren ilimi da har ta kai a ke yiwa wannan lokacin laqabi da “Dark Ages.

Amma a hankali-a-hankali sai hasken wannan xabi’ar ta qwaqwa da kuma haqqaqe nazarce-nazarce da nazariyyoyin ilimi da al’ummomin Musulmai ke dashi a wancan lokacin haxe da zazzafar qishirwar neman sani da ilimi suka fara dudaxewa da yin qasa. Ya kamata mutane su sani cewa ita wannan dusashewar ta al’ummar Musulmai a vangaren kaiwa qololuwar su a ilimin kimiyya da fasaha da sauran ilimai ta faru ne qarnuka masu yawa qasa da yadda Yammacin Duniya ke tunani. Amma fa duk da hakan, an ci gaba da samun havvaka da ci gaba a fannonin ilimai kamar su Likitanci, da Lissafi, da kuma Ilimin Kimiyyar Sararin Samaniya, a vangaren Musulmai har zuwa qarni na 15 (15th Century).  Abun tambayar a nan shi ne, waxanne sabuba ne da dalilai suka qyanqyasar da wannan naqasa da al’ummar Musulmai suka yi a vangaren binciken kimiyya da fasaha?

Babban ummul-aba’isin hakan ya xamfara ne da xaixaicewa da rarrabuwa da kowa yaci gashin kansa da Daular Musulunci ta fuskanta sanadiyyar wasu buqatu na siyasa a wancan lokaci. Na biyu kuma shi ne, samun jagorori da shuwagabanni na Musulmai dake da rauni ko rashin sha’awa ko shauqi ga bunqasa harkar ilimi da binciken kimiyya da fasaha da sauran ci gaban xan adam a wancan lokacin. Na uku yana da alaqa da samun kinintakar daulolin Musulunci a wancan lokacin a vangaren binciken kimiyya da fasaha da xabi’ar haqqaqe abubuwa na ilimi da farkawa daga barci da yankunan Turai suka yi, wanda hakan ya haifar musu da bunqasar ci gaban su a vangaren kimiyya da fasaha.  Wannan yanayi shi ake kira da “European Renaissance”.   Wannan ya faru ne a tsakankanin qarni na 16 da qarni na 17.

Dalili na huxu, za ka iya qara mulkin mallaka da Turawa suka yi wa qasashe da yankunan Musulmai wanda ya haifar musu da shiga dabur-dabur da laluben asali da zatinsu, ko kuma su waye su haqiqa, wato dai suka samu abunda ake kira da Turanci da Identity Crisis. Suka kuma samu ko kuma ka ce a ka sa mu su abunda ake kira da wufcewar tunani ko mantuwa ko rashin qimanta ximbin abubuwan da Turawan Mulkin Mallaka suka same su a kai na Ilimomi, da al’adu, da sauransu da ake kira “the Cultural Heritage”. A yanzu, za mu iya gane rauni da rashin qarfin hujjojin masu jingina durqushewar da kaiwa qololuwa da Musulmai suka kai a binciken kimiyya da fasaha da sauran ci gaban duniya a kan suka da qyama da caccaka da wasu varin Musulmai da malamai na wancan lokacin suka ringa yiwa Ilimin kimiyya da makamantansu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.