Sakonnin Masu Karatu (2017) (11)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

290

Assalamu alaikum Baban Sadik, ina da tambayoyi guda uku kamar haka, don Allah a taimaka a amsa mini su: 1) Don Allah ya zanyi in hada ko da “Game” ne ko wata manhaja?  2) Yaya zanyi in yi karatu “Online” na kwamfuta, ko da “Certificate” ne?  3)  Shin, wayar Android ana iya Programming da ita, ko sai kwamfuta? Ni ne dalibinka Mubarak: mubaraksani15109@gmail.com

Wa alaikumus salam Malam Mubarak.  Ina rokon Allah yam aka albarka.  Amsar tambayarka ta farko dai ita ce:  za ka iya gina manhaja ce kadai ta hanyar koyon ilimin yadda ake gina manhajar kwamfuta ko wayar salula.  Kamar yadda ka gani daga darussan da nake kawowa, wannan fanni yana da matakai da kuma ka’idoji.  Da farko sai ka iya sarrafa kwamfuta iya gwargwado.  Abu na biyu, dole ka koyi ilimin gina manhaja, wato: “Programming.”  Abu na uku, dole ne ka koyi wani yare na musamman, kamar “Java” ko “C++” da dai sauransu.  A wannan mataki na uku ne za ka iya gina manhaja na musamman.  Gina manhaja kuma bayan ka samu kwarewa, kana bukatar kwamfuta wacce a kanta za ka iya aiwatarwa.  Eh, in amsa tambayarka ta karshe, za ka iya gina manhaja ta amfani da wayar salula, amma ba kowace irin manhaja ba.  Domin kuncin mahalli da takaituwar kudurarta wajen yin hakan.  Idan kana bukatar dama mai fadi da sarari mai nishadi, sai ka mallaki kwamfuta.

Tambayarka ta biyu, akwai shawarwari da na baiwa da dama cikin masu karatu kan hanyoyi da wuraren da za a bi wajen koyon wannan ilimi a Intanet, ba ma sai ka biya ko sisin kwabonka ba.  Zan makalo maka wadannan shawarwari tare da amsar wadannan tambayoyi naka.  Sai ka duba akwatin Imel dinka don daukawa.  Da fatan ka gamsu.


Da fatan kana cikin koshin lafiya tare da iyalanka, Allah yasa haka amin.  Baban Sadik don Allah ina so ka taimaka mini da kofi na cikakkiyar kasidar da ka gabatar kan tekunan duniya  ta hanyar imel dina.  Saboda ni mazaunin karkara ne ba na iya samun jarida ko da wane lokaci.   Hakan yasa na kasa samun bayanan a kammale.  Da fatan za ka sha ruwa lafiya, Allah ya karbi ibadunmu a wannan wata mai albarka amin. Sako daga:  Ibraheem Rabiu D/S Malumfashi jihar Katsina.  Imel din shi ne: Bassarache@gmail.com.  Ka huta lafiya.  Na gode

- Adv -

Wa alaikumus salam Malam Ibrahim, barka dai.  Kana iya daukan wadannan kasidu daya-bayan-daya cikin sauki a shafi na musamman da na tanada don taskance kasidun da ke bayyana a wannan jarida mai albarka.  Tunda wannan kasidar ce kake so, akwai fanni mai dauke da kasidu kan Teku gaba daya, wadanda na taba rubutawa a wannan jarida, idan kaje bangaren za ka ci karo da wadannan kasidu.  Sai dai kasancewar na sauya wa wasu daga cikinsu take, sai ka bi su daya-bayan-daya, don daukan wanda kake bukata.  Za ka same su a wannan rariyar likau din, idan ka matsa: https://babansadik.com/category/teku.  Da fatan ka gamsu.  Allah sa a dace amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik. Allah Ya saka da alheri dangane da fadakar da mutane da kake yi. Ina rokon Allah ya saka maka da gidan Aljannah.  Ina rokon a taimaka min kasidun da ka gabatar a kan Bamuda Triangle,” da kuma kasidunka wanda kayi bayani akan networking da kuma yadda ake programming, duk ta wannan email nazifirabiu44@gmail.com.  Daga Nazifi Rabiu Abdullah.

Wa alaikumus salam, barka Malam Nazifi.  Kana iya daukan wadannan kasidu gaba dayansu a shafinmu dake Intanet, inda na taskance dukkan kasidun da suka bayyana a wannan jarida mai albarka tsawon shekaru goma da suka gabata.  Dangane da kasidun da suka shafi tsibirin bamuda, idan gaba dayan kasidar kake so a dunkule, kana iya ziyartar sashin da na tanadi dunkulallun kasidu don saukar da wannan shahararriyar kasida, a wannan rariyar likau: https://babansadik.com/dunkulallun-kasidu, sai ka gangara cikin taken kasidun, idan kaci karo da wanda kake nema, sai ka duba can kurya daga dama, akwai alama mai dauke da: “Sauke”, kana latsawa za a saukar maka da kasidar.  Idan kuma kana son kasidar kashi-kashi ne, kana iya cin karo da kashi na daya a wannan rariya: https://babansadik.com/binciken-malaman-kimiyya-kan-tsibirin-bamuda-1.  A daya bangaren, kana iya samun wadanda na rubuta kan fannin “Networking” a sashin “Kwamfuta”.  Sai kaje matsa wannan rariyar likau:  https://babansadik.com/category/kwamfuta.  Wadanda suka shafi gina manhaja kuma, wato: “Programming,” kana iya samunsu a sashen “Gina Manhaja” dake: https://babansadik.com/category/gina-manhaja.  Allah sa a dace, ya kuma amfanar damu abin da muke koyo, amin.


Assalamu alaikum, da fatan kana lafiya. Baban Sadik don Allah ka taimaka idan da hali ka turomin rubutunka  na programming kashi na 1.  Wallahi na rasa sauran bangarorin sakomakon rashin jin dadi.   Kuma na je inda ake sayar mana da jarida ko zan samu ban samu ba na kuma duba a Intanet ban gani ba. Na karanta na 2 da na 3, ka taimaka ka turomin ta wannan Imail din don Allah. Daga mai karanta rubutunka Musbahu Rudwan Birnin kudu, Jigawa State: musbahurudwan12@gmail.com

Wa alaikumus salam Malam Musbahu barka dai.  Ai nesa ta zo kusa.  Yanzu kana iya zuwa shafin taskar kasidun ma gaba daya kawai ka karanta duk abin da kake son karantawa.  Dangane da kasidun da suka shafi gina manhaja kuwa, wato: “Programming,” kana iya samunsu a sashen “Gina Manhaja” dake: https://babansadik.com/category/gina-manhaja.  Allah sa a dace, ya kuma amfanar damu abin da muke koyo, amin.

- Adv -

You might also like
4 Comments
 1. ALIYU TAHIR says

  Aslm Dafatan Kana Lafiya Baban Sadiq Sunana Aliyu Tahir Daga Garin Sabon Gayan abuja road Dan Allah Inaso Ka Taimakami ne Ta Bangaren Yadda Zan Qirqire Website Dina Dakuma Yadda Zanyi Diseang Din Shi, 2, Dan Allah Kuma Inasan Nazama Dalibinka A Koda Yaushe Tawani Site Ne Zandinga Ziyartanka Sbd Inasan Nazama Masani Akan wayar Android Da Sauran Wayoyi Bislm, Gakuma Addreshina Na Email .aliyutahir072@gmail.com

  1. Baban Sadik says

   Wa alaikumus salam, Malam barka ka dai. Ina godiya matuka da wannan sako naka. Allah saka da alheri.

   Dangane da abin da ya shafi haduwa dani don karuwa ta ilimi, ina ba da hakuri cewa sai nan gaba kadan zan bude azuzuwa na karatu a Intanet, don karuwar jama’a kan fannonin ilimi daban-daban, musamman fannin kwamfuta da wayar salula. Shafin zai kasance da turanci da hausa ne, in Allah Ya yarda.

   A ci gaba da kasancewa tare damu a wannan shafi ko a jaridar AMINIYA, za a samu bayanai kan haka in Allah Yaso.

   Na gode.

   Baban Sadik

 2. ALIYU TAHIR says

  aslm baban sadiq nagode insha allah muna jiran wannan shafin dazaku bude, bayan wannan dan allah yazanyi in koya harking din wani a fecebook daga ALIYU TAHIR

 3. Abubakar umar says

  Salamu alaikum, malam Inaso in iya programming sosai. Ina so a bani shawara sannan a fadamin website Wanda zan iya koyon wannan fanni a saukake.na gode. Allah ya Kara basira.

Leave A Reply

Your email address will not be published.