Sakonnin Masu Karatu (2011) (7)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

132

Baban Sadiq ina da tambaya.  Tambayar ita ce, ina son na zama mamba a dandalin “Facebook” da yadda zan samu abokan hira.  Daga kaninku Kabeer BK Dandago Kano – 08032512767/064918663

Babban Magana, ashe Baban Sadiq ya samu kannai a shafin Kimiyya da Kere-kere, bayan abokai marasa iyaka.  To na gode Kabiru.  Da farko dai za ka shiga shafin Facebook, ka yi rajista, kamar yadda bayanai suka gabata.  Sannan ka shiga shafinka, ka nemi abokai, ko ka gayyaci wadanda ka sani.  Da zarar ka samu abokai, sai ka koma shafinka, ka gangara can kasa daga hannun dama, ka matsa alamar da aka rubuta: Chat.  Idan ya budo, za ka ga iya adadin abokanka da ke cikin shafukansu, sai ka matsa sunan wanda kake son hira dashi, ka kama hira.  Allah sa a dace.


Assalaamu alaikum Baban Sadik, ina maka fatan alkairi Allah ya kara hazaka amin. Dan Allah Baban Sadik kowace waya ce take da tsarin GPS? Kuma ya ake shiga? Waya ta Nokia 5130c-2 xpressMusic ce tana da shi? Na gode ni ne Hassan Adamu.

Malam Hassan Adamu ka yi hakuri da jinkirin da nayi wajen amsa maka wannan tambaya.  A gaskiya galibin wayoyin salula kan zo da kafar masarrafar GPS, watau Global Positioning System, wanda masarrafa ce ko manhaja mai zaman kanta da ke taimaka wa mai waya gano bigiren da yake.  Wannan masarrafa ko manhaja na amfani ne da tauraron dan adam, watau Satellite da ke sararin samaniya. To amma in da matsalar take shi ne, ba kowace waya bace ke iya sadar da mai wayar da wannan tauraron dan adam da ke taimakawa wajen gano bigiren.  Kananan wayoyi irin wadda ka zayyana a tambayarka ba su iya wannan aiki, kawai ana sanyawa ne don kwadaitar da mai wayar.

- Adv -

Ba ma irin wannan kadai ba, akwai da yawa wadanda suka fi ta girma da karfin iko, duk ba su iya aiwatar da wannan aiki.  Wayar Nokia nau’in 5130 XpressMusic ba ta da wannan masarrafa ta GPS. Manyan wayoyin salula kadai ke da shi, irinsu Nokia E52, da Nokia E71, da kuma Nokia E72.  Kai a takaice dai, galibin manyan wayoyi ne suke dauke da wannan masarrafa.  Da fatan an gamsu.


Assalaamu alaikum, zuwa ga Malam Abdullahi da fatan kana lafiya amin.  Suna na Adam a nan Kaduna ina so ka min gajeren bayani game da facebook, ina so na yi rajista, na kasa. Shi ne nake bukatar bayani daga gare ka. Da fatan Allah ya taimake ka amin, na gode.

Malam Adam na amsa tambayoyi makamantan wannan, kuma na tabbata zuwa yanzu ka karanta su.  Da fatan an gamsu.


Salamu alaikum Baban Sadik, tambayata ita ce, wani irin sanadari ne a tattare da man gas, watau “Diesel Gas”. Me yasa idan ya zuba a kan titi ya kan kayar da motoci idan suka taka birki, sabanin sauran nau’ukan man? Daga: Aliyu Mukhtar Sa’idu (I.T) Kano 08034332200.

Malam Aliyu, man dizil na dauke ne da wasu sinadarai da ke hana kasa shanye shi a duk inda ya zuba. Wadannan sinadarai dai su ne sinadaran da bayanai suka gabata a kansu a cikin kasidar da muka gabatar kan Danyen Mai da Yadda ake Sarrafa Shi.  A duk inda wannan mai na dizil ya zuba, wadannan sinadarai kan rike shi, ya like da kasa, ko kwalta, musamman, ya kama naso.  Da zarar an haye samansa, sai ya goce da mutum.  Ba komai ke kawo haka ba sai dabi’ar santsi da ke dauke cikin wadannan sinadarai.  Amma man fetur ba shi da wannan dabi’a. Shi da zarar ya zuba a wuce, saboda rashin nauyinsa, sai kasa da iska su shanye ko narkar da shi.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.