Sakonnin Masu Karatu (2011) (8)

A yau kuma ga mu dauke da wasu daga cikin tambayoyinku da kuka aiko ta wayar salula da hanyar Imel.  Kamar yadda na sha sanarwa dai, duk tambayar da na riga na amsa ta a lokacin da aka aiko ban cika kawo su ba.  Sai in na ga akwai wata fa’ida mai gamewa ga sauran masu karatu.  Domin wasu kan rubuto tambaya su ce in bamu amsar ta wayar salularsu ko adireshin Imel dinsu, kada in jira sai lokacin amsa tambayoyi a shafin jaridar.  Wasu kuma tambayoyinsu na bukatar amsa ne nan take, saboda irin matsalar da ke dauke cikin tambayar, wacce ke bukatar a warwareta nan take.  Allah mana jagora, amin.

76

Ina mana murnar samun kanmu cikin wannan wata na Ramalana mai tarin albarka.  Allah karbi ayyukanmu, ya kuma mu samu tsira daga tabewar duniya da azabar lahira.  Don Allah, duk abin da za ka fada, ka fadi alheri.  Duk abin da za ka aikata, ka aikata alheri.  Duk abin da za ka rubuta, ka rubuta alheri.  Da wannan, sai ka samu tsira a rayuwarka ta duniya da lahira baki daya.


Salam Malam Abdullahi (baban Sadiq) yaya aiki? Allah ya ba da sa’a. Don Allah kayi min karin bayani a kan “2GO”. Na gode: Aminu Sadauki U/dosa kaduna.

Malam Aminu, “2go” dai tsarin sadarwa ne na “ga-ni-ga-ka”, wato “real time chatting”, wanda ke baiwa masu amfani da shi damar aiwatar da sadarwa kai tsaye, a lokacin da suke yi, ta wayar salula.  Wannan tsari bai da bambanci da tsarin hirar kai tsaye da muke da su a Intanet ta hanyar kwamfuta. Bambancinsu kawai shi ne ta hanyoyin da ake aiwatar da su.  Yana da kyau ka san cewa wannan tsari yana da amfani, sannan yana da cutarwa.  Amfaninsa shi ne za ka samu saduwa da jama’a, a yi zumunci.  Rashin amfaninsa kuma shi ne cinye lokaci, ko bata lokaci musamman kan  hiran da babu fa’ida tattare da shi.  Sai a rika lura da tsawon lokacin da ake kashewa da kuma abin da ake fada a ciki.  Allah mana jagora.


Assalamu alaikum, ina fata Baban Sadik ya tashi lafiya. Wato malam akwai ranar da na yi wani rubutu a wannan jarida ta mu aminiya mai farin jini inda har na aika da adireshin Imail di na. To a wannan lokacin wani bawan allah ya kira ni yana tambayana akan yaya zai rika shiga shafukan sada zumunta irinsu facebook da twitter daga wayarsa? To, sai naga akwai bukatar malam yayi bayanin yadda ake saduwa da yan uwa cikin shafukan. Daga Kabeer, Rikkos, jos 07066574843

Malam Kabeer ai bayani kan haka ya sha maimaituwa a wannan shafi.  Sai dai wani sabon abu idan ya samu, ko wasu matsaloli da mutum zai fuskanta, a taimaka masa.  Amma dangane da abin da ya shafi budewa da mu’amala, sai dai kari.  Mun gode da wannan fadakarwa.


Assalamu alaikum Baban Sadiq, ya aiki? Ina da waya nokia kirar x2-00 ko zan iya aikawa da sakon Imel in kuma karba da ita? Daga Mukhtar Musa Jirgwai

Malam Mukhtar lallai za ka iya, domin wayar Nokia X2-00 na da wadannan ka’idojin sadarwa da za su iya taimaka maka yin hakan.  Sai dai ya kamata ka san cewa akwai hanyoyi guda biyu na yin hakan. Akwai tsarin manhajar Imel da wayoyin nokia ke zuwa da ita, wacce ke bukatar sai ka shigar da wasu bayanai da suka shafi adireshinka, da kalmomin shiga da kuma tsarin ka’idar karban sakon imel din da kamfanin imel dinka ke amfani da shi, wato “Email Protocol” kenan (irinsu POP3, da IMAP, da kuma SMTP).  Wannan tsari na da wuyan sha’ani idan baka san su ba.  Hanya ta biyu ita ce ka bude shafin intanet don shiga akwatin imel dinka. Wannan shi ne gama-gari wanda yafi sauki.


Assalamu alaikum, Baban sadik, muna yi maka fatan alkhairi. Ya Allah muna rokonka ka biya wa bawanka Baban sadik bukatunsa na alkhairi, kamar yadda yake biya muna bukatunmu na kwamfuta da fatam Allah ya kara yawaita muna ire irenku a duniya amin. Tambaya ta a yau itace: ina yin anfani da wayar salula, Nokia E71-1(42) ina son a yi min karin bayani kan yadda zanyi nayi rijistar “Video Call”, saboda idan nasa lambar ba ya yi, sai in ga ”Video Call is not supported by network”, Daga sunusi NNPC

- Adv -

Malam Sanusi, lallai Baban Sadik na godiya da wadannan addu’o’i.  Allah ya saka da alheri amin. Abin da ya shafi tsarin kira ta hanyar bidiyo a wayar salula, ya shafi tsari ne na kamfanin waya, wato “Network Service.”  Kowane kamfanin waya kuma yana da tsarinsa dangane da abin da ya shafe shi.  Wasu kan tafiyar da tsarin, ma’ana su samar da shi, ta yadda za ka iya kiran wani kuna hira kana kallonsa yana kallonka idan akwai tsarin a wayarsa.  Wasu kamfanonin kuma su kashe tsarin.  Duk dai wannan ya danganci kamfanin waya.  A baya na san kamfanin MTN na da tsarin, domin akwai wadanda ke kira na dashi daga cikin masu karatu da ke jihar Legas. Amma yanzu ban sani ba.  Don haka ta yiwu sun kashe tsarin, ko kuma ka je ofishin kamfanin wayarka ka musu bayani, watakil za su gamsar da kai kan haka.  Da fatan za a yi hakuri da dan bayanin da ya samu.


Assalamu alaikum Baban Sadik. Bayan gaisuwa ina yi maka fatan alheri da taya ka farin ciki saboda baiwan da Allah ya yi maka, kuma ga shi mutane na amfana da bayanai da kake musu. To Alhamdu lillahi. Ni ma wani lokaci zan aiko da nawa tambayar. Daga Abdullahi Muh’d anguwar Jabba S. G. Zaria

Malam Abdullah mun gode da addu’o’inku, wallahi muna farin ciki da ganin cewa dan abin da muke yi yana tasiri, ba don kowa ba sai don Allah.  Allah ya sa mu cikin sahun masu amfanar jama’a cikin dukkan lamuransu, amin. Sai mun ga naka tambayoyin, kuma Allah bamu ikon amsawa, amin.


Assalamu alaikum.  Don Allah Baban Sadik ka turo mini da bayanan nan da ka taba yi akan wayoyin BlackBerry ta wannan adireshin Imail din (musulmi5952@yahoo.com). Dalibinka: Abubakar U. Muhammad

Malam Abubakar sai ka duba jakar Imel dinka.  Da fatan za a gamsu da dan abin da ya samu.  Mun gode sosai.


Gaisuwa ga Baban Sadiq. Ina matukar karuwa da wannan shafi naka. Allah ya taimaka, ya kara basira. Nabude jakar Imail ne ina so in rika karbar sakonni ta wayata Nokia E51. Idan na shiga Retrieve email, na sa “ID” da “Password” na tura, sai ta dowo min da sakon cewa “you are sending…accept it this time or permanently”, idan na duba ta lntanet zan ga inbox di na. To ta yaya zan seta in rika karbar sako ta wayata? Sannan abu na biyu shi ne irin bidiyoyin da ake sa wa a shafukan Intanet ta youtube, idan na kunna sai ta ce “kana da matsalar real player, shiga nan ka sabunta ko kuma close an active one first” Dan Allah ina so a yi min bayanin hanyar da zan warware matsalata. Allah yai jagoranci amin.Daga Abba A.S Kano

To, Malam Abba, da farko dai, akwai alamar ko dai baka gama saita tsarin Imel dinka ba, ko kuma akwai matakan da suka kamata ka bi kafin kaiwa zuwa ga jakar Imel din, wanda ba ka isa zuwa garesu. Ban sani ba, shin, kana amfani da tsarin Imail da ke jikin  wayar ne ko ta “browser” kake shiga?  In tsarin Imel din waya ne, ya kamata a duk sadda aka maka tambayar farko, ka ce “accept permanently”, wannan zai sa duk sadda ka tashi shiga, ba za a kara turo maka wadannan tambayoyi ba.  Hanya ce ta tantance tsarin shiga wani shafi mai dauke da tsaro irin na bayanai. 

Matsalar bidiyo kuma wannan matsala da kake samu na nuna cewa lallai masarrafar “Real Player” da ke wayarka ta tsufa, kuma ba za ta iya aiwatar da aikinta ba a shafin Youtube. Domin wayar Nokia E51 tsohuwar waya ce, idan aka yi la’akari da yadda al’amura ke sabuntuwa ko caccanzawa a duniyar sadarwa.  Sai ka je shafinsu a http://www.real.co.uk, don ka sauko da sabon zubin, ka loda wa wayarka.  Da fatan an gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.