Sakonnin Masu Karatu (2011) (6)

Ci gaban sakonnin masu karatu. A sha karatu lafiya.

61

Salamu alaikum, Baban Sadik, tambaya ta ita ce game da nau’urar daukar yatsun hannu, watau “Finger Print Scanning Machine”, yadda ba ta ganin hannaye da wuri bayan an dora, wanda hukumar zabe ta kasa ta bayar don sabinta rijistar masu zabe na 2011, matsalar a ina take ne?. Aliyu Mukhtar Sa’idu (I.T) Kano email: aliitpro2020@yahoo.com 08034332200 08186624300

Dangane da abin da ya shafi matsalar rashin gano zanen yatsun hannun mutane da wannan na’ura ta yi fama da shi, akwai dalilai da dama.  Na farko shi ne, idan ya zama mai yatsun ya kankare su sosai, ta yadda zanen sun goge, ba a iya gano layukan da ke saman yatsunsa – ko dai saboda yawan aiki, ko saboda kanta, ko kuma saboda ‘yan dabarun da wasu ke yi wajen boye zanen hannayensu don gudun a kama su idan suka aikata wani ta’addanci da hannunsu.  A yanayi irin wannan ba abin mamaki bane idan wannan na’ura ta kasa gano zane tafukan hannun mutum.

Domin an dabi’antar da ita ne ta rika nuna wadannan zane da zarar mai yatsun ya dora su a kanta.  Muddin ya zama babu zane a saman yatsun, babu yadda za a yi a ga wani abu.  Wannan ka’ida ce sananniya, cewa: idan babu kira, to babu abin da zai ci gawayi.  Wasu lokuta kuma matsalar na iya samuwa ne daga na’urar; ko wanda ke lura da ita bai iya sarrafa ta ba, ko kuma babu makamashi isasshe (ma’ana batirinta ya yi rauni) da dai sauran matsaloli.  Da fatan Malam Aliyu ya gamsu.


Salam bayan gaisuwa, ko zan iya mallakar shafin intanet ta hanyar salula? Ni ne Ilyasu Muhammad Kiru, nagode.

Malam Ilyasu wannan ba abu bane mai yiwuwa, sai dai idan an gina maka gidan yanar sadarwar, sai ka yi amfani da wayar salularka wajen shiga.  Amma ba a iya amfani da wayar salula wajen mallakar gidan yanar sadarwa. Idan kana da babbar waya, wacce ke da dabi’u irin na kwamfuta a misali, kana iya bude shafukan Mudawwanai, watau Blog Pages, ko shafin Facebook.  Amma bude gidan yanar sadarwa mai zaman kansa, wannan sai ta amfani da kwamfuta.  Da fatan na fahimci tambayar da kyau.


Assalamu alaikum warahmatullahi taala wabarakatuh, bayan sallama ta Islama, ina mai matukar jinjina da addu’ar Allah ya kara lafiya da basira ga Baban Sadiq tare da fatan alheri ga filin kimiyya. Don Allah ina son in mallaki littafin nan [WHY ASTRONOMY] na Adnan Abdulhamid a ina zan samu.  Wassalamu alaikum, ni ne naku Bala Mohammad Zango T/Wada Kaduna.

To, Malam Bala Muhammad samun wannan littafi dai ba wani abu bane mai wahala, sai in bugun da aka yi ya kare.  Idan kaje shagunan sayar da littattafan musulunci, za ka samu in Allah ya yarda.  Ni kaina a masallacin Jumu’a na sayi nawa.  Kafin daga baya na nemi izinin fassarawa tare da buga littafin daga wajen marubucinsa.  Allah sa a dace.


- Adv -

Assalamu alaikum, da fatan kuna lafiya. Don Allah ina son a mini bayanin yadda zan yi in bude turaka a shafin “Facebook” ta cikin waya, don Allah a taimaka a mini bayani.  Daga Rumanah Abdullahi Gombe.

Dangane da abin da ya shafi yin rajistar shafi a dandalin abota na Facebook, mai son yin hakan na bukatar wayar salula mai iya mu’amala da shafin Intanet, karama ce ko babba. Amma in da hali a samu babba ko ‘yar madaidaiciya.  Daga nan sai a shiga shafin da ke http://m.facebook.com ko kuma http://www.facebook.com/mobile. Idan aka shiga, sai a matsa inda aka rubuta “Sign Up”.  Akwai fam da za a budo maka, sai ka cike, sannan a zarce da kai zuwa shafin da ka bude.  Idan aka zo yin rajista, za a bukaci adireshin Imel, da kuma kalmomin iznin shiga, watau Password.  Da zarar an sanar da kai cewa ka shafinka ya samu, sai ka yi maza ka zarce zuwa akwatin Imel dinka, akwai sakon Imel da aka aika maka, wanda ke sanar da kai cewa shafin ya samu, sannan ga wasu haruffa nan da ake kira Passcord.  Idan ka zo shiga shafin nan gaba, za a bukaci wadannan kalmomi da aka aiko maka cikin jakan Imel dinka.

Don haka ka kiyaye, kada ka jefar da su.  Bayan haka, da yawa cikin masu karatu sun sha bugo mini waya suna cewa sun samu matsala da shafinsu; sun bude amma kuma sun dawo don shiga shafin an ce musu ba za su iya shiga ba sai sun shigar wasu kalmomi, ko kuma a ce musu “Username or Password not correct.”  Duk ba komai ke kawo haka ba sai wannan matsalar.  Sai a rika kiyayewa.  Da fatan an gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadiq, yaya aiki da fatan Allah ya kara taimakawa da hazaka, amin. Bayan haka, a gaskiya ina jin dadin yadda kake kokari wajen wayar mana da kai, kasancewar kowane mako ina tare da wannan filin, na fahimci abubuwa da dama. Sai dai har yanzu na kasa fahimtar yadda zan tura bayani ta hanyar Imel ko karba. Na gode. Abubakar Sani Kaigar Malamai, Karamar Hukumar Danmusa, Jahar katsina.

Malam Abubakar bayani kan yadda ake aikawa ko karban sakonni ta Imel a wayar salula ya sha maimaituwa a wannan shafi.  Na farko dai ka ta tabbata wayar tana iya mu’amala da fasahar Intanet.  Na biyu kuma ya zama kana da adireshin Imel da ka yi rajista da shi, wanda kuma kake amfani da shi.  Na fadi haka ne don ka san cewa lallai ba a iya yin rajistar Imel ta hanyar wayar salula, sai in babbar waya ce mai cikakkiyar dabi’a irin ta kwamfuta – kamar su Blackberry a misali. Daga nan sai ka shiga wannan adireshin, wanda zai kaika inda za ka shigar da adireshin Imel dinka da kalmomin iznin shiga. Wannan adireshi kuwa shi ne: http://mobile.yahoo.com/mail. Da zarar ka shiga za ka ga wasikunka na Imel.  A sama za ka ga inda aka rubuta “Compose”, ko daga can kasa.  Idan ka matsa za a kaika inda za ka rubuta sako, har ka iya aika wa wasu ko wani.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum. Baban sadiq, na ga kasidarka game da “Ayyukan Wayar Salula.” Na amfana kwarai da gaske da karatun wadannan bayanai. Allah ya saka maka da alherinsa. Ameen. Da fatan nan gaba za ka yi mana bayani gameda “blogging” Haruna Abubakar Sokoto.

Malam Haruna na gode da wadannan addu’o’i, kuma Allah ya saka maka da alheri.  A gaskiya mun dade yin bayanai kan abinda ya shafi bude Mudawwana ko Turaka, watau Blogging.  Kasidu guda biyu muka gabatar tun cikin shekarar 2008 in ban mance ba.  Don haka idan kana bukata, za ka samu wadannan kasidu a Mudawwanar da muka tanada don zuba kasidun wannan shafi gaba da ke: http://fasahar-intanet.blogspot.com.  Da fatan ka gamsu.  Allah sa mu dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.