Saƙonnin Masu Karatu (2024) (4)

Hanyoyin Sadarwar Intanet

An buga wannan maƙala ne a jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 3 ga watan Mayu, 2024.

39

Hanyoyin Siginar Intanet (Ci gaba)

Hanyar farko ita ce ta amfani da tsarin sadarwa na kai-tsaye, wanda ya shafi samun siginar Intanet daga kamfanonin dake samar da hanyar sadarwa ta amfani da na’urorin sadarwa na ƙarƙashin teku.  Waɗannan su ake kira: “Internet Infrastructure Companies”.  Kuma suna nan a warwatse a nahiyoyin duniya gaba ɗaya.  Na zayyana uku daga cikin waɗanda ke nahiyar Afirka, wanda ɗaya daga cikinsu ne ke baiwa kamfanonin wayar salula 7 siginar Intanet a Najeriya.  Wannan kamfani kuwa shi ne MainOne, wanda ke baiwa kamfanin MTN siginar Intanet.  Shi wannan kamfani na MainOne yana samun siginar Intanet ne kai tsaye daga kamfanonin sadarwa na duniya, musamman waɗanda ke ƙasar Amurka da nahiyar Turai.  Sai ya shimfiɗa wayoyin kebul ta ƙarƙashin teku, don sadar da wannan sigina zuwa kamfanonin sadarwar wayar salula dake bukata a nahiyar Afirka.  Yana kawo waɗannan wayoyin kebul ne zuwa bakin gaɓar tekun ƙasashen da kamfanonin suke, daga nan kuma sai su jona kai tsaye.  Wannan haka tsarin yake a dukkan nahiyoyin duniya.

Hanya ta biyu kuma ita ce ta amfani da tauraron ɗan adam wajen sadar da masu amfani da katin SIM ɗinsu.  Kamar yadda bayani ya gabata a wancan maƙala da nayi ishara kanta na bayanin tsarin sadarwar wayar salula, siginar rediyo da muke amfani da ita wajen karɓa da amsa kira a wayoyinmu, muna samun isa gare ta ne ta hanyar wayar-iska, wato: “Wireless Communication”, wacce ke ɗauke ta hanyar tauraron ɗan adam da sandunan sadarwa (Communication Antenna) ke ɗarsanowa daga sararin samaniya.  Ta wannan hanya ne kamfanonin wayar salula ke aika wannan sigina na Intanet don amfanin masu ta’ammali da katin SIM ɗinsu.

Sai dai kuma, duk da cewa ta hanya ɗaya ake aika su, amma kowannensu na cin gashin kansa ne.  Misali, kana iya kasancewa a inda sabis yake, kuma ga shi kana gani a wayarka, kuma kana iya kira da karɓan kira, amma kuma ya zama ba ka da siginar Intanet.  Wannan shi ne ma abin da ke faruwa a halin yanzu sanadiyyar wancan matsala da aka samu na tsinkewar wayoyin kebul dake sadar da kamfanonin wayar salula da siginar Intanet.  Amma kuma idan babu sabis gaba ɗaya a wayarka, da wahala ka iya samun siginar Intanet.  Domin siginar na ɗauke ne a cibiyar sadarwar kamfanin wayar.  Idan babu hanyar da wayarka za ta iya aiwatar da sadarwa tsakaninta da cibiyar sadarwar kamfanin wayarka (Mobile Phone Station), babu yadda za ayi ka iya samun siginar Intanet.

Waɗannan su ne hanyoyin da kamfanonin wayar salula ke amfani dasu wajen sadar da kwastomominsu da siginar Intanet.  Da fatan ka gamsu.  Na gode.

- Adv -

Assalamu alaikum Baban Sadiƙ, barka da warhaka.  Da fatan kana lafiya tare da iyalinka.  Wai shin, meye alaƙar “P2P” da Cibiyar Binance?  A ɗaya ɓangaren kuma, meye alaƙar duka biyun da farashin dala a Najeriya?  Saboda abin na bani mamaki ne ace wai Binance tana da alaƙa da farashin dala a Najeriya.  Na gode. – Baban Umma Ibrahim, Anguwar Mu’azu, Kaduna, Najeriya: namaazukd@gmail.com.

Wa alaikumus salam, barka ka dai Baban Umma.  Ina godiya matuƙa da addu’a.  Allah saka da alheri, amin.  Wannan tambaya ta ka tana ɗauke ne da ɓangarori guda uku mahimmai – bayani kan tsarin P2P, da Cibiyar Binance, sannan da alaƙarsu da farashin dala a Najeriya. Zan yi iya ƙoƙarina wajen ganin na amsa su gwargwadon fahimta, ba tare da tsawaitawa mai gimsarwa ba.  Amma saboda tabbatar da tsari wajen bayani, zan fara da Cibiyar Binance ne.

Cibiyar Binance  

Wannan kalma ta “Binance” dai na ishara ne ga abubuwa guda uku, kowanne daga cikinsu na da alaƙa da dan uwansa ne.  Da farko dai, kamfani ne, sannan kuma gidan yanar sadarwa ne, wato: “Website” – https:// binance.com –  kuma manhaja ce da ake amfani da ita wajen gudanar da hada-hadar kuɗaɗen zamani ta hanyar Intanet, wato: “Cryptocurrency”.  A baya munyi bayani gamsasshe kan ire-iren waɗannan na’ukan kuɗaɗe na zamani a doguwar makalarmu mai take: “Fasahar Digital Currency, da Virtual Currency, da Cryptocurrency”.  A taƙaice dai, wannan shafi cibiya ce ta hada-hadar kuɗaɗen zamani.  Yadda ake hada-hadar hannayen jari a cibiyar “Nigerian Exchange” (NGX) a Najeriya, misali, haka ake hada-hadar waɗannan kuɗaɗe na zamani a wannan kafa ta Binance.

Wanda ya samar da wannan kamfani shafi shi ne: Changpeng Zhao, wanda ɗan asalin ƙasar Sin ne, amma yanzu ya mallaki shedar zama a ƙasar Kanada.  Wannan mutum, wanda ake wa laƙabi da “CZ”, ƙwararren maginin manhajar kwamfuta ne.   Wannan cibiya ta hada-hadar kuɗaɗen zamani ta Binance, ita ce cibiya mafi girma a duniya, cikin cibiyoyin hada-hadar kasuwanci sama da 500 tare da nau’ukan kuɗaɗen zamani sama da 300.  A duk mako wannan cibiya ta Binance tana samun maziyarta shafin guda miliyan 17 a taƙaice.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.