Sakonnin Masu Karatu (2019) (3)

Bayani kan tsarin "Cloud Computing"

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Fabrairu, 2019.

102

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya kai da iyalanka. Ni dalibi ne a fannin “Software Engineering”, ina son ka mini gamsasshen bayani game da “Cloud Computing.”  Ka huta lafiya.

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Bayani kan tsarin “Cloud Computing”, in dai gamsasshe ne, yana bukatar bincike mai zurfi don samar da gamsarwa.  Sai aka yi sa’a shi ne fannin da za mu kutsa da zarar mun gama amsa wadannan tambayoyi da a halin yanzu muke amsawa.  Amma duk da haka, abin da kalmar “Cloud Computing” ke nufi a dunkule shi ne: “Tsarin sadarwa na tafi-da-gidanka.”  A warware kuma, “Cloud Computing” wani tsari ne dake baiwa mutane damar mu’amala da bayanai ko manhajoji kai tsaye, wadanda ke aijye a wasu kwamfutoci a wasu wurare daban, ta hanyar wayoyinsu na salula ko kwamfuta.  Abin da yafi shahara a zamanin baya shi ne ka saukar da manhaja sannan ka loda wa kwamfutarka ko wayar salula, don amfani da ita a duk sadda ka samu dama.  Ko ka saukar da wasu bayanai a kan wayarka ko kwamfutarka, don amfani dasu a duk sadda ka tashi bukata.  A tsarin “Cloud Computing” ba haka lamarin yake ba.

Karkashin wannan tsari na “Tsarin sadarwar tafi-da-gidanka”, asalin bayan ko manhajojin suna ajiye ne a wasu kwamfutoci ko ma’adanai na zamani, wadanda jama’a ke iya kaiwa gare su a duk sadda suka tashi bukata.  Karkashin wannan tsari, ba ka bukatar saukar da manhaja a kan wayarka da dukkan bayananta, ko saukar da wasu tarin bayanai ya zama suna dauke kan wayarka a kodayaushe.  Sai dai ka shigar da bayananka kawai a asalin shafin dake dauke da su, sai a isar dakai kai tsaye, ta hanyar Intanet.

- Adv -

Kyakkyawan misali da zan baka shi ne na manhajar Gmail.  Manhajar dake kan wayarka ta Gmail ba ita ce ke dauke da sakonninka na Imel da ake aiko maka ko kake aika wa jama’a ba.  Kawai kofar isa ga bayanan ne ke kan wayarka.  Da zarar ka shigar da suna (username) da kalmar sirri (password) sai a riskar dakai asalin bayanan.  Shi yasa ma idan ka rasa wayarka, sanadiyyar sata ko lalacewa, da zarar ka samu wata sabuwar wayar, kana saukar da manhajar Gmail a sabuwar wayar, za a loda maka sakonninka kai tsaye.  Ka ga da ace akan wayarka hakikanin bayanan suke, da ka rasa su kenan daga wancan tsohuwar wayar da aka sace ko ta lalace.

Haka nan manhajar rubutu na Microsoft Office – irin su Word, da Excel, da Powerpoint.  A farkon lamari ana sayansu ne a dauke cikin faifan CD, ko kaje shafin Microsoft dake Intanet ka saya, sai a saukar maka su kan kwamfuta ko wayarka.  Amma a halin yanzu wasu lambobi kawai zaka saya masu suna: “License Code”.  Da zarar ka saya za a baka dama a shafin Microsoft dake Intanet, ka samu isa zuwa ga manhajar ita kanta, kai tsaye.  Haka ma kamfanin Google suna da irin wadannan manhajoji, irin su: “Google Docs”, da “Google Sheets”, da kuma “Google Slides”.  Dukkan wadannan ba ka bukatar saukar dasu a kan kwamfutarka.  Shafin google kawai zaka je a Intanet, ka budo su, ka rubuta abin da zaka rubuta, ka dabba’a (printing), ko ka taskance su (saving) a shafinka;  duk sadda ka tashi bukata sai dai ka shiga shafinka na Google dake dauke da wannan manhaja, kayi ta’ammali dasu kai tsaye.

Kafin in karkare.  Tsarin “Cloud Computing” na dauke ne da rukunai guda uku.  Na farko shi ne asalin mahallin dake dauke da bayanai ko manhajar.  Wannan shi ake kira “Cloud Storage System”.  Kwamfutoci ne dake jone da dibga-dibgan ma’adanai na zamani masu mizani bila-adadin.  Dukkan manyan kamfanonin sadarwa na duniya suna dasu a wasu wurare ko kasashe da suka tanada.  Google na da irin wannan mahalli da ake kira: “Data Centers” a wurare sama da goma shabiyu a fadin kasar Amurka kadai.  Kamfanin Microsoft ma na dasu.  Sannan cikin watan jiya (Janairu, 2019) ya bude wani sabon cibiyan adana bayanai a kasar Jamus, da Suwizaland da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa (United Arab Emirates).  Rukuni na biyu shi ne fasahar Intanet.  Wannan shi ne titin da wadancan bayanai dake ma’adanar da bayaninsu ya gabata, suke bi a yayin da ka bukace su daga inda kake, a ko ina ne kuwa a fadin duniyar nan.  Kada ka mance, a tsarin “Cloud Computing”, bayanan da kake mu’amala dasu ba akan waya ko kwamfutarka suke ba.  Dole sai da Intanet za ka iya riskarsu.  Sai rukuni na karshe, wato na’urar sadarwar da kake amfani da ita wajen isa ga wadannan bayanai ko manhaja.  Wannan kuwa ya hada da wayar salula, da kwamfuta, da iPada, ko duk wata na’ura da ke iya aiwatar da sadarwa tsakaninta da wata na’ura ‘yar uwarta.  Wannan ya hada da talabijin, da na’urar dafa abinci (oven), da na’urar Wanki (washing machine), da na’urar wanke farantai ko kwanukan abinci (dish washer), wadanda ke dauke da tsarin dake taimaka musu wajen aiwatar da sadarwa tsakaninsu da duk wata na’ura ko mahallin dake iya hakan.

Wannan, a takaice shi ne dan abin da zan iya cewa a halin yanzu. Kamar yadda nayi alkawari, da zarar mun gama amsa tambayoyi, za mu kutsa cikin wannan fanni in Allah Yaso.  Aci gaba da bibiyarmu.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.