Tasirin Killace Jama’a Sanadiyyar Cutar COVID-19 Ga Kamfanoni da Kafofin Sadarwa na Zamani a Duniya (2)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 5 ga watan Yuni, 2020.

144

Facebook Inc.

Tsawon lokacin da wannan cuta ta bayyana har zuwa yanzu, kamfanin Facebook yayi uwa da makarbiya wajen toshe kafofin yada jita-jita da sakonnin karya (Fake News), musamman a manyan manhajojinsa guda uku: Dandalin Facebook, da WhatsApp, da kuma Instagram.  Ya kashe kudade sama da dala miliyan dari uku ($300m) wajen haka.  Ya kuma sauya tsarin gudanar da hira ta hanyar rubutu da hotuna da bidiyo da sauti da ake amfani dasu a WhatsApp da Facebook chat, duk don rage yawaitar sakonnin bogi da na karya.  Cikin wannan lokaci dai, kamfanin ya samu cinikin da ya kai dala biliyan goma sha bakwai da miliyan dari hudu ($17.4bn), wanda kari ne da kashi 18% kan cinikin da yayi a marhalar kasuwanci na farko na shekarar 2019.  Wannan ciniki na tallace-tallace ne kadai, wanda shi ne asalin hajar da kamfanin ya mallaka daman.  Sannan yayi cinikin dala miliyan dari biyu da casa’in da bakwai ($297m) a wasu fannonin kasuwanci da yake yi ta karkashin kasa.  A takaice dai, cikin watanni hudu da suka gabata, kamfanin Facebook yaci ribar dala biliyan hudu da miliyan dari tara ($4.90bn), wanda ya rubanya ribar da yaci a marhalar kasuwanci na farko na shekarar 2019 da kashi 102%.

Amma duk da haka, kasancewar babbar hajarsa ita ce karban tallace-tallace daga kamfanoni da masana’antu, kamfanin yace akwai alamar cinikinsa a wannan bangare ya fara ja baya, saboda rufe kamfanoni da shaguna da kasashe suka yi.  An rage bayar da tallace-tallace, tunda galibin mutane sun koma gidaje, an daina tafiye-tafiye, sannan adadin kayayyakin da ake saye ya ragu sosai matuka.  Wannan shi ne abin da malaman fannin tattalin arziki ke kira: “Reduction in aggregate demand and supply”.

A bangaren maziyarta kuwa, an samu karin jama’a masu rajista matuka.  Adadin masu ziyartar dandalin Facebook a duk yini yanzu ya kai biliyan daya da miliyan dari bakwai da talatin (1.73bn).  Wannan kari ne akan adadin shekarar 2019 da kashi 11%.  A duk wata daga cikin watannin da suka gabata kuwa, kamfanin yace ana samun masu ziyara biliyan biyu da miliyan dari shida (2.60bn), wanda shi ma kari ne, amma da kashi 10%.  Wannan ke nuna cewa lallai jama’a suna yawaita amfani da wannan dandali musamman a bangaren manhajar Facebook Messenger, da Facebook Groups, da Facebook Video, sai kuma Facebook Live, wanda manhaja ce da galibin malamanmu suka yi amfani da ita wajen gudanar da tafsirin watan Ramadan da ya gabata, inda jama’a ke kallo da sauraro kai tsaye.  A takaice dai, kamfanin Facebook, kamar sauran kamfanonin da suka gabata, ya ci riba sosai.

- Adv -

Zoom Video Communications

Wannan kamfani dai karamin kamfani ne, amma dalilin da yasa na kawo bayaninsa don manhajar da yake tallatawa ne, wato: “Zoom”.  Na tabbata mai karatu yaji wannan suna ko da sau daya ne cikin watan Ramadan da ya gabata.  A tare da cewa karamin kamfani ne, amma manhajar da ya samar, wanda kafin shiga wannan annoba corona, ba kowa ya santa, sai gashi ta shahara, ta kere sauran.  Sunanta kawai kake ji.  Daga bayyanar wannan cuta zuwa yanzu, kamfanin Zoom ya samu karin kudaden shiga da kashi 78%.  Cikin watan disamba, kwastomominsa duk basu shige dari shida da arba’in da daya ba.  Amma zuwa karshen watan Maris, sai gashi da kwastomomi guda dubu tamanin da dari tara (80,900).

Wannan manhaja ta zoom dai ana amfani da ita ne wajen aiwatar da hira ta hanyar bidiyo, ko tarurruka.  Kana iya amfani da sauti kadai.  Ko kuma ka hada tsakanin sauti da bidiyo.  Sannan wannan manhaja ana iya amfani da ita a kan wayar salula.  Na kalli tafsiran malamai kuma na saurara ta amfani da wannan manhaja, musamman Sheikh AbdurRazaq Yahaya Haipan.  Kusan dukkan tafsiransa da wannan manhaja aka cilla su ga masu sauraro.  Daga cikin abin da ya kebance wannan manhaja da ‘yan uwanta shi ne, kana iya aiwatar da taro da mutane dubu daya a lokaci daya; kowa kana kallonsa a bidiyo kuma kana jin sautinsa.  Sannan mutane dubu goma na iya halartar taron da kuke yi; suna ji, kuma suna  gani.

Daga adadin maziyarta miliyan goma da yake samu a duk yini cikin watan Disamba na shekarar 2019, daga bayyanar wannan cuta zuwa yanzu, wannan manhaja na samun maziyarta sama da miliyan dari biyu a duk yini.  Wannan ke nuna tasirinsa, inda jama’a da kamfanoni da masana’antu da jami’o’i ke amfani dashi wajen aiwatar da laccoci da tarurruka ta hanyoyi daban-daban.  A halin yanzu an kididdige cewa wannan kamfani shi ne na daya, a fagen aiwatar da hira da tarurruka ta hanyar bidiyo a duniya.  Faduwar wani, inji Hausawa, tashin wani.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.