Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (4)

Wannan shi ne kashi na 4 a jerin binciken da muke gabatarwa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. A sha karatu lafiya.

227

Dabaru da Hanyoyin Satar Bayanai

Masu aiwatar da wannan munnunar sana’a dai, kamar yadda bayanai suka gabata, na dogaro ne da bayanan da suke sacewa masu alaka ta kai tsaye da wadanda suke son sace zatinsu don cinma manufofinsu munana.  Wadannan hanyoyin satar bayanai su ma suna da yawa, kamar yadda dabarun nasu ke da yawa.  Domin duk abin da ya shafi kafafo da na’urorin sadarwa na zamani, ba ka iya haddade iya abin da za a iya yi dasu ko ta hanyarsu kai tsaye.  Ya danganci kwarewa da basirar da mai basira kawai.  Amma akwai shahararrun hanyoyi da dabarun da suka saba amfani dasu wajen tattaro bayanan jama’a cikin sauki.  Wasu daga cikin wadannan hanyoyi masu sauki ne, wasu kuma suna da tsauri, suna bukatar kwarewa ga mai son amfani dasu.  Ga dai bayani nan kan wadannan shahararrun hanyoyin:

Tsintar Bayanai a Bola

Wannan tsari na tattaro bayanai shi ake kira “Dumpster Diving”, a fannin Kutse (Hacking).  Masu amfani da wannan hanya wajen tattaro bayanan da suka danganci wanda ake son sace masa zati na amfani da tarin takardun da aka zuba ne a bola; bolar ma’aikatar da suke son tattaro bayananta, ko hukumar da suke son tattaro bayananta ko bayanin wani daga cikin ma’aikatan dake hukumar ko ma’aikatar.  A ka’ida dukkan ma’aikatu da hukumomi da kamfanoni suna da bola (Dustbin) da suke zuba sharar da aka kwaso daga ofisoshin dake ma’aikatar.  Wannan shara ba irin sharar da muka sani bane mai dauke da kazanta.  A a, tarin takardu ne da aka daina amfani dasu amma kuma masu dauke da bayanai masu mahimmanci ga dan Dandatsa (Hacker); ko dai sunayen ma’aikatan ne, ko sunayen kwamfutocin dake ma’aikatar, ko taswirar yadda aka tsara gajeren zangon sadarwar ma’aikatar (Local Area Network – LAN), ko adireshin Imel din ma’aikatan dake hukumar, ko lambobin wayarsu da adireshin gidajensu, ko duk wani abin amfani ga dan Dandatsa.

Idan aka zuba su a bolar ma’aikatar, sai ya rabo yazo kamar dan Bola Jari, yana tsintar abubuwa; kai baka san me yake nema ba. Da zarar ya kwashi bayanan da yake nema shikenan. Sai dai kaji mummunar labari bayan wasu ‘yan lokuta.

 

 

 

 

 

 

Tsintar Bayanai daga Tsofaffin Na’urorin Sadarwa

- Adv -

Wannan ita ce hanya ta biyu.  Wato tsintar bayanai daga tsofaffin na’urorin sadarwa da aka jefar, ko aka yi gwanjonsu ga ma’aikata ko jama’ar gari.  Sau tari hukumomin gwamnati kanyi gwanjon kwamfutoci, kamar yadda muke gani ana yi a Najeriya, da ma’adanar bayanai  – irin su “Flash Drive” ko “Hard Drive” ko “Zip Drive”  – wadanda aka dade ana amfani dasu a kamfani ko hukumar, da sauran kayayyakin sadarwa masu mahimmanci.  Dan Dandatsa na iya zuwa ya saya ko ya kwaso su daga inda aka zubar.  Cikin basirar da Allah ya bashi zai tayar dasu, idan ma ana ganin sun lalace ne.  Idan kuma ana tunanin an goge bayanan dake cikin ma’adanar ne, wannan abu ne mai sauki ya dawo dasu.  A yanzu akwai manhajar da za ka iya amfani da ita wajen dawo da dukkan bayanan da aka goge daga wata kwamfuta ko ma’adanar bayanai.  Abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka.  Wannan tana cikin hanyoyin da suke bi wajen tattaro bayanai.

Tsintar Bayanai daga Shafukan Hukumomi ko Kamfanoni

Masu amfani da wannan hanya kan je shafin hukumomin gwamnati ne, ko kamfanoni, ko ma’aikatu, don rairayo bayanan jama’a cikin sauki.  Misali, Hukumar Zabe ta kowace kasa kan buga jerin sunayen mutanen da suka yi rajistan katin zabe, a shafinta.  Don kowa ya zo ya duba.  Wannan jerin bayanai na dauke da cikakken sunan masu rajista ne, da adireshinsu a cike, da lambar wayarsu, da jinsinsu, da tsayinsu, da launin idanunsu, da inda suke aiki, da addininsu, da harshensu, da ranar haihuwarsu da dai sauransu.  Dukkan wadannan bayanan da na zayyana, jari ne a wajen dan Dandatsa.  Haka idan kaje shafin manyan bankunan kasashe (Central Banks), za ka samu bayanai tinjim na kamfanoni da jama’a.

Satar Katin “ATM” ko “SSN” ko Katin Tafiye-Tafiye Zuwa Kasashe

Daga cikin hanyoyin satar bayanai har wa yau akwai satar katin “ATM” din jama’a, ko lambar katin tallafin kasa da hukuma ke baiwa marasa aikin yi ko gajiyayyu a wasu kasashe, wato: “Social Security Number,” ko kuma sace katin bulaguro tsakanin kasashe, wato: “International Passport” Kenan, irin wanda ake amfani dashi don zuwa kasashe.  Me yasa?  Saboda mallakar wadannan katuna ko lambobi, hanya ce mafi sauki wajen mallakar “hakikani” kuma “ingantattun” bayanan jama’a, kamar yadda suke a ma’adanar hukuma.  Domin hukuma ce ko bankuna ke bayar da wadannan katuna ko lambobi.  Amfani dasu kai tsaye na nuna masu asalin katin ne suka yi amfani dasu, kuma nan take za a musu abin da ya kamata.

Hanyar Siyasar Rayuwa da Dabi’a

Wannan hanya ce mai matukar tasiri da ‘yan Dandatsa ke amfani da ita wajen tatsar bayanai daga jama’a cikin hira dasu da suke yi dasu.  Wannan tsari na satar bayanai shi ake kira: “Social Engineering” ko “Human Hacking”.  Idan Dan dantsa na son tatsar bayanan da suka shafeka, cikin hira da yake yi da kai yake tatsa.  Da kanka zaka bashi bayanan ba tare da saninka ba.  Domin zai yi ta maka tambayoyi ne masu alak ta kai tsaye da bayanan, cikin dabara, har ka fadi abubuwan da daga cikinsu ne zai yi ijtihadi (na shedanci, ba na fikihu ba), har ya zakulo abin da yake so cikin sauki.

Misali, idan yana son sanin tarihin haihuwarka; da ranar, da watan, da shekarar, sai ya dauko hira mai alaka da hakan a kaikaice.  Idan yana son sanin sunan mahaifi ko mahaifyarka, sai ya dauko hira mai alaka da sunan mahaifiyarsa, har ma ya gaya maka (a wasu lokuta sunan bogi zai fada, ba hakikanin sunan mahaifiyarsa ba).  Idana yana son sanin adireshinka na Imel, nan take zai kawo hira mai alaka da adireshinsa na Imel, ko yace akwatin Imel dinsa ya samu matsala ko makamancin hakan.  Idan yana son sanin sunan (Username) da kake amfani dashi wajen hawa shafukanka na Dandalin sada zumunta, zai dauko labari mai alaka da nashi shafin.  Da dai sauran dabaru da ba kowa ke iya gane hakan ba.  Dabara ce irin ta wasa da kwakwalwar mutane, wacce ke dauke cikin fannin ilimin Dabi’a, wato: “Psychology.”

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Aminu Musa Aliyu says

    Barka da kokari ML Abdullahi baban Sadik
    Ubangiji Allah yakara dauka Ameen,
    Ina daya daga cikin daliban ka
    A kullum

Leave A Reply

Your email address will not be published.