Yaduwa da Munanan Tasirin Labaran Bogi (Fake News) a Kafafen Sadarwar Zamani (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 3 ga watan Satumba, 2021.

268

Ma’ana da Asalin Labaran Bogi a Duniya

Daga cikin abin da ya sake daukan hankulan ‘yan Najeriya cikin makonni biyu da suka gabata, musamman ma a arewacin kasar, shi ne yaduwar labaran bogi ko na kanzon kurege, wanda yaci gaba da yaduwa sanadiyyar hatsaniyar da aka samu a garin Jos na jihar filato.  An samu wani sakon bidiyo da aka ta yadawa, wanda kuma ake jingina shi ga wannan hatsaniya.  Alhali wannan bidiyo ba shi da alaka ko na sisin kwabo da wannan mummunar lamari da ya auku a garin Jos.  Asali ma da aka bincika sai aka samu cewa abin dake kunshe cikin bidiyon ya yi shekaru kusan 10 da faruwa. To amma da yawa cikin mutane sun yarda, kuma har ma sun harzuka.  Allah kadai yasan abin da wannan bidiyo ya haifar na hasarar rayuka da dukiya.

Wannan nau’in labari, wanda zallar karya ce, ko gaskiya ce amma aka cakuda ta da karya, shi ake kira: “Fake News” a harshen fasahar sadarwa na zamani.  Manufar yada irin wannan labari dai mummuna ce, kuma galibin masu yadawa suna yin hakan ne don kokarin cinma bukatu na siyasa, ko addini, ko kabila, ko kasuwanci.  Mafi yawancin mutane ba sa iya tantance labaran karya daga na gaskiya.  Sannan ba su da hakurin bibiyar asalin labarin, musamman idan a yanayi ne irin wannan dake cike da rashin tsaro da tashin-tashina tsakanin al’ummomi mabambanta.

Samuwar ire-iren wadannan labarai na karya dai ba wani sabon abu bane.  A iya cewa sun samo asali ne tun samuwar jinsin dan adam a bayan kasa.  Sai dai sun habaka ne cikin shekarun da basu wuce 20 ba, sanadiyyar yawaita da bunkasar hanyoyin sadarwa na zamani, wadanda ke taimaka wa jama’a samarwa da aikawa da kuma ta’ammali da nau’ukan bayanai masu yawa, a lokaci daya kuma a wuri daya.  Amma duk da haka, ma’anarsu bata canza ba. Sai dai karkasuwa da wannan nau’in labari yayi, sanadiyyar mahallin dake taimakawa wajen samar dashi.

- Adv -

Yaduwar Labaran Bogi a Duniya

Duk da cewa labaran bogi sun dade tare da dan adam, kuma samuwar hanyoyi da kayayyakin sadarwa na zamani sun dada fadada yaduwarsu, sai dai kuma basu fara daukan hankalin duniya ba sai lokacin da zaben shugaban kasar Amurka da ya gudana a shekarar 2016, wanda a karshe Donal Trump ya lashe takarar.  Shi kanshi Trump na cikin wadanda suka sa Kalmar “Fake News” ta shahara har zuwa yau.  Saboda a lokacin ne kafafen sada zumunta (Social Media) suka yadu, jama’a ta yawaita a kansu fiye da sauran lokutan baya.

Saurin yaduwar bayanai na daga cikin manyan siffofi da dabi’un dandalin sada zumunta.  Domin manhajojin dake wadannan kafofi suna kururuta labari ne iya gwagwadon yawa ko adadin wadanda suka yi ta’ammali dashi.  Misali, idan ka wallahi labari a shafinka na Facebook, iya yawan wadanda suka gani ko karanta labarin, iya yadda manhajar Facebook zai kururuta shi, ta hanyar bijirar da sakon ga sauran jama’an da basu ganshi ba.

Bayan haka, daga cikin abin da ya kara habaka yaduwar labaran bogi ko na karya, akwai Karin bunkasa da yaduwar kafafen sadarwar sada zumunta, wadanda ta nan ne galibin ire-iren wadannan labaru ke samun ruruwa.  Alkaluman bayanai sun nuna cewa, zuwa wannan shekara ta 2021, akwai mutane biliyan 3.78 dake amfani da kafafen sada zumunta.  Wannan adadi shi ne kashi 48 cikin 100 na adadin mutanen dake raye a wannan duniya tamu.  Daga cikin wannan adadi, kashi 91, wanda galibinsu daga kasashe masu tasowa ne, suna amfani da wayar salula ne wajen ta’ammali da wadannan kafafe na sada zumunta.  Sannan, Dandalin Facebook ne ke da kashi 68 na adadin wadanda ke mu’amala da shafukan sada zumunta.  A wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da kamfanin bincike mai suna: “Phew Research” ya gudanar a kasar Amurka kadai, ya tabbata cewa ‘yan kasar masu shekaru daga 18 zuwa 29, kashi 84 cikin 100 dinsu na amfani da kafafen sada zumunta.  Tsakanin masu shekaru 30 zuwa 49 kuma, kashi 81 ne ke amfani da kafafen sada zumunta.  Ta bangaren masu shekaru 50 zuwa 64 kuma, kashi 73 ne ke amfani da kafafen sada zumunta a kasar.  Sannan daga masu shekaru 65 zuwa sama, kashi 45 ne ke amfani da wadannan kafafe na sada zumunta a kasar Amurka.   Sannan a karshe, sakamakon binciken na nuna cewa a duk yini, cikin masu amfani da kafafen sada zumuntan nan, kowannensu na kashe a kalla a awanni biyu da rabi wajen yin hakan.

Abin da wannan bayani ke tabbatar mana shi ne, wadannan kafafe na sada zumunta suna da tasiri mai karfin gaske wajen ta’ammalin jama’a a tsarin sadarwa na zamani a duniyar yau.  Kuma wannan ke nuna cewa, iya gwargwadon yawan masu sadarwa a wannan mahalli, iya gwargwado gamewa da tasirin irin sakonnin da suke aikawa ko karba ne a tsakaninsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.