Tallafin Fasahar Hasken “Laser” Ga Fannin Likitanci (2)

Ga kashi na biyu cikin jerin kasidun da muka fara kawowa makon jiya kan fasahar hasken “Laser” da alakarsa da fannin likitanci.

411

Tsarin Tiyata

Saboda saukin mu’amalar da ke tattare da hasken leza wajen tiyata, da zarar an hasko shi saman fatar jiki, sinadaran da ke cikin hasken kan narke cikin ruwan da ke cikin  fatan, nan take.  Kamar yadda muka sani, abin da yafi komai yawa a jikin dan adam shi ne ruwa.  Wannan haske zai narkar da sinadaransa ne cikin ruwan da ke fatan jiki, daga nan kuma ya hade da sinadaran da ke samar da jinni, wato Hemoglobin, da Melanin.  Wannan haske na leza ne ke shiga cikin fata, ya kona duk kwayar cutar da ke cikinsa, ko ya bayar da damar rede matattaciyar yadin (wato Tissue) da ke tsakanin nama da fatar jiki. Da wannan haske har wa yau ake amfani wajen haska cikin kodar dan adam, don gano inda tsakuwa suke.  Da zarar an hasko su, sai a cilla haske mai matukar zafi don narkar da wadannan duwatsu da ke cikin kodar ba tare da an keta kodar ko fatan jikin mara lafiya ba.  Dangane da magance matsalolin hakora, akan yi amfani da wannan haske wajen haskawa ko leko inda matsala take a hakoran mara lafiya.  Ana amfani da wannan haske har wa yau don cire gashin jiki, ko na kai, ko na wasu bangarorin jikin dan adam.

Su ma nau’ukan zanen haihuwa ko zanen sha’awa da wasu ke yi a jikinsu, a yanzu an gano cewa da hasken leza duk ana iya goge su ko share su har abada.  Idan muka koma bangaren gyaran fatan jiki ma haka abin yake.  Da wannan haske ake amfani wajen baje dukkan kurajen da ke fuska (irinsu kyasbi da sauransu) ko kurajen baya ko kuma tamojin da ke bayan yatsun tsofaffi.  Dukkan wadannan na karkashin tsarin amfani da hanyoyin tiyata don gyaran jiki, wato Laser Cosmetic Surgery.  A karshe, a yanzu ma an gano cewa za a iya amfani da wannan haske na leza wajen kankare sinadaran da ke jikin wanda ya kamu da ciwon shan tabar sigari ko tabar wiwi a misali.  Hakan na yiwuwa ne ta amfani da wannan haske don hasko muhallin da wadannan sinadarai suke, da kuma yin amfani da hasken wajen baje su ko narkar da su, su zama ba su da wani tasiri a jiki.  Bincike ya nuna cewa ana samun nasara kashi 80 cikin 100 kan wannan matsala. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, hakan ya danganci yanayin jiki ne, da kuma zurfin jarabtuwa da tabar ga mara lafiya. Don haka, gwajin da za a yi wa mara lafiya kafin a fara aiwatar da wannan tiyata, shi zai tabbatar da cin nasara ko rashinsa.

Amfanin Hasken Leza

Masana fannin likitanci sun tabbatar da cewa wannan sabuwar fasahar tiyata ta hasken leza na da fa’idoji masu yawa wajen saukake tsarin tiyata, musamman tiyatar idanu, da na koda, da na fatan jiki, da cire gashi da dai sauran fannonin da wannan fasaha ta shafa.  Amfani na farko ita ce saurin warkewa.  Sun tabbatar da cewa lallai ana samun saurin waraka idan aka yi amfani da hasken leza wajen tiyata, idan aka kwatanta tsawon kwanaki ko lokacin da mara lafiya ke dauka kafin ya warke daga tiyatar da aka masa ta amfani da wukaken tiyata.  Domin a bangaren fasahar hasken leza, akwai tiyatar da za a yi wa mara lafiya a rana guda, kuma ya mike a ranar ya ci gaba da harkokinsa. Illa dai za a bashi magunguna ne da zai rika sha.

Fa’ida ta biyu ita ce rage yawan kamuwa da wasu cututtuka a yayin tiyata.  Kamar yadda muka sani, da yawa cikin wadanda ake wa tiyata ta amfani da wukaken tiyata kan kamu da wasu cututtuka, saboda fede fatan jiki ko cikinsu da ake yi da wukar tiyata.  Wannan ke sa a dauki tsawon lokaci ana shan magani bayan an yi tiyatar.  To amma idan aka yi tiyata da fasahar hasken leza, hakan kan rage yawan kamuwa da wasu cututtukan daban, wato Infection.  Daga cikin fa’idojin amfani da fasahar hasken leza wajen tiyata har wa yau, akwai rashin zuban jini.  A bangaren amfani da wukaken tiyata a kan samu zuban jini sanadiyyar fida da ake yi.  Amma a tsarin amfani da fasahar hasken leza kuwa babu wannan matsalar.  Domin akwai tiyatar da za a yi wa mutum, daga farko har karshe ba a zubar da jini ba.  Saboda hasken na shiga cikin fata ne, yana iya yanke fatan ma ba tare da jini ya zuba ba ko kadan.  Wannan na daga cikin fa’idoji masu muhimmanci.

Fa’ida ta gaba ita ce rage yawan rauni ga mara lafiya.  Duk da cewa amfani da fasahar hasken leza wajen tiyata akwai zafi, amma kuma yana rage yawan raunuka da mara lafiya ka iya samu a yayin da ake ta fede shi ta amfani da tsarin aiwatar da tiyata da wukaken tiyata.  Maimakon a yi ta yanke fatan ana kutsawa cikinsa don isa zuwa ga wata gaba da ake son aiwatar da aiki a cikinta ko a kanta, a tsarin fasahar hasken leza sai dai sinadaran haske su kutsa cikin fatan, har su isa zuwa ga gabar da ake son aiwatar da aikin a cikinta ba tare da an yi wa fatar rauni ba.

Fa’ida ta karshe ita ce, wannan fasahar haske ta leza tana da saukin sha’ani wajen aiwatar da tiyata ko samar da waraka a fannin likitanci, ta kowace fuska idan aka duba.  Saukin sha’ani wajen yin tiyatar; saukin sha’ani wajen samar da waraka nan take (domin ana iya yi wa mutum tiyata da wannan sabuwar tsari, cikin awanni biyu ya mike ya kama harkokinsa).  Sannan ga saukin sha’ani wajen mu’amala da gabobin jikin mara lafiya ba tare da an kutsa inda bai kamata ba a yayin tiyatar.

Wasu ‘Yan Matsaloli

Kamar dai duk wani abin amfani ne, wannan fasaha ta hasken leza na da nata fa’idoji da kuma ‘yan matsaloli wadanda ba za a rasa ba. Daga cikin ‘yan matsalolin da ke tattare da wannan fasahar tiyata ta amfani da hasken leza akwai dan Karen tsada.  Aiwatar da tiyata ta amfani da wannan sabuwar fasaha na bukatar kudi mai dimbin yawa, da kuma kwarewa.  Saboda ba kowane likita bane zai iya aiwatar da tiyata ta amfani da wannan fasaha ta hasken leza.  Abu na biyu kuma shi ne rashin yaduwa.  Ba ka safai ake samun wannan fasaha a kasashe masu tasowa ba.  Galibi sai kasashen Turai.  Wannan yasa abin yayi tsada.  Idan an samu a kasashe masu tasowa ma sai ka ga a asibitoci masu zaman kansu ne, kuma dole ya yi tsada.  Har wa yau, duk da cewa amfani da wannan fasaha ta hasken leza na rage kamuwa da wasu cututtuka sababbi, a daya bangaren kuma akan kamu da wasu cututtuka masu alaka da sinadaran hasken, idan ba a dace ba.

- Adv -

Nau’ukan Fasahar Hasken Leza

Akwai nau’ukan hasken leza kala-kala. Na farko shi ne nau’in hasken leza mai dauke da sinadaran iska wanda ake kira Carbondioxide Laser (CO2 Laser).  Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, wannan fasaha ta hasken leza na dauke ne da haske da kuma iska, wato Gas.  Wannan nau’in hasken leza mai suna CO2 Laser yana taimakawa ne wajen yanke fatar jiki ba tare da jini ya zuba ba.  Kuma da shi ne ake yin tiyata don cire kwayoyin cutar da ke haddasa kuraje a cikin fatan jiki.  Har wa yau ana amfani da shi wajen cire kwayoyin cutar sankara ko kansa (wato Cancerous Diseases).  Saboda nau’in haske ne mai karfi, mai kaifi, kuma mai dauke da sinadaran haske masu zafi.

Nau’in hasken leza na biyu shi ne wanda ake kira ERBIUM Laser.  Wani irin haske ne mai fitowa a hankali, ya shiga fatar jiki a hankali cikin natsuwa, sannan ya narke cikin ruwan jiki nan take, yana barbazuwa babu kakkautawa.  Da wannan nau’in hasken leza ne ake iya rede matacciyar yadin fatar jiki (wato Skin Tissue), da irin fatar da zafin hasken rana ta kashe, daga jikin tsofaffi.  Har wa yau akan yi amfani da wannan nau’in haske wajen cire rubabbiyar yadin fatar jiki (wato Dead Tissue) sanadiyyar kamuwa da kwayoyin cuta.  Bayan haka, akan yi amfani da wannan nau’in haske don share kurajen fuska, irinsu kyasbi da sauransu.

Nau’in hasken leza na gaba shi ne wanda ke fitar da haske launin rawaya ko ruwan kwai, wato Yellow Light Laser.  Wannan nau’in haske yana fitar da gajerun ballin haske ne launin rawaya, ko Short Pulses of Yellow-Color.  Wannan launin hasken leza yana shiga cikin ruwan jiki ne, ya saje da launin sinadaran da ke samar da jini; ko Hemoglobin ko Melanin.  Ana amfani da wannan launin hasken leza ne wajen magance matsalolin jijiyoyin bangarorin jiki.   Ana kuma amfani da shi don goge jajayen tsagar jiki, wato Red Birth Marks. 

Launin hasken leza na gaba shi ne launin hasken leza ja, wato Red Light Laser.  Wannan nau’in hasken leza shi ne wanda ake amfani da shi wajen share ko goge tamojin yatsun hannu masu bayyana sanadiyyar tsufa ko yanayin zamantakewa a wani muhalli.  Launin hasken leza ja shi ma yana fitowa ne da gajerun ballin haske, amma masu dauke da dimbin sinadaran haske masu yawa, don aiwatar da aikin cikin sauki.  Hakan kuma na samuwa ne ta hanyar wani tsarin amfani da haske mai suna Q-Swtiching, a turancin kimiyyar lantarki.

…………………………………………………………………………………

Fadakarwa

Na lura a duk lokacin da muka gabatar da wata kasida kan fannin likitanci ko kimiyyar magunguna, sau tari sai masu karatu su yi ta bugo waya ko aiko sakonnin tes suna neman bayanai kan wasu nau’ukan kawayoyi ko cututtuka da yadda za a magance su.  Ba komai ya jawo haka ba sai don irin bayanin da suka gani a shafin, wanda a cewarsu sun gamsu da su.  Wanann a baya kenan.  A yanzu da kashin farko na wannan kasida kan hasken leza ya bayya a makon baya, wasu ma sun yi ta kira suna neman bayanai kan yadda za su fusktanci wasu matsaloli masu alaka da bayanan da suka karanta, inda nan take nake katse su saboda rashin alaka a tsakanin abin da suke nema da kwarewar mai rubutun.

Na sha maimaita mana a baya, zan kuma kara maimaitawa cewa, wannan shafi na FADAKARWA ne kawai.  Duk da cewa muna taimakawa wajen magance matsalolin da suka shafi wayoyin salula da yadda ake mu’amala da fasahar Intanet a aikace, amma a bangaren likitanci babu abin da zan iya yi sai fadakarwa.  Wannan na daga cikin dalilan da suka sa ban cika son kawo bayanai kan fannin likitanci ba, don ba fanni na bane ko kadan.  Duk wanda ke son shawara kan abin da ya shafi kiwon lafiya gaba daya, akwai shafin Dakta Auwal Bala, kana iya daukan lambar wayarsa ka rubuta masa tes don neman Karin bayani. Amma Baban Sadiq ba likita bane, ba kuma kwararre bane a fanni likitanci, don Allah mu kiyaye.  SHAFIN KIMIYYA DA KERE-KERE SHAFIN FADAKARWA NE KADAI, BA SHAFIN BA DA SHAWARA KAN HARKAR KIWON LAFIYA BANE. 

Haka akwai masu bugo waya suna neman Karin bayani kan hotunan wayoyin salula ko kwamfuta da ake sanyawa a shafin; idan na sayarwa ne, suna so.  Wannan ma ba na sayarwa bane.  Kuma ba na sayar da kwamfuta ko wayar salula, sai dai in ba da shawara kan irin wacce za a iya saya, iya gwargwado.  Duk hoton da aka gani a shafin, an sa ne don fadakarwa, da kuma munasabar bayanin da ke shafin da hoton da aka sa. Domin wasu har cewa suka yi idan na sayarwa ne za su aiko da kudi. Ba haka lamarin yake ba.  Don Allah mu kiyaye.  Na gode.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.