Gaskiya da Gaskiya (1): Tasirin Wa’azi

Wa’azi yana da tasiri matuka, tamkar tasirin ruwa ga kasa busasshiya, ko tasirin zafin duka da bulala. Babban Malami AbdurRahman Ibn Al-Jawziya zai taya mu hira yau.

193

Watarana an tambayi babban malamin birnin Baghdad a karni na biyar bayan Hijira, wato ABDUR-RAHMAAN IBN AL-JAWZI (ba Ibn Al-Qayyim ba) sadda yake fadakarwa ga dubban jama’a:

“Shin, me yasa idan ana wa mutum wa’azi ko nasiha, sai ya fashe da kuka saboda tasirin wa’azin. Amma da zarar ya bar wurin wa’azin bayan wasu lokuta sai ka ga ya kama aikata assha, kamar ba shi bane ya fashe da kuka a baya?”

Sai babban shehin yace:

- Adv -

“Ai shi wa’azi kamar bulala ce ake lafta wa mutum. Muddin za a dimanci zabga masa ita, ba zai taba daina jin zafinta ba. Amma da zarar an daina, sai zafin ya gushe.”

Tun sadda na karanta wannan zance na wannan malami a cikin littafisa mai suna SAIDUL KHAATIR, daga nan na kara fahimtar tasirin gaya wa kai gaskiya. Na sha jin wa’azi a lokuta daban-daban tun muna tsangaya, in ji na kadu, amma bayan wasu lokuta sai in nemi tasirin kaduwar da nayi sadda ake min wa’azi in rasa. Sai in na sake sauraran wani wa’azi makamancinsa. Abin da wannan ke nuna mana shi ne:

1. Muddin ana sauraran fadakarwa, to, aikata laifuka zai ragu; sannan kuma

2. Ba a killace kwanaki ko shekaru da za a daina yi wa al’umma wa’azi. A ta yin wa’azi, daga zanin goyo zuwa likkafani.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    Wannan gaskiya ne

    Dan Uwa, sai dai fatan Allah yasa mu da ce Amin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.