Gaskiya da Gaskiya (10): Ni’imar ‘Ya’Ya – Me Ka Koya Daga Rayuwarsu?

‘Ya’ya na daga cikin ni’imar da Allah Yayi wa bayinsa a wannan duniya. Kai hatta ma a Aljanna. A tare da cewa mu muka haife su, akwai abubuwan darasi da dama da za mu iya koya daga rayuwarsu.

163

An tambayi wani babban malami cewa: “Wa kafi so a duk cikin ‘ya’yanka?” sai yace: “Karamin cikinsu har sai ya girma; mara lafiyar cikinsu har sai ya warke; wanda yayi tafiya daga cikinsu har sai ya dawo.” Abin nufi a nan shi ne, yana son kowannensu, musamman wanda ke cikin tsanani; domin yafi bukatar kulawa. Wannan iya makurar adalci kenan.

Sai dai wani abin da bamu cika lura dashi ba shi ne, yadda muke abin koyi gare su, haka su ma suka kamata su zama abin daukan darasi daga rayuwarsu (ko shirmensu, kamar yadda muke cewa). Abin da zai sa su ji sun rasaka gaba dayansu bayan ka koma ga Ubangiji, shi ne adalci da kake yi a tsakaninsu a duk sadda bukatar hakan ta taso. Akwai abin birgewa, da daukan darasi, da nishadi, da bakin ciki, da nadama a cikin rayuwar yara, musamman ‘ya’yanka. Suna da kishi a tsakaninsu, suna da tausayi a tsakaninsu, suna da son kansu, suna da tausaya wa juna, suna da son sanin abin da basu sani ba, suna kuma da son a yabe su idan sun kyautata.

Cikin watan azumin da ya gabata, watarana ranar asabar na shigo gida kafin sallar azahar, sai nayi kacibis da Hanan (‘ya ta mai shekaru 5) ta bata rai, ta murtuke a tsaye a bakin kofar kicin. Ina zuwa sai kawai tace mini: “Baba ka ga Nabila ta karya mini azumina ko?” Sai nace: “Subhanallah! Ya aka yi haka?” A zato na ko ta danne ta ne ta sa mata abinci a baki. Nace: “Da me ta karya miki azumin?” Sai tace: “Da wuka.” Nan take sai na kwashe da dariya. Na gane bakin zaren. Cewa nayi duk wanda yayi azumi guda, akwai naira 100. Shi ne take son nuna mini cewa ta fa dauki azumin, Nabila ce ta karya mata azuminta da wuka. Don haka, wannan sako ne gare ni idan nazo biyan masu azumi, kada a mance da ita.

Watarana Nabila (mai shekaru 8) ta tsare ni a falo tace mini: “Wai Baba me yasa kowa sai ya rika ce maka Baban Sadik, ba a ce maka Baban Nabila?” Ranta a bace. Nace kiyi hakuri, ai ni ma Baban Nabila ne. Bata samu natsuwa sosai ba sai da taji wasu na kira na Baban Nabila. Rannan ina cikin daki sai na ji ta da kannenta (Hanan da Abdulhamid) tana ce musu: “Ai babana ne, ba baban ku ba. Babana ne ni kadai.” Nabila akwai kishi in ana magana kan batuna ne. Sai ga Hanan ta garzayo a guje ina cikin daki, tace, ranta a bace: “Baba ka ji Nabila na cewa wai kai ba babanmu bane ko?” Sai nayi murmushi nace, “Ni baban kowa ne; Baban Sadik, Baban Nabila, Baban Hanan, Baban Abdulhamid, kuma Baban Imam (Abdullah).” Sannan hankalinta ya kwanta.

- Adv -

A duk sadda Sadik (mai shekaru 10) ya tafka shirme, ko na dawo aka ce min yayi wani abu mara dadi, nakan killace shi a daki in ce masa: “Haba Babana na kaina! (yana son wannan kalma), me yasa kake haka? Ka mance cewa babban suna ne da kai. Sunanka fa sunan babban abokin Manzon Allah ne; ko ka mance ne?” Sai ya kama murmushi. Daga nan sai in masa fada kan abin da yayi. Ashe ba haka lamarin yake a zuciyarsa ba. Rannan kawai sai na ji yana gaya wa kannensa: “Ai ni ba ruwana da ku, ku kananu ne. Ni babana yace ni babban mutum ne. Ku yara ne, ba ruwana da harkarku.”

Wasu lokuta idan baka lura ba, sai yaro ya dauki dabi’un da baka dauke su a bakin komai ba, a matsayin tafarki. Dabi’ar Maman Sadik ce idan yaro yayi abin da ya bata mata rai, sai tace: “Allah shirye ka/ki.” Watarana mun tashi ranar asabar da safe, Maman Sadik na shara, sai Hanan (sannan shekarunta uku da rabi) ta kalleta da kyau, tace mata: “Eh! Ka ga mata. Yau da kanki kike sharan? To, Allah Ya shirye ki.” Ina cikin daki sai na kwashe da dariya da Maman ta ban labari. Nace ai addu’a ce ta miki.

Haka wata ‘yar ajinsu ke ba da labari. Dabi’arta ce a duk sadda aka nemi tayi wani abin da ba ta da karfin yi, sai tace: “Wace ni Kaza!” Ashe danta mai suna Arafat yana ji. Rannan sai ya bukaci ta masa wani abu, sai ta daki kirji tace: “Ni wa, Arafat?” Sai yace mata: “Mama ke Kaza…!” Sai ta firgce. Tun daga wannan rana ta daina fadar wannan kalma.

Don haka, kayi kokarin zama Uba nagari; kiyi kokarin zama Uwa ta gari, mai tausayi, mai adalci, mai raha; kana so ko ba ka so, ka sani ko baka sani ba; kina so ko ba ki so, kin sani ko baki sani ba, sai ‘ya’yanka/ki sun yi koyi da abin da kake/kike yi.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Muryar Hausa24 Online Media says

    MASHA ALLAH

    ALLAH YA KARA MANA KAUNAR ZURI’AR MU BAKI DAYA, YA KUMA BAMU IKON TARBIYANTAR DA SU BISA TAFARKI MADAIDAICI

Leave A Reply

Your email address will not be published.