Sakonnin Masu Karatu (2009) (4)

Ci gaban Sakonnin makon baya. A sha karatu lafiya.

56

Kwamfutar Tafi-da-Gidanka

Salamu Alaikum Baban Sadik, ko rufe kwamfuta nau’in tafi-da-gidanka ba tare da an kashe ta ba yana haifar mata da wasu matsaloli? –  Aliyu Mukhtar Sa’id (IT), Kano: 08034332200

Eh to, idan har aka ci gaba da haka, hakan na iya haifar mata da matsala, musamman idan ya zama sanya ta ake yi cikin jaka ko wani killataccen wuri inda iska baya shiga, ba tare da an kashe ta ba.  Babbar matsalar da ka iya samuwa ita ce, raguwar inganci tare da karfin na’urar da ke sarrafa ta gaba daya, wato Processor.  Hakan zai rika sa ta rika yin zafi, a karshe kuma masarrafar ta gaza, ya zama sai an canza sabuwa.  Amma duk da haka akwai inda za a iya saita kwamfutar, ta zama duk sadda ka rufe marfinta, za ta kashe kanta nan take.  In haka aka saita ta, to ba wata matsala. Ko da kuwa da zarar an rufe ana sanya ta cikin jaka ne.  Domin nan take za ta kashe kanta.  Da fatan an gamsu.


Tsakanin Fasahar “Bluetooth” da “Infra-red”

Salamu Alaikum Baban Sadik, tambaya ta ita ce: tsakanin Infared da Bluetooth ya tsarinsu yake ne wajen karbar sakonni da aikawa?  –  Aliyu Mukhtar Sa’idu (IT), Kano: 08034332200

A fasahance, idan aka ce “Bluetooth”, musamman ma a wannan zamani namu, ana nufin wani tsari ne ko hanyar sadarwa da ke kumshe cikin kayayyakin sadarwa na zamani irin su wayar salula, wanda ake iya aikawa ko karban jakunkunan bayanai da suka shafi haruffa da sauti ko murya (irin na wakoki da karatuttuka da laccoci) ko hotuna; masu motsi (Video) ko marasa motsi, a tsakanin wadannan kayayyakin sadarwa.  Wannan ita ce ma’anar “Bluetooth” a takaice.  Sadarwa a tsarin Bluetooth na yiwuwa ne ta hanyar neman wayar salular wanda kake son aika masa, a iya tazarar da bata wuce taku talatin ba (30ft), ko kuma nisan mita goma (10 meters).  

- Adv -

A iya wannan tazara, idan ka kunna na’urar Bluetooth din ka, to duk wanda wayarsa ke kunne a iya kadadar wannan tazara ko zango, za ka same shi da zarar ka nemo, har ma ka iya aika masa da sako.  Idan wayar ka ta nemo sunan wannan waya da take son saduwa da ita, za ta bata suna na musamman, sannan sai ta nemo kogo (Port) mafi sauki da zata iya aikawa da sakon, ba tare da mishkila ba. Da zarar ta nemo, sai ta fara barbara, don sheida wa wancan wayar salular cewa ‘gani nan tafe’.  Idan aka amsa mata, sai ta fara aikawa kai tsaye.  Tana gama aikawa sai ta rufe wannan hanya, tare da yanayin sadarwar.

Ita kuma wacce ake barbara da zarar sakon neman alfarma ya zo mata, sai ta nemo ka’idar da za ta yi wannan aiki na karban sako. In ta nemo, sai ita ma ta zabi kogon (Port) da zai karbi wannan sako, don shigar mata.  Da zarar ta gama wannan aiki, sai ta fara sauraron sakon.  Idan aka turo, sai ta karba kai tsaye.  Idan sakon ya shigo kogon da aka tanada masa sai ita wannan waya da ta karba, ta rufe kofofin da ta bude da farko, don cika sadarwa.  Duk wannan na faruwa ne cikin lokacin da bai wuce dakiku ashirin ba.  Illa kawai aikawa da sakon ne ya danganta da yawan mizanin sakon; idan mai yawa ne, zai dan dauki lokaci.  Idan kuma kadan ne, nan da nan sai a gama.  Wannan tsari na aikawa, a yayin da ake aikawa din, shi ake kira Pairing, ko kuma Point to Point Communication (wato P2P, a harshen ilimin aikawa da sako ta zamani).

Wannan fasahar sadarwa ta samo asali ne shekaru goma da suka gabata, lokacin da wasu kamfanonin kayayyakin fasahar sadarwa guda biyar suka kafa wata kungiya ta masu sha’awan ci gaban yadawa da kuma sawwake hanyar sadarwa a tsakanin kayayyakin sadarwa, wato Special Interest Group, ko SIG a takaice.  Sun yi haka ne cikin shekarar 1998, kuma a karshen shekarar 1999 ne suka cin ma matsaya kan wannan fasahar sadarwa, inda suka zabi sunan wani sarki da yayi zamani a karni na goma a turai mai suna Harold Bluetooth, suka ba wannan sabuwar hanyar sadarwa da suka kirkira. 

A daya bangaren kuma, abin da kalmar Infra-red ke nufi shi ne: kasa da launi ja!  Wannan fassara ce ta la’akari da ma’anar daidaikun kalmomin – wato “infra”, da kuma “red”.  Amma a fasahance idan aka ce Infra-red, ana nufin hanyar sadarwa ta zamani wacce ke amfani da makamashin harske kasa da launin ja, mai dumi, da ke taimakawa wajen sadarwa a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa na zamani.  An kuma siffata wannan nau’in haske ne da kalmar “Infra”, saboda kwayan ido ba ya iya tsinkayarsa.  Ba kamar sauran nau’in haske irin na rana da muke tsinkaya har mu ji ya ishe mu ba.  An gano tasirin wannan yanayi ko makamashin haske ne shekaru dari biyu da suka gabata, inda aka lura da cewa akwai wani tasiri mai amfani da ke taimakawa wajen gano abubuwa da dama ; daga aikawa da sauti zuwa gano darajar yanayi ; daga gano cututtuka zuwa aikawa da sakonni ; daga daukan hoto zuwa magance cututtuka, duk ta amfani da haske da ke samuwa a wannan sararin samaniya da Allah Ya hore mana!  

Sabanin fasahar Bluetooth, sadarwa a tsakanin kayayyakin fasahar sadarwa masu dauke da makamashin Infra-red ya sha banban.  Ba a bukatar doguwar tazarar da ta  gota taku uku, ko kuma mita guda, Wato digiri talatin (30 Degrees) kenanHar wa yau, fasahar Infra-red na iya aiwatar da sadarwa ne idan ya zama babu wani shamaki komai kankantarsa tsakanin kayayyakin sadarwa biyu.  Idan akwai shamaki, ko da na kaurin yadin riga ne, sadarwa bata yiwuwa.  Amma sabanin yadda muka dauka, cewa sai an hada wayar salula jiki-da-jiki kafin a iya aikawa da sako ta Infra-red, ba haka abin yake ba.  Idan an yi haka ba komai, amma ba ka’ida bace cewa dole sai ta haka za a iya sadarwa.  Har wa yau, fasahar sadarwa ta Infra-red ta dara fasahar Bluetooth a wurare da dama.  

Misali, ba ka bukatar sai ka nemi abokin huldan ka ta hanyar barbaran wayar salularsa.  Da zarar ya kunna tasa shikenan. Amma Bluetooth dole ne ka bata lokaci wajen neman abokin hulda da kuma barbaro wayarsa.  Haka na’urar Infra-red, ta fi gaugawa wajen sadar da bayanai. Wannan tasa za ka iya aikawa da bayanai masu mizani mai yawa cikin kankanin lokaci, sabanin Bluetooth uwar saibi da nawa; duk kuwa da kwaskwariman da ake ta mata shekara-shekara.  Wannan ya faru ne saboda ka’idar da ke taimaka wa Infra-red sadarwa, wato Very Fast Infra-red Protocol (VIFR Protocol) ta shallake wacce ke isar ma Bluetooth, nesa ba kusa ba.  A daya bangaren kuma, wannan bai sa Bluetoth ta gaza ba kwata-kwata. 

Misali, a tsarin sadarwa ta Bluetooth ba a bukatar dole sai masu sadarwa na tsaye cif, ba motsi, sai kace gumaka.  A a, kana iya kunna Bluetooth dinka, ka sanya na’urarka cikin aljihu, ka ci gaba da harkokin ka alhali wani na karban sako daga gareka.  Haka fasahar Bluetooth ba ta saurara wa wani shamaki; ko da shamaki ko babu, kana iya aiwatar da sadarwa kai tsaye.  Ka ga kowa da nashi maziyyar kenan.  A cewan masana ci gaban fasahar sadarwa ta zamani, zai yi wahala wani ya doke wani daga kasuwa.  Domin kowanne cikin su na da nashi siffa wacce abokin mukabalar sa ba shi da ita.  A takaice dai kowanne na da fagensa, kuma zasu ci gaba da habaka lokaci-lokaci, iya gwargwadon yadda  bincike ko mu’amala da su ya kama.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.