Kumbon Hukumar NASA Ya Isa Sararin Samaniya

Kumbon da Hukumar Binciken Sararin Samaniya na Kasar Amurka ta harba, ya isa sararin samaniya. Ga takaitaccen bayani kan wannan jigila da kasar tayi.

302

A wani sabon shirin binciken sararin samaniya da take son fara gabatarwa nan da wasu shekaru masu zuwa, hukumar NASA na kasar Amurka ta cilla wani kumbo mara direba ko matuki zuwa duniyar wata.  Wannan nau’in kumbo da ta harba, wanda shi ne na farko tun shekarar 1998, ta sanya masa suna Lunar Reconnaissance Orbiter (LRO), kuma ya isa falakin wata ne a ranar Talata (22/06/2009), bayan kwanaki biyar da ya kwashe a kan hanyarsa ta tafiya.  Ya baro wannan duniya tamu ranar Alhamis, ya isa can a safiyar Talata, ya kuma fara shawagi ne da misalin karfe biyar da minti arba’in da bakwai (5:47am) na safe.

Harba wannan kumbo na musamman wanda babu direba a tare dashi, gabatarwa ne a sabon shirin bincike na musamman da hukumar ke yi kan duniyar wata, da sanin irin tsari da kimtsin muhallinsa, don bude wani sabon lale a binciken sararin samaniya.  Bayan isarsa falakin wata, shugaban kwamitin binciken Hukumar, Mr. Richard Vondrak, ya sanar da cewa tuni dai kumbon ya fara shawagi a falakin wata, don fara gudanar da aiyukan da aka tura shi gabatarwa.  Ire-iren wadannan aiyuka dai sun hada da dauko hotunan muhallin, da zayyana taswira na musamman kan gundarin wata, tare da nemo bayanai gamsassu kan yiwuwar samun ruwa da kankara da ke iya nuna cewa dan Adam na iya rayuwa a wannan bigire.  Daga cikin aikinsa har wa yau akwai nemo bayanai kan muhallin da mutane masu bincike zasu iya sauka a ciki idan sun isa wurin nan da wasu ‘yan shekaru.

- Adv -

Wannan kumbo mai suna Lunar Reconnaissance Orbiter (LRO) dai shi ne na farko da hukumar ta harba, tun shekarar 1998 da ta fara harba ire-irensa.  Kumbo ne mai sarrafa kansa, ba tare da direba ba, kuma yana iya daukan hotuna, bayan shawagin da yake yi a sararin samaniya ko falakin da aka tura shi.  Wannan kumbo na LRO dai yana dauke ne da muhimman sassa guda bakwai masu taimaka masa wajen gudanar da aiyukansa na daukan hotuna, da taskance makamashin hasken rana, da kuma sunsuna muhallin da zai isa tun kafin ya isa wurin, don kauce wa matsala.  Har wa yau, an hada shi da na’urar da ke iya taskance irin yanayin zafi ko sanyin da ke wurin, dangane da abin da ya shafi hasken rana da makamashinta, don samun bayanai da zasu taimaka wajen kwatanta yiwuwar rayuwar masu binciken da watakil za a tura nan gaba.  Tuni dai wasu sassansa suka fara aiki bayan isarsa cikin falakin wata, wasu kuma, a cewar Mr. Richard Vondrak, sai nan da makonni biyu za a sake su don fara nasu aikin.

Hukumar NASA ta kashe a kalla dalar Amurka Miliyan dari biyar da hudu ($504M) wajen kera wannan kumbo, ta kuma harba shi ne wata guda kafin ta fara bikin murnar cikan shekaru arba’in da harba kumbon farko mai suna Apollo 11 da ya isa cikin falaki a ranar 20/07/1969.  Ta kuma sanar da cewa nan da wasu ‘yan makonni wannan kumbo na Lunar Reconnaissance Orbiter (LRO) zai fara aiko musu da hotunan da ya fara daukawa a wannan muhalli da ya fara shawagi cikinsa.  Sannan za ta fara nuna wa al’ummar Amurka hotunansa na bidiyo a yayin da yake shawagi, kai tsaye, da zarar ya isa tazarar kilomita dubu tara (9,000 KM) da fara wannan shawagi.

Wannan kumbo dai, kamar sauran wadanda hukumar ke harbawa, ana lura da shawaginsa ne a wannan duniya tamu, a cibiyar bincike da ke nan kasar Amurka.  Ta haka ake sanin yaushe ya isa, wani hali yake ciki, wani irin yanayi ake son yaci gaba da kasancewa ciki, sannan, ta wannan hanya ake sarrafa sassansa, kamar dai yadda bayanai suka gabata.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.