Tasirin Hadarin Nukiliyar Kasar Japan Ga Duniya

Cikin watan da ya gabata ne kasar Jafan ta fuskanci wata girgizar kasa mai girma da karfin gaske, wanda kuma sanadiyyar haka nan take tekun kasar ya kama ambaliya (Tsunami).  Wannan ambaliya ya kwashe gidaje da garuruwa da jama’a sama da dubu talatin – tsakanin wadanda suka mutu da wadanda aka rasa inda suke – sannan ya yi mummunar tasiri a kan cibiyoyin nukiliyar kasar, wadanda suke cikin tsibiri, daidai inda wannan lamari ya auku.  A yanzu wadannan cibiyoyi na fuskantar barazanar fashewa a kowane lokaci, kuma tuni har an fara samun yaduwar mummunar tururin guba (radiation) da ke fitowa daga cikinsu.  Wannan tasa muka kawo wa masu karatu bayanai kan mummunar tasirin wannan abu dake kokarin bayyana muddin ba a dauki wani mataki mai tasiri ba.  Domin wannan matsala muddin ta fara yaduwa, ba kasar Jafan kadai za ta shafa ba, kusan duk duniya baki daya na cikin hadari. Saboda abu ne mai gamewa ba wai a jiki ko ruwa ko gidaje ko kasa kadai ba, har da iskar da ake shaka.

295

Munanan Tasirin Makamashin Nukiliya

Makamashin nukiliya na tattare ne da sinadaran kimiyya masu matukar illa ga rayuwa, musamman lokacin fashewarsa a wani wuri da aka harba ko jefa shi.  Wannan ke wajabtar da samuwar illoli da dama ga rayuka da muhallin da makamin ya fashe.  Muhalli ya shafi iskar da ake shaka a bigiren, da duwatsu ko tsaunukan da ke wannan muhalli da kuma teku ko koguna ko rafuka.  Duk idan makamin nukiliya ya fashe, zai shafe su mummunar shafa, tare da yada illolinsa ga duk wani abinda ya ta’allaka dasu; dabba ce mai rai ko wani abu dabam.

Da zarar an harba ko jefa makamin nukiliya a wani wuri, gari ne ko dajin Allah ta’ala, akwai abubuwa guda hudu da ke haddasuwa idan makamin ya fashe, har sinadaran da ke cikinsa suka yadu.  Abu na farko shi ne wata kara mai tsananin firgitarwa, wato Blast a turance.  Wannan kara mai tsananin firgitarwa ita ta kumshi kashi arba’in zuwa hamsin (40% – 50%) na bala’in da ke tattare da wannan makamashi mai narkar da rayuwa da muhalli.  Har wa yau, yawa ko karfin wannan kara mai firgitarwa ya ta’allaka ne da yanayin makamin da aka harba, a yayin da ake kera shi. Makamin da ke cike da sinadaran makamashin nukiliya mai dimbin yawa ya fi haifar da kara mafi girma da firgitarwa.  Babban abin da ke haddasa wannan kara mai firgitarwa yayin fashewar makamin nukiliya su ne wasu dimbin makamashin sinadaran kimiyya masu dauke da maddar kimiyya masu tsananin hadari ga rayuwa da muhalli.  Idan fashewa ya auku, zai haifar da wannan kara, wanda ke kunshe da iska mai bala’in tunkudowa don raunana dukkan wani abin da ta riska, tare da tarwatsa shi nan take babu kakkautawa.  Wannan kara mai dauke da wannan iska mai bala’in tunkuda na haddasuwa ne cikin ‘yan dakiku (seconds), amma tasirinsu wajen tarwatsa muhalli da abin da suka darkake, ya zarce na dukkan wata mahaukaciyar guguwa mai dauke da iska (Hurricane) da aka taba samu a duniya.  An kiyasta cewa karfin wannan kara mai firgitarwa na iya kwantar da dukkan gidajen da ke bigiren da fashewar ta auku.  Haka idan akwai hanyar dogo (jirgin kasa) a wajen, karar na iya daukan taragon jirgin ta jefar da shi wata duniya daban.

Abu na biyu cikin abubuwan da fashewar makamin nukiliya ke haifarwa shi ne wani haske mai dauke da tururin guba ko sinadaran kimiyya masu illa ga muhalli da rayuwa.  Wannan shi ake kira Thermal Radiation a turance, kuma yana fitowa ne da zarar wancan kara mai firgitarwa ta haifar da makamashin maddar kimiyya zuwa muhalli, wanda ke dabaibaye dukkan ilahirin wuri ko bigiren da fashewar ta auku cikin kasa da dakika guda.  Wannan nau’in makamashin haske mai dumi da ake kira Thermal Radiation, shi ne ya kunshi kashi talatin zuwa hamsin (30% – 50%) na makamashin da fashewar makamin nukiliya ke haifarwa.  Kuma wannan tururin haske ya kumshi nau’ukan haske ne guda uku; na farko shi ne asalin haske irin na rana da ido ke iya jure ganinsa, wanda muke da shi a nan duniya kenan (wato Visible Light), sai kuma nau’in hasken da ido ba ya iya jure kallonsa, saboda gundarin haske ne mai cike da makamashi mai dimbin yawa (wato Ultraviolet Light), na karshe kuma shi ne nau’in haske mai dauke da makamashin Infra-red, wato hasken da ke kasa da ganin dan Adam, amma yana nan kuma yana da tasiri matuka ga muhallinsa da kuma jikinsa.  Hasken makamashin nukiliya nau’in Infra-red ne ya bayyana a kasar Jafan sanadiyyar matsalar da tashoshin da ke girke da makamashin nukiliyar kasar suka samu lokacin da Tsunami da ya gataba a tsakiyar watan Maris. Kuma yana da cutarwa matuka, kamar yadda Dakta Roberts Gale, wani masanin Kimiyya a birnin Tokyo ya sanar da tashar Al-Jazeera ta turanci makonni biyu da suka gabata.

Masanin ya ce yaduwar wannan sinadarin makamashin nukiliya na haske yana mummunar tasiri a kan fatan jikunan mutane, kuma wannan tasirin na da isarwa sosai, domin bayan haddasa cutar sankara (Skin Cancer) da suke yi a jikin fatan, suna kuma tarwatsa duk sinadaran halitta masu habbaka jini da ke cikin bargon dan Adam. Don haka duk wanda wannan mummunar haske mai guba ta shafe shi, babu tabbacin zai iya rayuwa, saboda har yanzu likitoci da malaman kimiyyar kere-kere ba su samo hanyar da za ta iya maye gurbin wadanann kwayoyin sinadarai masu haifar da jini a cikin bargo ba.

- Adv -

Wadannan nau’ukan haske na cikakken tasiri wajen haddasa makantar wucin-gadi (Interim Blindness) har na tsawon mintuna arba’in, ko tabbatacciyar makanta.  Hakan ya danganta da kusancin mai idon da kuma wajen da aka samu fashewar makamin ne.  Domin haske ne da ke shiga jiki ko duk abin da yayi karo da shi, tare da mannewa ko tabbata a jikin, bayan tasirin kuna mai tsanani da ya mallaka.  Bayan dukkan wannan, tururin hasken Thermal na iya gurbata dukkan iskar da ake shaka da zarar ya fito, tare da haddasa maganadisun lantarki cikin iskar (Electromagnetic Shockwave), mai cikakken tasiri ga dukkan wani jiki, kamar yadda mayen-karfe (magnet) yake ga sauran karafa!  Da iskar da ke muhallin, da rafi ko kogi ko tekun da ke muhallin duk zai gurbata su.  Kai hatta dutse ko wani tsauni dake wannan wuri yana iya samun nasa rabon.  Idan ya samu damar saduwa da jikin dan Adam, ya kan raunana dukkan gabobinsa, ya haifar da mummunar illa ga kasusuwa da bargonsa, sannan ya karya wa jijiyoyinsa dukkan lagonsu, bayan haka, ya bi mabudan hanji ko tumbi, da huhu da kuma gangar kunne (Ear Drum), duk ya bata su ta hanyar rubar da su nan take!  Abu na karshe da wannan tururin haske ya mallaka shi ne haddasa gagarumar gobara a muhallin da fashewar ta auku.

Abu na uku da ke samuwa sanadiyyar fashewar makamin nukiliya shi ne tururin hayaki mai haifar da sinadaran kimiyya nau’in ayon, ko kuma ionization a turance.  Wannan tururin haske aikinsa shi ne ya haifar da sinadaran madda masu tattare da maganadisun lantarki (Electromagnetism), masu taimaka wa tururin hasken Thermal da bayaninsa ya gabata, don gurbata yanayin gaba daya, da hana dukkan wani abin halitta sararawa.  Wannan nau’in tururin haske na ayon shi ne kashi biyar (5%) na makamashin da makamin nukiliya ke fitarwa da zarar ya fashe.  Wadannan nau’ukan tururi guda biyu, da zarar sun watsu cikin muhalli sanadiyyar fashewa da aka samu na makamashin nukiliya a wurin, to garin ba ya iya zaunuwa har abada.   Wannan shi ne abin da ya faru da mutanen birnin Pripyat da ke kasar Yukiren (Ukraine), lokacin da wata masana’anta ko cibiyar nukiliya ta fashe, dole suka bar garin, don ba zai zaunu ba.  Saboda dukkan iska da ake shaka, da ruwa da ake sha da kuma muhallin shi kansa, duk sun gurbace matukar gurbacewa; wata halitta mai rai ba ta iya jure zaman wurin, balle ta amfana da abin da ke muhallin wajen gaba daya.  Dole garin, duk da girma da kuma kayan alatun da ke cikinsa, ya zama fako, kowa ya gudu.  Ire-iren wadannan garuruwa da ke samun kansu cikin wannan hali ana kiransu Nuclear Ghost Town a harshen turancin malaman kimiyya

Nau’in abin da ke samuwa daga fashewar makamin nukiliya na karshe shi ne hayaki mai dauke da haske, wanda ke tudadowa don mamaye ilahirin muhalli ko bigiren da fashewar ta auku.  Wannan hayaki, wanda dan Adam na iya ganinsa, yana fitowa ne tare da masifaffen karar fashewar makamin, a matsayin wata gagarumar da’ira ta hayaki, wacce ke haurawa sama don yada dukkan sinadaran tururin hasken da bayaninsu ya gabata a baya.  Da zarar wannan hayaki ya yi ziri zuwa sama, sai ya warwatsu, ya yi wata rumfa kamar lema, don tarwatsawa da yada wadannan sinadaran guba, wadanda ke gurbata muhalli gaba daya.  Wannan tarin hayaki shi ne ke daukan kashi biyar zuwa goma (5% – 10%) na yawan makamashin da makamin nukiliya ke fitarwa yayin fashewarsa.  To me ye kimar hasarar da ke iya shafan rayuka ko ababen da ke kusa da wajen wannan fashewa?

Duk lokacin makamin nukiliya nau’in Atomic Bomb ya fashe a wuri, duk wani abin halitta – ko gida ko dutse ko tsauni ko wani teku – da ke kusa da wurin fashewar da gwargwadon nisan mil guda, zai hallaka gaba daya.  Babu abin da za a samu mai amfani tattare da shi.  Idan kuma nau’in Hydrogen Bomb ne, duk abin da ke gwargwadon mil biyar ko nisan kilomita takwas zai hallaka nan take.  Domin Hydrogen Bomb ya fi Atomic Bomb masifa wajen hasarar rayuka da muhalli.  Bayan nan, idan kuma nisan da ke tsakanin wata halitta ko gine-gine ya kai mil daya da digo biyu, ko gwargwadon kilomita biyu kenan, to, zai samu mummunar illa wanda zai sa a gwammace rasa shi ma gaba daya.  Idan kuwa nau’in Hydrogen Bomb ne, duk wanda ke iya nisan kilomita bakwai da fashewar na iya samun wannan mummunan illa.  Idan, a daya bangaren kuma, fashewar ta auku a nisan kilomita uku ne, to duk wanda ke kusa da wajen iya takin wannan nisa na samun illa mummana wacce bata kai mutu-kwakwai-rai-kwakwai ba.  Irin wannan illar na iya samun wanda ke nisan kilomita goma shabiyar tsakaninsa da fashewar Hydrogen Bomb.

A karshe, halitta na iya samun takaitattun raunuka ko ‘yar karamar dameji, idan gine-gine ne, muddin aka samu tazarar kilomita biyar tsakaninta da wajen fashewar makamin nukiliya nau’in Atomic Bomb, ko kuma nisan kilomita ashirin da bakwai idan nau’in Hydrogen Bomb ne.  Wadannan, a takaice, su ne kadan cikin bala’i ko masifar da ke dauke cikin makamashin nukiliya.  Shi yasa hukumar kasar Jafan, da na kasar Amurka duk suka rikice.  Domin idan wadannan cibiyoyin taskance makamashin nukiliya na kasar Jafan suka fashe, tasirinsu na iya ambaliya cikin teku, har ya isa kasar Amurka. Idan kuwa ya isa can, to Allah kadai ya san mutum nawa za su rage a duniya! Don haka kasar Jafan ke ganin, muddin lamari ya kai wani hali, to, za su binne wadannan tashoshin ma gaba daya a karkashin kasa…kada mummunar tasirinsu ya shafi duniya baki daya.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.