Bayani Kan Ɓangarorin Wayar Salula da Dalilan Tsada ko Araharta (4)

Ma'adanar Wayar Salula (2)

Daga bayanan da suka gabata mai karatu zai fahimci saurin ci gaba da ake samu wajen ingantawa da kuma ƙarfafa girma da mizanin ma’adanar wayar salula, musamman ma’adanar wucin-gadi, wato: “RAM”. 

95

Ma’adanar Wayar Salula (2)

A ɗaya ɓanagaren kuma, ma’adanar RAM dai ma’adana ce ta wucin-gadi.  Ma’ana, idan wayarka tana kunne ne ma’adanar ke iya adanawa da kuma sarrafa bayanai.  Amma da zarar ka kashe wayar, dukkan bayanan dake cikinta sai su ɓace baki ɗaya; ta gama aikinta na wannan lokacin kenan.  Da wannan yasa ake kiranta da suna: “Volatile Memory”.  Ma’ana, nau’in ma’adanar dake iya taskancewa da sarrafa bayanai na wani lokaci, wanda da zarar ma’adanar ta rasa makamashin lantarki, sai bayanan su ɓace.

Aikin wannan ma’adana shi ne, a duk sadda ka kunna wayar salula, duk wata manhaja ko masarrafa (Application) da ka buɗo, nan take zuwa ta zauna, har sai ka gama amfani da manhajar ka rufe, sannan bayanan su koma wancan ɗayar ma’adanar ta ROM.  Misali, idan ka buɗe manhajar rubutawa da aika saƙonnin tes, wato: “Message” a wayar salula mai ɗauke da babbar manhajar Android, nan take wayar za ta ɗauko bayanan wannan manhaja daga asalin ma’adanar ROM, sai ta jibge su a ma’adanar RAM, don baka damar ma’amala da manhajar.  Da zarar ka gama aika saƙo kuma ka rufe manhajar, sai bayanan su ɓace.  Haka idan ka buɗo manhaja sama da ɗaya, duk bayanansu za su zauna ne a wannan ma’adana ta RAM.  Wannan ke nuna cewa, muddin kana son wayarka ta riƙa sarrafa bayanai cikin sauƙi, to, ya zama tana ɗauke ne da isasshen ma’adanar wucin-gadi, wato RAM.

Kamar ma’adanar ROM da bayaninta ya gabata, ma’adanar RAM ma ta kasu kashi-kashi ne wajen girman mizani ko ƙarancinsa.  Mafi ƙarancinta a wannan zamani da muke ciki shi ne 1GB.  A sama kuma akwai 2GB, da 4GB, da 6GB, da 8GB, kai har 12GB akwai.  Bayan girman mizani kuma, ma’adanar RAM mataki mataki ce wajen inganci da saurin sarrafa bayanai.   Galibin wayoyin salular zamanin yau suna ɗauke ne da nau’in RAM  mai ƙarancin cin makamashin lantarki ko batir.  Wannan nau’i shi ake kira: “Low Power Double Data Rate”, ko LPDDR a gajarce.   Akwai wayoyin salula dake ɗauke da RAM nau’in LPDDR4, da LPDDR4X.  Sai LPDDR5,  da kuma LPDDR5X, wanda shi ne ƙololuwa a yanzu.  Kamfanin Samsung ya bayyana cewa nan da wani ɗan lokaci kaɗan zai fitar da sabon nau’in RAM na wayar salula mai mizanin LPDDR6 da kuma LPDDR7.  Kamar girman mizani ne, iya girma iya tsadar wayar salula.  Don haka, galibin ƙananan wayoyin salula masu araha, za ka samu suna ɗauke ne da ma’adanar RAM mai ƙarancin mizani, kuma mai ƙarancin tagomashi wajen sarrafa bayanai.

Daga bayanan da suka gabata mai karatu zai fahimci saurin ci gaba da ake samu wajen ingantawa da kuma ƙarfafa girma da mizanin ma’adanar wayar salula, musamman ma’adanar wucin-gadi, wato: “RAM”.  Akwai da suka haddasa hakan.

- Adv -

Na farko, dandazon bayanai da ake samu sanadiyyar yawaitar kayayyaki da na’urorin sadarwa na zamani a kowane daƙiƙa, ya lazimta samar da ma’adana mai tagomashi wajen sarrafa waɗannan bayanai a wayoyin salula.  Misali, ana yawan ɗaukan hotuna sosai da wayoyin salula yanzu, kuma galibin hotunan nan masu inganci ne, wato: “High Resolution Images”.  Ire-iren waɗannan hotuna kuma suna ɗaukan wuri sosai a ma’adanar waya, sannan idan ka tashi amfani dasu ma, suna buƙatar masarrafar waya mai ƙarfi don ɗauko su daga asalin ma’adanar  wayar kai tsaye, zuwa ma’adanar wucin-gadi.

Dalili na biyu shi ne, wayoyin zamani na buƙatar tsarin sarrafa bayanai cikin hanzari a ƙanƙanin lokaci.  Wannan shi ake kira “High Refresh Rate”.  Ma’ana, iya ƙarancin lokacin da waya ke iya sarrafa wani umarni da ka bata ko wanda ke aukuwa lokaci zuwa lokaci.  Mafi mahimmancin ɓangaren wayar salula dake taimakawa wajen aiwatar da wannan aiki shi ne ma’adanar wucin-gadi, wato “RAM”.  Wannan yasa dole kamfanoni ke ƙoƙarin samarwa tare da inganta wannan ɓangare na waya.

Dalili na uku shi ne haɓaka da bunƙasar fasahar Artificial Intelligence (AI) a wayoyin salula.  Wannan tsari ne da ya shafi koyar da na’urar sadarwar zamani wasu daga cikin ɗabi’un ɗan adam – irin su tunani, hazaƙa, basira, hankali da iya tantance bambancin dake tsakanin abubuwa mabanbanta cikin ƙanƙanin lokaci, sanadiyyar sanayya da sabo da ganin abin.  Cin nasarar wannan fasaha na AI ya ta’allaƙa ne kacokam kan ma’adanar wucin-gadi na wayar salula.

Dalili ba huɗu dake haddasa saurin haɓaka da bunƙasar ingancin ma’adanar wayar salula musamman ma’adanar wucin-gadi, wato: “RAM”, shi ne marhalar da ake kai yanzu na ficewa ko hijira daga marhalar sadarwar wayar salula na 4, wato “4th Generation” ko “4G” (LTE), zuwa marhala ta 5 da ake kira: “5th Generation” ko “5G” a gajarce.  Ƙarƙashin wannan sabuwar marhala ta sadarwa na 5G, kamar yadda muka nazartu a kai a shekarar da ta gabata, za a samu dandazon bayanai masu ɗinbin yawa, tare da na’urori nau’uka daban-daban na sadarwa, waɗanda za su riƙa musayar bayanai a tsakaninsu, ta amfani da tsarin musayar bayanai mai girman mizani a mafi takaituwan lokaci.  Tsarin sadarwa a wannan yanayi na buƙatar waya mai inganci, wacce ke ɗauke da na’urar sarrafa umarni na bayanai (Processor) mai ƙarfi, tare da ma’adanar wucin-gadi mai saurin aikawa da karɓan bayanai cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.

Waɗannan dalilai, a taƙaice, su ne suka sa a halin yanzu ake samun ci gaba cikin gaggawa, wajen ingantawa da haɓaka na’urorin sadarwa na zamani, ba ma wayar salula kaɗai ba.  Kuma siffatuwa da wannan yanayi ko rashin hakan ke sa tsada ko rashin tsadar wayar salula.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.