Tasirin Ci Gaban Kimiyya da Fasaha Ga Rayuwa da Zamantakewar Dan Adam a Duniya (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar jumma’a, 13 ga watan Disamba, 2019.

214

Mabudin Kunnuwa

A cikin littafinsa mai suna: Our Posthuman Future: Consequences of the Biotechnology Revolution, wanda ya rubuta a shekarar 2002, Farfesa Francis Fukuyama ya shimfida bayanai kwarara kan hakikanin inda rayuwar xan adam ke fuskanta da kuma inda ake sa ran za ta fuskanta nan gaba; a dunkule, yana hasashe ne, ta hanyar dalilai da hujjoji tabbatattu a lokacin da yake rubutu (2002), kan yadda rayuwa a wannan duniya za ta kasance, sanadiyyar tasirin ci gaban da ake samu a fannin kimiyyar sinadarai da fasahar kere-kere, wato: Biotechnology.  Ire-iren ci gaban da aka fara samu a lokacin da yake rubutun wannan littafi dai sun hada da magunguna ko kwayoyi masu sanya xan adam farin ciki, da waxanda ke janye wa xan adam bakin ciki da damuwa; yaji ya koma wasai kamar ba abinda ke damunsa a rayuwarsa. Sauran sun hada da ci gaban da ake samu wajen iya canza sinadaran xabi’ar halittar xan adam.  Wannan tsari shi ake kira: “Genetic Modification”, ko “Genetic Engineering”.  Waxanda suka saba karatun wannan shafi shekaru goma da suka gabata zasu tuna makalolin da muka jero kan wannan maudu’i na sinadaran xabi’ar halitta, wato: “Genetics”.

Farfesa Fukuyama yace an fara tunanin canza sinadaran xabi’ar halittar xan adam don gano nau’ukan kwayoyin halittar da ake haifar mutum dasu masu haddasa masa cututtuka.  Manufar ita ce a cire waxannan kwayoyin halitta, a canza su da waxanda ba su da matsala, don a haifi jariri salin-alin.  Bayan wannan, an fara gano hanyoyin shigar da wasu dabi’o’i na musamman cikin kwayar halittar jariri gabanin a haifeshi, don samar da ‘ya’ya masu siffofi na musamman; kamar hazakar karatu, da kaifin basira, da saurin fahimta, da kuma karancin mantuwa.  Wannan ke nuna cewa nan gaba masu kudi zasu rika zuwa wajen likitoci don a tsara musu ‘ya’ya masu siffofi na musamman, waxanda ba za su kamu da cututtuka irin su cutar kanjamau, ko sikila, ko wasu munanan cututtuka ba.

A daya daga cikin shirye-shiryenta na mako a shekarar 2017, tashar rediyon BBC Inquiry ta kawo bayanin wata fasaha mai suna CRISPR, wacce ita ce hanya mafi sauki da aka samar wajen iya nazarin sinadarai da kwayoyin halittar xan adam, da iya gano kwayoyin da suke da matsala, da iya cire su, da iya maye gurbinsu da wasu lafiyayyu, cikin sauki kuma ba tare da kashe kudade masu dimbin yawa ba.  Samuwar wannan hanya, a cewar masana, babbar bala’i ce.  Domin kwararru marasa kishin jinsin xan adam na iya amfani da fasahar wajen kasuwanci – ta hanyar samar da ‘ya’ya masu siffofi na musamman.  Wannan shi ake kira: “Designer Babies”, kamar yadda za ka iya zuwa kamfanin kera motoci ka musu bayanin irin motar da kake so; su kera maka ka biya.

- Adv -

A bangaren qwaqwalwar xan adam ma an samu ci gaba sosai. Makanta da kurumtaka sun kusa zama tarihi a rayuwar xan adam ta yau da abin da zai biyo baya.  Ana kan samar da sinadaran fasahar gani da waxanda suka shafi samar da kafar ji ga waxanda suke da matsalar gani da ji.  Waxannan fasahohi dai ana sigar dasu ne cikin jikin mara lafiya, suyi yawo a cikin jini don tantance bangarorin jijiyoyin qwaqwalwar dake da matsala, masu kashe ganinsa ko jinsa, sannan su maye gurbinsu da lafiyayyun jijiyoyin sadarwa da ake kira: “Neurons”.  Nan ba da dadewa ba za a samar da tsarin hada qwaqwalwar xan adam da na’urorin sadarwa, don tantance bugawar qwaqwalwa da kokarin hararo tunanin da manufa ko niyyar xan adam.

A cikin daya daga cikin shirye-shiryenta na watan Nuwamba mai suna: “Outlook”, tashar rediyo na BBC World ta yi hira da wani da likita da ya dasa wata na’ura a qwaqwalwar wani bawan Allah dan qasar Faransa, wanda kafin wannan lokacin yayi shekaru kusan goma ba ya iya motsa bangaren jikinsa na dama, sanadiyyar hadari da yayi da mota.  Ana dasa masa wannan na’ura, nan take ta fara karanto bayanan dake cikin qwaqwalwarsa, wanda ta hakan ta gano jijiyoyin aika sakonnin da suka mace a qwaqwalwarsa, ta dasa sababbi sannan ta fara taimaka masa iya motsa bangaren jikinsa da ya shanye.

Galibi a al’adar rayuwa mun san jinsin xan adam guda biyu ne; namiji da mace.  Akwai waxanda Allah ke halittarsu da bangarorin duka jinsin.  Amma a halin yanzu ci gaban kimiyyar halitta da sinadarai sun kai ci gaban da ake iya mayar da namiji ya koma mace – tare da dukkan bangarorin mace – kamar yadda ake iya mayar da mace ta koma namiji.  Wannan tsari ya samo asali ne daga masu akidar kin wani jinsi da Allah Ya halicce su a kai. Waxannan su ake kira: “Non-Binary Gender Identities”.

Daga wannan mako in Allah Yaso, zuwa makonnin dake tafe, za mu ci gaba da kawo bayanai filla-filla kan irin ci gaban da aka samu a baya da wanda ake samu yanzu a fannin kimiyya da fasahar sadarwar zamani, da abin da hakan zai iya haifarwa a siyasance, ko addinance, ko al’adance.

A mako mai zuwa za mu ci gaba.  A ci gaba da kasancewa tare damu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.