Mahimman Abubuwan Ci Gaba a Fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwa a Shekarar 2021 (3)

Manhajar "For You" na TikTok

Wannan ginanniyar manhaja mai suna: “For You”, ita ce ke tarkato maka nau’ukan mutane (gwaraza) da suka yi fice a dandalin, don ka bi su ko yi abota dasu.  Da zarar ka saukar kuma ka hau manhajar TikTok a karon farko, kana gama rajista da fara bibiyar mutane, wannan mahaja za ta fara aikinta kai tsaye. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 25 ga watan Fabrairu, 2022.

185

Fasahar “For You” Ya Kara Wa TikTok Tagomashi

Cikin shekarar 2021 ne kamfanin Byte Dance, wanda ya mallaki Dandalin Abota na TikTok, ya yi fice a duniya sama da kowane kamfanin sadarwa na.  Hakan ya biyo bayan adadin mutanen da suka saukar da manhajar ne a cibiyar manhajoji na Play Store, inda aka samu mutane sama da biliyan daya da suka saukar da manhajar akan wayoyinsu.  Wannan shahara dai ya samo asali ne sanadiyyar wani garambawul da kamfanin yayi, inda ya gina wata manhajar tantance bayanai (Algorithm), don nuna wa masu amfani da manhajar shahararrun mutanen da zasu bi.

Wannan ginanniyar manhaja mai suna: “For You”, ita ce ke tarkato maka nau’ukan mutane (gwaraza) da suka yi fice a dandalin, don ka bi su ko yi abota dasu.  Da zarar ka saukar kuma ka hau manhajar TikTok a karon farko, kana gama rajista da fara bibiyar mutane, wannan mahaja za ta fara aikinta kai tsaye.  Bayan ta gama fahimtarka gaba daya, sai fara bijiro maka da irin mutanen da ta fahimci sun dace da dandanonka.  Wannan ke sa ka ta cin karo da wasu mutane shahararru a dandalin, wadanda baka yi tunaninsu ba.  Kaddamar da wannan sabon tsari a dandalin ya kara wa manhajar TikTok shahara, inda a shekarar 2021 kadai ya samu kudin shiga sama da dalar biliyan 50.  Kusan tiriliyon 25 kenan a kudin Najeriya, kamar yadda aka sanar a watan Nuwamba. Bayan shekarar ta kare, an kiyasta kimar kamfanin zai kai tsakanin dala biliyan 350 zuwa 400.  Tun kaddamar da kamfanin a shekarar 2016, manhajar TikTok bata samu irin shaharar da ta samu tsakanin shekarar 2020 zuwa 2021 ba.  Musamman sadda tsohon Shugaban kasar Amurka Donald Trump yayi yunkurin hana amfani da manhajar a kasar sadda yake shugabanci.  To yaya wannan manhaja ta “For You” take aiki?

- Adv -

A tsarin gudanar da shafukan sada zumunta a manhajar kimiyyar sadarwa na zamani, hankalin jama’a kan koma ne kan bayanan da abokansu ke zubawa.  Wadannan bayanai dai sun hada da rubutattun bayanai, da hotuna, da bidiyo da kuma sauti, a wasu lokuta.  Wannan tsari shi ake kira: “Data-centric”, kuma masu gudanar da dandalin kan samar da manhaja ce ta musamman don tantance irin bayanan da za su nuna wa mutane.  To amma a bangaren TikTok ba haka lamarin yake ba.  kasancewar shafi ne na bidiyo wanda ke dauke da sauti (da rubutu a wasu lokutan), yasa kamfanin bai yi amfani da wancan tsarin ba.  Sai ya kirkiri fasahar “For You”, mai dauke da abubuwan al’ajabi.

Manhajar “For You” na kururuta mutanen da suka shahara ne a dandalin, ba wai bayanan da suke dorawa ba.  Matakin farko da manhajar ke bi wajen gudanar da aikinsa shi ne tantance bayanan da mai shafi ya rubuta dangane da rayuwarsa.  Irin su adireshi, da kasa, da jinsi, da addini, da abubuwan da yake sha’awa, da kuma na’ukan bidiyon da ya kalla a baya; shin, ya kallesu daga farko har karshe ne, ko dai zuwa tsakiya kawai ya kalla ya barsu?  Sai mataki na biyu, shi ne bibiyar bayanan da suka shafi wayar salular da yake amfani da ita wajen ta’ammali da manhajar TikTok.  Wannan ya hada da nau’in wayar, da irin manhajar da take dauke dashi, da bigirenta a duniya, da kuma lambobin wayar da take dauke dasu, da sauran bayanai makamantansu.  Sai mataki na uku, shi ne bayanai kan wadanda yake bi (follow) a dandalin, da irin bidiyon da ya kalla, da alakar dake tsakaninsa da wadanda yake bi.

Bayan ta tattaro dukkan wadannan bayanai, sai ta tantance tayi ninkaya cikin rumbun bidiyon dake dandalin gaba daya, ta debo mutanen da suka shahara, wadanda bayanansu suka yi canjaras da naka.  Sai ta bijiro maka dasu kai tsaye, kamar kai ne kaje ka zabo su.  Duk bidiyon da ka gani a bangaren “For You”, to, an taco maka su ne daga bayanan da aka tankado daga gareka, kai tsaye.  Wannan tsari da salo shi ne abin da ya sauya alkiblar kasuwancin kamfanin Byte Dance, saboda burge mutane da yake yi.  Shi yasa tsarin ya samu karbuwa sosai, har wannan manhaja ta TikTok ta shahara fiye da sauran dandamalin abota dake Intanet ko wayar salula.

A tare da cewa ba manhajar TikTok bace kadai ke da tsarin tantance bayanai don kururuta su, sai dai natsa tsarin yayi fice; watakila saboda dandalin bidiyo ne.  A halin yanzu da dama cikin mutane sun shahara a TikTok, kuma wannan ya baiwa kamfanonin kasuwanci wata dama don tallata hajojinsu ta hanyar wadannan shahararrun mutane.  Da yawa cikin bidiyon da kake kallo inda za ka ga mai bidiyon na ta’ammali da wasu hajoji na kasuwanci – tufafi ne, ko wayar salula, ko kwamfuta, ko nau’in abinci, ko abin sha – galibi za ka samu yana tallata hajar ce ga wani kamfani.  Ire-iren wadannan mutane ana kiransu “Social Influencers”.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.