YouTube: Taska Mafi Tsada Da Haɗari a Intanet (2)

Fa'idojin Shafin YouTube

A shafin YouTube akwai tsofaffin saƙonnin bidiyo masu ɗauke da abubuwan tarihi da suka wuce da daɗewa; wasu ma tun kafin a samar da fasahar Intanet a duniya. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 26 ga watan Mayu, 2023.

143

Taska Mai Tsada

Dandali ko shafi ko manhajar YouTube, taska ce mai ɗauke da mafi tsadan abubuwa na amfani a rayuwa – duniya da lahira.  Kusan tun sadda aka samar da wannan mahalli a Intanet nake amfani dashi, har zuwa yau.  Kuma na amfana sosai da wannan taska mai tsada.  Ga kaɗan daga cikin fa’idojin da masu ziyara za su iya samu a wannan taska ta duniya mai cike da amfani:

Jakar Magori

Shafin YouTube “Jakar Magori” ce; komai kake so akwai a ciki.  Idan kaga baka samu ba, to ɗayan biyu: ko dai baka san inda za ka samo shi bane, ko kuma baka san me kake nema ba.  Daga ilimin kimiyya, da fasaha, da sadarwa, da likitanci, da addini, da al’ada, da zamantakewa, da motsa jiki, da siyasa, da kwamfuta, da kanikanci, da ilimin ƙasa, da fannin sararin samaniya, zuwa yadda ake ƙera motoci, da jiragen sama, da kasuwanci, har zuwa yadda ake gudanar da rayuwa.  Duk kana iya samunsu a tsarin bidiyo a shafin YouTube.  Ga kaɗan daga cikin shahararrun fannonin da ake samun ilmi mai tsada nan.

Fannin Kimiyya Zalla

Akwai tashoshi da yawa dake yaɗa ilimomin dake fannin kimiyya zalla, da yawa.  Daga kan ilmin sararin samaniya (Astronomy), zuwa ilmin falaki, da ilimin likitanci, da makamashi, da mahalli, da sinadarai, da yadda ake haɗa magunguna a tsari na zamani, duk ana samu a YouTube.

Fannin Kimiyyar Sadarwa

Wannan na cikin fannonin da ilmi ya yawaita a cikinsu sosai a YouTube.  Daga ilmi kan kwamfuta, da wayar salula, da fasahar Intanet, da yadda ake ginawa da tsarawa da kuma tafiyar shafukan yanar sadarwa, har zuwa kan tsari da yanayin sadarwa na duniya wanda kamfanonin wayar salula ke amfani dashi wajen aiwatar da sadarwa.  Ba wannan kaɗai ba ma, masu ɗora waɗannan nau’ukan ilmomi shahararrun masana ne, waɗanda suka ci suka sha a wannan fanni a duniya.

Siyasa da Zamantakewa

A ɓangaren siyasa da zamantakewa kuma akwai saƙonnin bidiyo da yawa.  Tun daga kan siyasar duniya, zuwa siyasar ƙasashe, duk suna nan birjik.  Kafofin yaɗa labaran cikin gida suna da tashoshi a kan YouTube, kuma suna hakaito mana kusan dukkan abin da ke faruwa a fagen siyasa da zamantakewa na ƙasar nan.  Ta wannan shafi za ka san me ke faruwa a ƙasarka da ma sauran ƙasashen duniya.

- Adv -

Tarihi

A shafin YouTube akwai tsofaffin saƙonnin bidiyo masu ɗauke da abubuwan tarihi da suka wuce da daɗewa; wasu ma tun kafin a samar da fasahar Intanet a duniya.   Wannan na cikin abin da yasa wannan taska ta zama mai tsada.  Galibin abubuwan da suka faru tsakanin shekaru 50 zuwa 80 da suka gabata, duk kana iya samunsu a YouTube.  Misali, bikin samun ‘yancin kai na Najeriya da aka yi, da jawaban tsohon Firanministan Najeriya Marigayi Abubakar Tafawa Ɓalewa, da jawaban Firimiyan Arewa, Marigayi Sardaunan Sakkwato, da jawaban su Shagari marigayi, da su Abatcha, kai hatta juyin mulkin da aka a lokuta daban-daban, duk akwai bidiyo ɗauke dasu a YouTube.  Wannan hanya ce mai sauƙi wajen taskance tarihi a tsarin bidiyo.

‘Yancin Faɗin Albarkacin Baki

Daga cikin fa’idar dake ɗauke tattare da YouTube akwai ba da damar faɗin albarkacin baki.  Akwai jama’a da dama dake wasu ƙasashe da ba su samun daman faɗin halin da suke ciki na gaskiya, sai ta hanyar YouTube.  Waɗanda ke ƙasashe irin su Koriya ta Arewa, da Ƙasar Iran, da ƙasashe irin su Venuzuela da sauransu, kan yi amfani da tsarin sadarwa na Virtual Private Network (VPN), wajen ɗora saƙonnin bidiyo ga duniya kan haƙiƙanin halin da suke ciki.

Nesa A Kusa

Shafin Youtube na bai wa mutane damar shirya taro kai tsaye ta amfani da fasahar YouTube Live, wanda ke ɗauke a shafin ko manhajar.  Ta amfani da wannan fasaha, kana iya gayyatar mutane su halarci taro kai tsaye; kana gabatar da jawabi suna bibiyarka, a ko ina suke a duniya.  Malamanmu kan yi amfani da wannan tsari wajen gabatar da karatuttukansu na mako ko wata ko kuma muhadara.  Wannan hanya ce mai sauƙi wajen ɗaukan ilmi.  Bayan an gama shirin, nan take za a taskance bidiyon.  Ko baka samu halarta a sadda ake gabatar da shirin ba, kana iya kallon bidiyon a duk lokacin da ka samu dama.  Abin da kake buƙata kawai shi ne kuɗin data.

Faɗakarwa Da Ilmantarwa

Ta hanyar YouTube Malamai hamshaƙai daga ko ina na sassan duniya suna gabatar da faɗakarwa ta hanyar karatuttuka, da huɗubobi, da nasihohi, da kuma muhadarori da ake shiryawa a ƙasashensu.  A ɓangarenmu nan, kusan dukkan manyan Malamanmu na Najeriya, ba na arewaci kaɗai ba, suna da tashoshi na musamman a shafin YouTube. Kuma ana ɗora karatunsu, da huɗubobinsu da muhadarori da suke gabatarwa.  Ta wannan hanya za ka amfana da karatukan malaman da a baya sai dai kaji sunayensu, ko ganinsu baka taɓa yi ba, amma yanzu ga su warewake kana ganinsu, kuma kana jin karatunsu kyauta.

Ilimi A Aikace

A wannan kafa ne kaɗai za ka ga yadda ake koyawa ko karantar da ilimi a aikace, musamman kan abin da ya shafi kimiyyar fasahar sadarwa na zamani.  Haka dukkan sauran fannonin rayuwa ma.  Hatta ɓangaren ƙere-ƙere; haka za ka ga komai a aikace, yadda ake gudanar dashi.  A ɓangaren addini ma akwai yadda ake koyar da wanka, da alwala, da sana likkafani ga mamaci, da yadda ake taimama.  Komai za ka ganshi a aikace ne, babu ƙwange.

Waɗannan, a taƙaice, su ne nau’ukan abubuwan fa’ida da wannan shafi ke ɗauke dasu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.