Satar Zati a Kafafen Sadarwa na Zamani (6)

Wannan shi ne kashi na 6 a jerin binciken da muke gabatarwa kan Satar Zati a kafafen sadarwa na zamani. A sha karatu lafiya.

119

Dabaru da Hanyoyin Satar Bayanai (2)

Tsintar Bayanai a Bolar Intanet

Bayan wancan bola ta zahiri da Dan dandatsa zai iya zuwa ya tsinci bayanai masu alaka da kamfani ko ma’aikata don aiwatar da ta’addancinsa cikin sauki, akwai kuma bola ta Intanet.  To yaya wannan bola take ne?  Idan gaggan ‘Yan dandatsa suka yi kutse cikin wani shafi suka sato bayanai na jama’a (irin su adireshin Imel, da Kalmar sirri, da ranar haihuwa, da lambobin katin banki, da lambobin waya da sauransu), sukan watsar dasu ne a wata bola.  Wannan bola ba wani wuri bane face Gidan yanar sadarwa mai dauke da zauren hira (Internet Forums), ko su gina shafi na musamman su zuba bayanan a ciki; duk mai so yazo ya kwasa.  Wannan ita ce bola nau’in na farko.  Nau’i na biyu kuma tana can karkashin kasa a Intanet, wacce ake kira: “Dark Net”.

Wannan wani mahalli ne dake dauke da shafukan kazantattu, inda ake saye da sayarwa na miyagun kwayoyi da karuwanci da ta’addanci da duk wani nau’in aiki na laifi.  Wannan wuri shi ake kira “Dark Net”, wanda nan gaba zamu samu lokaci don tattaunawa kan haka.  A wannan wuri akwai shagunan sayar da bayanan jama’a da aka sato daga shafukan Intanet na zahiri da muke gani.  Wani abin mamaki shi ne, wannan bangare na Intanet mai suna “Dark Net” shi ne kaso 80 cikin 100 na abin da muke ji ana kira da suna: “Internet.”  Abin da muke gani kuma muke mu’amala dashi a zahiri na Intanet duk bai wuce kashi 20 ba cikin 100.  Sauran duk a “Dark Net” suke.

‘Yan kananan kwari daga cikin ‘Yan dandatsa kan je wadannan shafuka ne don tsintar bayanan jama’a cikin sauki, don aiwatar da wani nau’i na ta’addanci.  Ko dai suje bolar Intanet ta zahiri, ko kuma suje babbar bola dake bakar kasuwar Intanet mai suna “Dark Net”, su saya ko su tsinta.  Iya gwargwadon yadda hajar take.

- Adv -

Sanarwar Neman Aiki na Bogi

A wasu lokuta masu neman sace bayanan mutane kan buga sanarwar neman aiki a wata ma’aikata ta hakika ko ta bogi, don jawo hankalin marasa aikin yi tare da sace bayanan da za su zuba da hannunsu.  Misali, akwai shafukan da ake kira: “Internet Job Sites” ko “Job Search Sites”.  Wadannan shafuka ne cikakku masu dauke da sanarwar neman aiki a kamfanoni ko hukumomin gwamnati ko ma’aikatu masu zaman kansu.  ‘Yan dandatsa kan je dandalin sada zumunta don sanar da cewa ana neman aiki a ma’aikata kaza, sai su ba da adireshin shafin da suka samar, mai dauke da wurare ko gurabun shigar da bayanai.  Da zarar ka je wurin ka shigar da dukkan bayananka a matsayinka na mai neman aikin yi, sun samu bayanai cikin bulus.  Shi yasa, akwai sanarwar neman aikin yi da yawa da tayi ta yawo cikin watan Ramadan da ya gabata, musamman na hukumomin gwamnati irin su: “National Insurance Commission” (NAICOM), da EFCC, da sauran ire-irensu.  Duk sanarwar bogi ce.  Sun yi ta yawo a kafafen sada zumunta musamman Whatsapp.   Abin da zai baka mamaki shi ne, idan kaje shafukan kamfanoni ko hukumomin da aka ce suna neman ma’aikata, baza ka ga wannan sanarwa ba, balle a jarida.  Saboda yawaitar yaduwar wannan sanarwa har hukumar NAICOM ta ba da sanarwar cewa babu wani yunkuri na daukan ma’aikata da suka yi, kuma abin da ke ta yawo a kafafen sadarwa na sada zumunta ba daga gare su bane.  Wannan misali ne na yadda ake yada sanarwar neman aiki na bogi, musamman a kasashe irin namu da talauci ya yawaita, rashin aikin yi yayi toroko.

Satar Bayanai ta Gidan Yanar Sadarwar Bogi

Wannan hanya tana da alaka da wacce ta gabace ta, amma ta fi ta gamewa.  Tsari ne da ya kunshi gina Gidan yanar sadarwa na bogi, mai kama da Gidan yanar sadarwar wani kamfani ko ma’aikata, daidai-wa-daida.  Wannan shi ake kira: “Phishing.”  ‘Yan dandatsa kan bude ire-iren wadannan gidajen yanar sadarwa don karkatar da abokan mu’amalar hukumomin zuwa tarkon da suka kafa musu.  Misali, suna iya gina Gidan yanar sadarwa irin na bankin “GTBank” da muke da shi a nan Najeriya, wajen siffa, da launi, da hotuna, da kuma adireshi.  Sai dai idan ka lura da adireshin za ka ga akwai bambanci kadan da na asalin.  To saboda sun san cewa jama’a basu cika damuwa da lura da iri wadannan abubuwa ba a Intanet, duk abin da tunaninsu ya kawo musu kawai sai suyi amfani dashi.  Irin wannan tsari na satar bayanan jama’a an dade ana amfani dashi, kuma har yanzu ana amfani da wannan hanya.

A ranar 5 ga watan Agusta na shekarar 2017, jaridar Vanguard ta ruwaito cewa hukumar binciken cikin gida na kasar Amurka mai suna “Federal Bureau of Investigation” (FBI) ta kama wani dan Najeriya mai suna Daniel Adekunle Ojo, inda take tuhumarsa da laifukan ta’addanci a kafafen sadarwa (Cyber Crime), da zamba-cikin-aminci (Fraud), da kuma satar zati (Identity Theft).   Hukumar FBI dai ta cafke Adekunle ne a garin Durham dake jihar North Carolina ta kasar Amurka.  Tace ya gina gidanar yanar sadarwar bogi ne (Phishing Site), inda daga ciki ya rika aika sakonnin Imel na bogi ga ma’aikatan makarantun dake birnin Minnesota da Connecticut, don karban bayanan da suka shafi harajinsu.  Hukumomin makarantun dake wadannan birane dai, ba tare da la’akari da cewa wannan sakon bogi bane, sun aika masa bayanan ma’aikata dubu daya da dari shida (1,600).

Ta amfani da wadannan bayanai na ma’aikata ne Adekunle ya mika sakon bukatar biyan rarar harajin wadannan mutane da ya samu bayanansu, ga hukumar karbar haraji ta kasar Amurka, cewa an cire musu haraji fiye da kima, don haka a biya su dalar amurka dubu dari shida ($600,000.00) – kimanin Naira miliyan dari biyu da goma sha-shida Kenan (N216,000,000.00).  Nan take hukumar ta fara biyan wadannan kudade, a zatonta shi ne wakilinsu, ta la’akari da irin bayanai da dabarun da yayi amfani dasu.  Ta biya na mutum dubu shida, inda suka aika masa dalar Amurka kimanin dala dubu talatin da bakwai cikin taskarsa – kimanin Naira miliyan goma shadaya da dubu dari biyu da goma shabiyar (N11,215,000.00) kenan.  Abin da kasa mai tsari wajen gudanar da abubuwa, nan take aka gano cewa bayanan da ya bayar ba su da alaka da mutame ko makarantun da suka aiko masa.  Nan take aka yi amfani da dabarun tsaro aka cafke shi.  Wannan kadan ne daga cikin munanan sakamakon wannan sana’a ta satar zati.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.