Web 3.0: Fasahar “Artificial Intelligence” (2)

Misalin Fasahar AI a Wayar Salula da Kwamfuta da Intanet

Daga cikin ire-iren wadannan kananan manhajoji masu fasaha akwai na kamfanin Microsoft mai suna: “Cortana”, wacce ke iya gudanar da irin wadancan ayyuka na “Siri”. Duk da cewa tana kwamfuta ne, amma yanzu an samar da na wayar salula. Duk dabi’unsu daya ne. – Jaridar AMINIYA ta Jumma’, 25 ga watan Maris, 2022.

222

Wasu Misalai Kan Fasahar “AI”

Wannan fanni na fasahar “AI”, kamar yadda na sanar a makon jiya, tuni an fara amfani dashi.  Yana nan birjiki tsakanin kwamfutoci da wayoyinmu na salula, kuma tuni mun dade muna amfani da manhajoji ko wasu na’urorin dake dauke da fasahar.  Ta bangaren sadarwa, wanda shi ne yafi yaduwa, akwai manhajoji masu fasaha (Intelligent Apps) a wayoyinmu na salula ko kwamfuta, masu dauke da wannan tsari.

Manhajar “Siri” a iPhone

Misali, wayoyin iPhone na kamfanin Apple, suna dauke da wata manhaja mai suna: “Siri”, wacce ke iya fahimtar dukkan abubuwan da kake gudanarwa a wayarka, da wuraren da kake ziyarta, da sadda kake fita gida da sadda kake dawowa aiki, da mutanen da kake yawan kira, da wadanda kake aika musu sakonnin tes, duk tana tantance su.  Haka idan akwai wasu abubuwa da ka rubuta su a kalandar wayarka don gudanar da wasu abubuwa, da zarar lokacin ya yi, nan take za ta tunatar dakai ta hanyar magana da murya. Idan wani kake son kira, da zarar ka umarceta da yin hakan, da kanta za ta kira maka shi kai tsaye.  Idan ka tambayeta inda ya kamata kaci abinci, nan take za ta yi nazarin inda kake, ta lalubo maka wuraren cin abinci dake unguwar da kake.  Abubuwan da take yi suna da yawa.

Manhajar “Cortana” a Windows

Daga cikin ire-iren wadannan kananan manhajoji masu fasaha akwai na kamfanin Microsoft mai suna: “Cortana”, wacce ke iya gudanar da irin wadancan ayyuka na “Siri”.  Duk da cewa tana kwamfuta ne, amma yanzu an samar da na wayar salula. Duk dabi’unsu daya ne.  Komai kake yi a kwamfuta ko wayar salularka tana lura dasu, kuma da zarar ka nemi wasu bayanai, nan take za ta gabatar maka.  Idan ma bata samu ba, za ta sanar dakai.  Idan wata kalma ce kake son a nemo maka ma’anarta, nan take za ta hau Intanet ta nemo maka.  Idan so kake ta baka shawara, abu ne mai sauki, wai cire wando ta ka!  Za ka iya yin hira da ita tsaf, kamar yadda kake hira ko zance da abokinka. A daya bangaren kuma, idan kana amfani da manhajar sarrafa bayanai na kamfanin Microsoft mai suna: “Microsoft 365” ko “Office 365” ne, irin su: “Word 365” ko “Excel 365” ko “PowerPoint 365”, dukkansu suna dauke da wannan fasaha ta “AI” a gine.  Duk abin da kake yi na rubutu, ko zane, ko gabatar da bayanai ta amfani da “PowerPoint”, manhajar na tantance ayyukanka, kuma dasu za ta yi amfani wajen baka shawarwari.  Abin kamar maita, amma ilimi ne tsantsa.

- Adv -

Manhajar “Google Assistant” a Google

A bangaren kamfanin Google, akwai manhajar “Google Assistant” ko “Google Voice Search”, wacce ita ma ke da ire-iren wadancan dabi’u, har ma da kari.  Wannan manhaja mai fasaha na Google, kasancewar kamfanin Google uwa ce a fannin zakulo bayanai da sarrafa su, dabi’unta suna da ban mamaki.  Tana iya tambayarka abin da kake son yi, cikin sautin mace ko namiji. Idan kace mata so kake ka karanta jaridu, nan take za ta nemo maka wadanda ke kasarku, ko inda kake ko duk inda kake so, ta baje maka su.  Sannan ma ta taya ka karanta su.  A bangaren neman bayanai kuma, manhajar “Google Search” gaba dayanta tana gine ne da wannan tsari.  Idan kai dan Najeriya ne, sai ka budo shafin Google daga https://www.google.com, misali, da zarar ka fara rubuta kalma ko jumlar da kake son neman bayanai a kai, nan take manhajar za ta hankalci abin da kake rubutawa, tana hada alaka tsakaninsa da abin da wasu ko kai, a baya, ka taba rubutawa.  Idan sun dace, kafin ka gama rubutawa ta aiko maka cikakken jumlar ko kalmar da kake son tambayowa, tare da wasu kalmomi ko jumloli masu kama ko alaka dasu.  Wannan duk aikin fasahar “AI” ne.

Manhajar “Alexa” a Amazon

Kamfanin Amazon, babban shagon sayar da kayayyaki mafi girma a Intanet a duniya, yana da nau’in manhaja mai fasaha mai suna: “Alexa”.  Wannan manhaja tana dauke ne a shafinsa na Intanet, sannan a wasu na’urorin sadarwa da yake kerawa masu suna: “Amazon Kindle”.  Kwanakin baya na yi odar littafi, sai naga an yi jinkirin aiko mini bayanin rana da lokacin da za a kawo mini.  Nan take na hau shafinsu don jin bahasi, aka hada da ita.  Haka nayi ta mata tambayoyi tana bani amsa, a karshe ta sanar dani cewa inyi hakuri, zuwa gobe zan samu cikakken bayanin ranar da littafina zai zo.  Hakan kuwa aka yi; gari na wayewa sai ga sako.  Kana iya amfani da muryarka wajen bata umarni, ka saurari labarai, da bayani kan yanayi da sauransu.  Wannan manhaja, da shi kanshi gidan yanar sadarwar na Amazon, a makare suke da wannan fasaha ta “AI”.

Fasahar “Facebook Algorithm” a Facebook

A bangaren kamfanin Facebook kuwa, an zo gidan “Artificial Intelligence.”  Dandalin Facebook an gina shi ne, daga farko har karshensa, da wannan fasaha na “AI”.  Wannan tsari na girke ne a cikin babban injin dake sarrafa Dandalin Facebook, wato: “Facebook Algorithm.”  Shi yasa, da zarar ka gama rajista a matsayinka na sabon mamba, nan take sai kaga ana nuna maka hotuna da sunayen mutanen da ka sansu a zahirin rayuwa; watakila ma unguwarku daya, ko kunyi makaranta daya, da dai sauransu.  Ba maita bane, injin ya yi amfani da bayanan da ka bayar ne, sai ya gina hasashe a kan cewa, “Tunda makaranta kaza kayi, kuma a gari ko kasa kaza aka haifeka, to, ba makawa dole ka san wane da wance da suke kasa kaza da makaranta kaza.”  Kashi 90 cikin 100 na abubuwan da kake gani a dandalin facebook na bayanai, duk wannan inji mai suna: “Facebook Algorigthm” ne ke sarrafa su.  Tun daga tallace-tallace da za ka gani, da wasu zauruka da za a bijiro maka (Suggested Groups) don kwadaitar da kai ka shiga, har zuwa irin labaran da kake gani idan ka hau shafinka na Facebook, duk wannan tsari ne dake girke cikin injin Facebook ke aiwatar dasu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.