Jawabin Steve Jobs (2005) – Kashi na Daya

Steve Jobs, wato shugaban kamfanin Apple dake kasar Amurka dai Allah yai masa rasuwa. Saboda wannan munasaba muka ga dacewar kawo wani jawabi da yayi wa dalibai yayin yaye su a Jami’ar Standford dake kasar Amurka, a shekarar 2005. Wannan shi ne kashi na daya. A sha karatu lafiya.

314

Laraba, Oktoba 5, 2011

Ranar Laraba, 5 ga watan Oktoba ne dai tsohon shugaban kamfanin Apple Inc., wato Steve Jobs, ya kwanta dama, makonni shida da mika ragamar shugabancin kamfanin.  Jobs dai ya rasu ne bayan fama da yayi da mummunar cutar sankara da ake kira Pancreatic Cancer, na tsawon shekaru bakwai.  Kafin rasuwarsa dai ana kirga shi daga cikin mutanen da suka yi tasiri mafi girma a duniya wajen habbaka harkar sadarwa da kere-kere, musamman kan wayar salula, da kwamfuta, da na’urorin sadarwa nau’uka daban-daban, da allon shigar da bayanai na kwamfuta (Keyboard), da lasifika da dai sauransu.  An kiyasta cewa Jobs ya mallaki hakkin mallaka (Patents) kan kirkirarrun kayayyakin fasahar sadarwa har wajen 338.

Shi ne ya kafa kamfanin Appl Inc. da kamfanin NeXT Computer (kamfanin da ya kera kwamfutar da aka fara amfani da ita wajen kirkira da mu’amala da fasahar Intanet), da kuma kamfanin Pixar & Disney.  Jobs ya shahara a fannin sadarwa a duniya, don haka duniya ta dauka a ranar rasuwarsa – daga shugabannin kasashe zuwa ‘yan makaranta. Daga cikin shahararrun kirkire-kirkirensa, akwai na’urar sauraren wakoki mai suna iPod da dukkan nau’ukanta – irinsu iPod Classic, da iPod Nano, da kuma iPhod Touch – da kwamfutar Mac da dukkan nau’ukanta – irinsu Macbook Air, da Macbook Pro – da wayar salula nau’in iPhone da dukkan nau’ukanta – irinsu iPhone, da iPhone 3G, da iPhone 3GS, da iPhone 4G, da kuma iPhone 4S, wadda ake gab da fitarwa kafin mutuwarsasai kuma shahararriyar na’urar sarrafa bayanan nan mai suna iPad. 

Kafin rasuwarsa, Jobs na da shekaru 56 a duniya, kuma ya mallaki tsaban kudi da kadara – dala na gugan dala – har wajen dalar Amurka biliyan takwas ($8billion), wato kusan Tiriliyon daya da biliyan dari uku da goma shabiyu kenan (N1.312 tr) a nairan Najeriya. A halin yanzu ga fassarar shahararriyar jawabin nan da ya taba yi wa daliban Jami’ar Stanford, daya daga cikin jami’o’i masu kima a duniya, ranar bikin yaye dalibai a shekarar 2005. A sha karatu lafiya:


“Rayuwarku ‘Yan Kwanaki Ne Takaitattu…”

“Ina matukar farin cikin kasancewa tare da ku a wannan rana da ake bikin yaye ku daga daya daga cikin Jami’o’i masu nagarta a duniya.  Ni kam ban samu damar gama Jami’a ba a rayuwata.  A hakikanin gaskiya ma dai, wannan shi ne lokacin da yafi kusantar da ni da bikin yaye dalibai a jami’a.  A yau zan baku wasu labarai ne guda uku daga tarihin rayuwata.  Su kenan.  Babu wani dogon bayani.  Labarai uku ne kacal.

Labarin farko dai waiwaye ne, abin da masu iya magana kan kira “Adon tafiya.”

Na yanke shawarar gujewa daga Jami’ar Reeds ne watanni shida bayan fara karatu.  Amma sai na tsaya a makarantar ina rabe-rabe tsakanin darussa, har na tsawon watanni goma shatakwas, kafin a karshe dai na gudu.  To me yasa na kasa gama karatuna?

Dalilin dai ya samo asali ne tun kafin a haife ni.  Mahaifiyata wata budurwa ce dalibar Jami’a, wacce bayan ta dauki cikina, a karshe ta yanke shawarar bayar da ni ga wasu ma’aurata bayan ta haife ni.  Ita dai tana ganin lallai ya kamata a ce ta bayar da ni ne ga wadanda suka yi karatu, don haka, haihuwata ke da wuya sai ga wani Lauya da matarsa sun zo, don sa hannu kan takardar yarjejeniyar karba ta a matsayin dansu.  To amma da suka duba suka ga namiji ne, sai suka fasa, domin su mace suke so.  Daga nan sai aka mika ni ga iyaye na (na yanzu), wadanda a lokacin suke jira, tunda wadancan ba su son namiji.  Cikin tsakiyar dare aka bugo musu waya ana tambayarsu: “Mun samu da namiji, duk da cewa ba namiji muke tsammani ba; kuna bukatarsa?”  Sai nan take suka ce: “Sosai kuwa.”   Sai bayan an mika ni ne daga baya asalin mahaifiyata ta gano cewa ashe wanda ya karbe ni bai gama Jami’a ba, matarsa ma ko sakandare bata gama ba.  Wannan yasa mahaifiyata ta ki sa hannu a kan takardar yarjejeniyar da aka rubuta.  Sai da aka yi ta mata magiya, da alkawarin cewa za a sa ni a makaranta har sai na gama, sannan ta sa hannu kan yarjejeniyar.

Haka kuwa aka yi.  Bayan na cika shekaru 17 aka sa ni a Jami’a.  To amma sai nayi ragon azanci na zabi Jami’a mai dan karen tsada, irin Jami’ar Stanford, inda aka wayi gari duk albashin iyayena yana karewa ne wajen biyan kudin makarantar.  Bayan tsawon watanni shida sai na ga wannan tsari bai da wata fa’ida.  Ni dai ban da wani tunani kan yadda zan tafiyar da rayuwata nan gaba, balle tunanin yadda karatun Jami’a zai iya taimaka mini cinma burina a rayuwa.  Amma ga shi duk dan abin da iyaye na ke samu na albashi na karewa wajen karatun.  Don haka na yanke shawarar fita daga makarantar, ina mai yakinin cewa lallai komai zai daidaita a karshe.  Wannan shawara da na dauka mai matukar hadari ce a lokacin, amma ta la’akari da abin da ya biyo baya, a halin yanzu ina iya cewa ita ce shawara mafi muhimmanci da na taba yankewa a rayuwata.  Da na yanke shawarar barin Jami’ar, sai na daina halartar dukkan darussa, sai wadanda nake da sha’awa a kai kadai.

- Adv -

Lamarin dai ba yadda aka so ba.  Domin ko dakin kwana ba ni da shi a Jami’ar; a kasa nake kwanciya a dakin abokai.  Sannan sai na je aike nake samun dan taro da kwabon da zan sayi abin da zan sa a bakin salati.  Kuma sai na yi tafiyar tazarar mil 7 a duk ranar lahadi nake samun abinci mai dadi a Hare Karishna.  Na ji dadin hakan.  Domin galibin abubuwan da na koya sanadiyyar kwazo da neman sani, a karshe sun fa’idantar da rayuwata baki daya.  Bari in baku wani misali:

A lokacin nan, Jami’ar Reeds ce kadai ke da kwararrun malamai masu karantar da darasi kan Fasahar Zane (Calligraphy) a duk fadin kasar nan (Amurka).  Duk wani hoto mai kayatarwa, duk wani taswira da zane da ka gani a manne a jikin kujerun dalibai ko a jikin gine-ginen Jami’ar, to, da hannu aka zana shi.  To, ganin cewa na yi niyyar barin Jami’ar gaba daya, kuma ba dole bane in halarci dukkan darussa, sai kawai na yanke shawarar lazimtar darasin koyon ilmin Fasahar Zane (Calligraphy) kadai, don samun kwarewa a wannan fanni.  Na koyi yadda ake zana haruffan Sans Seriff – daya daga cikin haruffan rubutu a kwamfuta – da dukkan nau’ukansa, da nau’ukan tazarar da ake so tsakanin hadakar haruffa a zane, da kuma dukkan hikimar da ake bukata wajen tsara rubutu ya kayatar.  Wannan abu yana da ban sha’awa ainun; cike da tarihi, da fasaha mai kyatarwa, irin kayatarwar da kimiyyar zamani ba ta iya bayarwa. Hatta ni kaina abin ya birge ni sosai.

Duk da wannan kwarewa da na samu, ban taba tunanin watarana zan kwatanta abin da na koya a aikace ba.  Amma shekaru goma da suka gabata, sadda muke tsara sabuwar kwamfutarmu ta farko nau’in Macintosh, sai wannan ilmin Fasahar Zane (Calligraphy) da na koya a Jami’ar Reeds ya halarto ni.  Kuma nan take muka yi amfani da wannan ilmin Fasahar Zanen haruffa muka shigar da haruffa masu kayatarwa cikin Mac.  Don haka, ita ce kwamfutar farko da ta zo da haruffa masu kayatarwa.  To, da a ce ban lazimci darussan koyon wannan fasahar ba a Jami’a, da wannan sabuwar kwamfuta ta Mac bata samu wadannan haruffa masu kayatarwa tare da tsarin tazara tsakanin haruffa ba, ko kadan.

Kuma musamman ganin cewa manhajar Windows ta kwaikwayi Mac ne wajen tsarin haruffa, kenan da ba don samuwarsu a cikin Mac ba, da babu wata kwamfuta a duniya da za ta mallake su.  Da a ce ban yanke shawarar barin Jami’a ba a lokacin, da ba zan taba tunanin barin sauran darussa ba balle har in lazimci darasin koyon Fasahar Zanen nan kadai.  Kuma da abin da wannan ke nufi shi ne: kwamfutoci ba za su samu wadannan haruffa masu kayatarwa ba kamar yadda suke da su a yau.  Tabbas, sadda nake Jami’a nake ta wannan bundun-dundun, ban taba zaton hakan zai iya faruwa nan gaba ba, ko kadan.  Amma a halin yanzu a bayyane yake, duk sadda na kalli rayuwata shekarun goma baya.

Har wa yau, ya kamata ku san cewa ba za ku taba iya fahimtar ci gaban rayuwarku ba idan kuna kallon me za ku yi nan gaba.  Za ku fahimci hakan ne kawai idan kuka kalli rayuwar da kuka yi a baya.  Don haka, dole ne ku tabbatar wa zuciyarku cewa nan gaba rayuwa za ta yi kyau.  Ya kamata ku zama masu yakini kan wani abu – kwazonku ne, ko kaddara, ko rayuwa, kai ko ma mene ne.  Wannan tsarin tafiyar da rayuwa da na dauka bai taba kai ni ya baro ba, kuma shi ne abin da yayi tasiri mafi girma a rayuwata.

Labarina na biyu kan soyayya ne da rashi.

Na ci sa’a – don na koyi abin da na fi sha’awar yi tun da kuruciyata. Ni da Woz mun kafa kamfanin Apple ne a garejin gidanmu, lokacin ina dan shekaru 20 a duniya.  Mun yi aiki tukuru ta yadda bayan shekaru 10, kamfanin Apple da ya faro da mutum biyu kacal a gareji, sai ga shi ya kasaita zuwa kamfanin da kimarsa ta kai dalar Amurka biliyan biyu ($2billion), da ma’aikata sama da mutum 4000!  Daidai wannan lokaci muka fitar da hajarmu ta farko mai kayatarwa, wato kwamfutar Macintosh, kuma daidai lokacin ne har wa wa yau na cika shekaru 30 a duniya.  Ana cikin haka sai aka kore ni daga kamfanin! Babban magana! Ta yaya za a yi a kore ka daga kamfanin da kai ka kafa shi?  Wato abin da ya faru shi ne, lokacin da kamfanin Apple ya fara habaka, sai muka yi hayan wani bawan Allah da nake da yakinin yana da kwarewar da zai iya taimaka mini wajen tafiyar da kamfanin.  Shekara daya bayan zuwansa komai ya tafi daidai.  Amma daga lokacin da mahangarmu kan tafiyar da kamfanin ta fara shan bamban da juna, sai sabani ya shigo.  Da haka ta faru, sai manyan daraktocin kamfanin suka goyi bayan ra’ayoyinsa.  Don haka ina cika shekaru 30 na fice daga kamfanin.  Kuma ficewa ce wacce ta yadu ko ina.  Nan take na rasa duk alkiblar rayuwar kuruciyata baki daya.  Wannan abu ya dagula mini lissafi matuka.

Har aka samu wasu watanni ban san me ya kamata in fuskanta ba.  Sai naji na fara zargin kaina kan rashin karfin halin rike nauyin shugabancin da aka dora mini, wanda kuma sa’o’ina suka damka a hannu na (sadda nake kamfanin Apple).  Nan take na hadu da David Packard da Bob Noyce, inda na yi kokarin basu hakuri kan wannan abin da nayi (na barin kamfanin Apple).  Na gaza matuka, inda har a karshe na yi tunanin barin kasar ma baki daya. To amma sai wani tunani ya fara shigo mini – ai har yanzu ina sha’awar abin da nayi (a baya).  Abin da ya faru a kamfanin Apple (na korar da aka mini) bai canza son da nake wa sana’ata ba.  Tabbas an kore ni, amma har yanzu ina sha’awar sana’ata.  Don haka na sake gwada wani kokarin.

Duk da cewa ban ji dadin abin da aka mini ba, amma daga baya na gano cewa, korar da aka mini daga kamfanin Apple alheri ne ga rayuwata.  Domin dawainiyar da ke kaina a wancan lokaci na shugabanci, yanzu ya sauka.  Na kuma samu sauki, inda na faro komai daga farko – cikin rashin tabbacin zan dace ko bazan dace ba.  Wannan ne ya bani damar shiga wata sabuwar marhala a rayuwata da ke cike da kwazo da hikimar kirkire-kirkire; babu nauyin kowa a kaina.”

Za mu ci gaba mako mai zuwa

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.