Mahimman Fasahohin da Suka Sauya Duniya Cikin Shekaru 175 Da Suka Gabata (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 28 ga watan Janairu, 2022.

216

Cikin makonni biyu da suka gabata mun yi sharhi kan makalolin da masu karatu suka kwankwada a wannan shafi mai albarka.  Wannan shi ne zama na 9 da muka yi tun fara rubutu a wannan shafi. Na sanar da cewa bayan wancan sharhi, darasinmu na gaba zai mana sharhi ne na musamman kan mahimman ci gaban da aka samu a fannin kimiyya da fasahar sadarwa da kere-kere a shekarar 2021.  Sai dai kafin nan, daga yau zuwa mako mai zuwa, za mu dubi manyan fasahohin da suka yi tasiri ne wajen canza tsari da gudanuwar rayuwa a duniya, a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani, tun daga shekarar 1876 da aka fara kirkirar wayar tangaraho, zuwa wannan zamani da muke ciki.  Bayan nan sai mu dubi mahimman ci gaban da aka samu a wannan fanni a shekarar 2021 da ta gabata.

Daga Shekarar 1876 Zuwa Shekarar 2021

Tsakanin wadannan shekaru ne aka samu kirkire-kirkiren da suka sauya tsari da gudanuwar duniya zuwa yanayin da take a yau.  Za mu dubi guda 10 daga cikinsu.  Bayan wannan sharhi, mai karatu zai fahimci lallai bunkasa da ci gaban duniya a fannin kimiyya da fasahar sadarwa ba abu bane na dare daya.  Ga 10 daga cikin wadannan manyan fasahohi da suka yi tasiri wajen sauya duniyarmu a yau:

Fasahar Tangaraho

Wannan fasaha ta samo asali ne a shekarar 1876, kuma wanda ya kirkirota shi ne shahararren masanin kimiyyar nan mai suna: Alexander Graham.  Ya samar da wannan fasaha ne sadda duniyar Turai ke dogaro da fasahar Telegiram (Telegram).  Tun sannan ake ta inganta wannan fasaha ta tangaraho, har zuwa lokacin da tsarin bincike a fannin ya fara sauyawa, bayan game kasashen duniya da wannan na’ura ta wayar tarho.  Duk da cewa fasahar wayar salula na kan maye gurbin fasahar tarho, a tabbace yake cewa wannan fasahar ce asalin ci gaba a fannin sadarwa na zamani.

Fasahar Lantarki

- Adv -

A shekarar 1879, bayan kirkira da gwajin fasahar kwan lantarki, Thomas Edison ya nemi hukumar sadarwar kasar Amurka ta masa rajistar wannan fasaha don tabbatar da hakkin mallaka gare shi.  Bayan samun rajista, a shekarar 1880 aka fara amfani da kwan lantarki, wanda ke samuwa ta hanyar dumin makamashin lantarki.  Wannan shi ake kira: “Incandescent Light”.  Daga nan kamfanonin samar da wutar lantarki suka ci gaba da samar da nau’uka daban-daban na wannan fasaha.  Ya zuwa karshen 2021, an kiyasta cewa akwai wutar lantarki na kan titi (Street lights) sama da miliyan 304 a duniya.  Sannan a kasar Amurka kadai ana da kwan lantarki masu rai guda biliyan 5.  A duk shekara ana sayar da kwan lantarki na zamani guda biliyan biyu da rabi.  A halin yanzu kusan kowace kasa da biranen duniya, wutar lantarki ya game ko ina.

Fasahar Talabijin

An samar da wannan na’ura ne a shekarar 1927.  A lokacin fasahar Talabijin na dauke ne da launin fari da baki (Monochrome).  Daga baya ne kamfanoni suka ci gaba da inganta wannan nau’in fasaha. A shekarar 1997 kamfanin Fujitsu ya samar da talabijin nau’in Plasma, wacce ta sha bamban wajen siffa da kama da kuma inganci.  A halin yanzu an samar da nau’ukan LCD da kuma OLED, wadanda duk masu shafaffen fuska ne kuma masu dauke da nau’in sinadaran da suka sha bamban da na baya.  An kiyasta cewa akwai talabijin a kashi 89% na gidajen dake duniya.  Sannan kashi 67% na mutanen duniya na kallon talabijin, duk da cewa alkaluman bayanai sun nuna cewa kerawa da sayar da akwatin talabijn ya fara raguwa sosai a duniya.  Kasashen da suka fi kowace kasa yawan tashoshin talabijin a duniya su ne: kasar Rasha, da kasar Sin, da kuma nahiyar Turai.  Fasahar talabijin ta taimaka matuka wajen bunkasa fannin sadarwa a duniya.

Fasahar Kwamfuta

Nau’in kwamfuta, a bisa kiyasin zamanin yau, ya samo asali ne a shekarar 1977, sadda kamfanin Apple ya kera kwamfutarsa ta farko nau’in Apple II, mai dauke da manhajar lissafi na farko mai suna: “VicsCalc”.   Cikin shekarar 1982 sai ga kamfanin IBM da sabuwar kwamfuta mai suna IBM PC.  Daga nan sai kamfanonin kera kwamfuta suka yawaita, inda aka ci gaba da inganta fasahar har zuwa wannan lokaci da muke ciki.  A shekarar 2020 an sayar da kwamfutoci sama da miliyan 275.  A yayin aka samu kari kan haka a shekarar 2021, inda aka sayar da kwamfutoci sama da miliyan 277, musamman nau’in laptop.  An kuma kiyasta ce akwai kwamfutoci sama da biliyan 2 a duniya a yau, wadanda ake amfani dasu.  Kamfanonin da suka yi fice wajen kerawa da sayar da kwamfuta su ne: Lenovo, da HP da kuma kamfanin Dell.  Bayan wayar tangaraho, ba a samu fasahar da ta sauya alkiblar rayuwa wajen sadarwa da yaduwar ilimi irin fasahar kwamfuta ba.

Fasahar GPS

Wannan fasaha ta samo asali ne a shekarar 1973, kuma ta fara game duniya ne daga shekarar 1995, lokacin da kasashen Yammacin duniya suka rungumeta don sauya alkiblar rayuwa.  Kalmar GPS na nufin “Global Positioning System” ne, a warware.  Fasaha ce dake tattaro bayanai ta hanyar tauraron dan adam da aka cilla cikin sararin samaniya, don ganowa da kuma tantance bigiren abubuwa dake wannan duniya.  Kasar Amurka ce ta samar da wannan fasaha, kuma hukumar sojin saman kasar ne ke kula da kuma habaka fasahar, don cin gajiyarta.  Ta amfani da wannan fasaha ne aka gina manhajojin gano bigire a wayoyin salula, wato: “Geolocation Apps”, da kuma manhajar taswirar duniya, wato: “Map Apps”.  Bayan haka, zuwa karshen shekarar 2021 akwai tauraron dan adam guda 77 da wannan fasaha ta GPS ke amfani dasu wajen karban bayanai da sarrafa su.  Kuma a duk shekara an kiyasta cewa gwamnatin Amurka kan kashe dala miliyan 750 wajen kulawa da wannan fasaha da taurarin adam dake cilla mata bayanai.  Bayan GPS, akwai fasahar gano bigire mai suna GLONASS, wanda nahiyar Turai (European Union) ta samar kuma take lura dashi.  Samuwar wannan fasaha da sauran ‘yan uwanta, ya taimaka matuka wajen bunkasa tsarin sadarwa a duniya sosai.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.