Facebook Gidan Rudu: ‘Yan Jaridun Bogi

Na fara rubuta wadannan makaloli ne a shafina na Facebook, a shekarar 2015.

238

‘Yan Jaridun Bogi

Daga cikin abin da ke ci mini tuwo a kwarya har ya shanye mini miya dangane da yaduwa da bunkasar dandalin sada zumunta, akwai yaduwar wata sabuwar kasuwar ‘yan jaridu, amma na bogi.  Kasancewar fasahar Intanet na da wani gamammen tsari ne wanda kowane lokaci ka hau, za ka samu masu sauraronka, shi yasa wannan lamari yayi kamari sosai.  Abin da nake nufi shi ne, a yanzu an samu wadanda ke amfani da Intanet wajen yada labaru da sunan wai su ma a matsayin “yan jarida” suke.

Da farko dai tukun, masu wannan aiki za ka samu ba su da wani ofishi nasu na kansu inda idan kaje za ka same su.  Sannan ba su da tsarin tace bayanai, ko labarun da suka samo (ko suka ci karo dasu a Intanet).  A takaice dai ba su da abin da ake kira “Editorial Board,” wanda aikinsu ne tace duk wani labari da wani jami’insu ya kawo, kafin a watsa shi.  Abin da zai baiwa mai karatu mamaki ma shi ne, mutum daya ne ko wasu gungun “gayu” ne ke farautar labaru su yada; ba tsari, ba kintsi, ba ka’ida.

Abu na biyu, za ka samu ba su da ginannen shafin gidan yanar sadarwa (Website) inda ta nan ne za ka iya sanin waye su.  Abu na uku, ba su da wani kamfanin yada labaru mai rajista da hukuma.  Abu na hudu, shafin da suke amfani dashi wajen aiwatar da aikin duk bai wuce shafin Facebook, ko Twitter ko wasu makamantansu.

Abu na biyar, wanda shi ne yafi hadari, za ka samu masu wannan aiki da sunan aikin jarida, galibinsu a Dandalin Sada Zumunta (Social Media) suke kalar labaru, wallahi.  Da zarar wani ya ce anyi kaza a unguwarsu, sai suyi wuf su cafke labarin, su yada.  Idan ya sanya hoto ma nan take za su dauki hoton, duk su yada.  A wasu lokuta ma ba su jira sai abu ya faru, da zarar sunji jita-jita, sai kawai su yada a Facebook, musamman.  Su ambaci sunan gari da unguwa, har da wasu sunaye na wasu mutane da suka ji a jita-jitar.  Akwai wanda ya yada wani labari na bogi, bai faru ba, yace abin ya faru.  Ya ambaci sunan gari da unguwa, abin mamaki, sai wani dan unguwar ya aika masa sako ta Inbox cewa shi fa a unguwar yake, amma ba abin da ya faru. Sai “dan jaridan” yace zai kara bincikawa.  Can ya sake tuntubarsa, yaya?  Sai yayi wuf yana ba da hakuri, wai kuskure aka samu.

- Adv -

Darasi:

  1. Ba duk labarin da ka gani an yada da sunan wani kamfani mai kama da na aikin jarida ko kafar yada labaru za ka dauka a matsayin gaskiya ba, musamman idan ba kamfanin yada labaru bane sananne;
  2. A kul ka kuskura ka rika yada (ta hanyar “sharing”) labaru daga ire-iren wadannan kafafe, ba tare da neman tabbaci ba. In kayi haka, za ka zama cikin masu yada karya, in har abin da suka yada karya ne;
  3. A karshe, haramun ne mutum ya siffatu da siffar da bai cancanceta ba, don neman suna ko don neman duniya. Idan babu wanda ya gane, Allah ya sani, kuma duk abin da mutum ya mallaka ta wannan hanya zai zama ya ci haramun ne, kuma sai Allah ya titsiye shi ya biya a ranar kiyama.

Allah kiyashe mu tabewa, amin.

BABAN SADIK

15.09.2016 – 9:07AM

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.