Tsokaci Kan Sabuwar Dokar Ta’ammali Da Kafafen Sadarwa na Zamani a Najeriya (1)

Manyan al’amuran da wannan doka ta shagaltu dasu dai guda biyu ne: na farko shi ne ayyukan dukkan kafafen sadarwa na zamani dake Intanet, wadanda ‘yan Najeriya ke amfani dasu; suna da rajista ne, ko babu rajista.  Wadannan kafafe kuwa, kamar yadda na ayyana a baya, su ne kafafen sada zumunta, irin su Facebook, da Twitter, da Google (Youtube), da WhatsApp (Facebook/Meta), da kuma dukkan jami’ai ko wakilansu a Najeriya.  Sai abu na biyu, wato tabbatar da hanyoyin kariya ga ‘yan Najeriya da ma baki, a kafafen sadarwa na zamani. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 1 ga watan Yuli, 2022.

267

Wata Sabuwar Doka Dake Tafe

Ranar Talata, 14 ga watan Yuni ne sashen Hausa na BBC dake Abuja ya tuntubeni don tattaunawa dani, kamar yadda suka saba, kan wata sabuwar doka da za ta kayyade tsarin ma’amala da kafafen sadarwa na zamani a Najeriya.  Hukumar da ke da alhakin samar da wannan sabuwar doka, wadda a halin yanzu ake mata kwaskwarima, ita ce Hukumar Bunkasa Fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwa na Zamani, wato: “National Information Technology Development Agency” ko “NITDA” a gajarce.

Duk da cewa har yanzu wannan kundi bai zama doka ba, amma akwai tabbacin nan kusa za a fitar dashi.  Domin tuni hukumar NITDA ta dora dokar a shafinta dake Intanet dake: https://nitda.gov.ng/draft-regulatory-instruments/.  Taken wannan doka dai shi ne: “Code of Practice for Interactive Computer Service Platforms/ Internet Intermediaries.”  Wannan yasa tuni kafafen yada labarum gida da na kasashen waje suka fara sharhi kan wannan doka dake tafe, tare da duba abubuwan da aka tanada a ciki, don ganin dacewa ko rashin dacewarsu da yanayin da ake ciki.  Wannan yasa daga wannan mako zuwa makonni biyu dake tafe in Allah Yaso, wannan shafi namu mai albarka zai tattauna kan wannan sabuwar doka.  A farko zamu dubi mahimman abubuwan dake cikin dokar ne.  na biyu kuma mu yi sharhi tare da ba da shawara ga hukuma inda akwai bukatar hakan.  A karshe kuma mu kawo misalan ire-iren wadannan dokoki da wasu kasashe suka samar, don kokarin tabbatar da maslaha ga al’ummarsu.

Bangarorin Dokar

Wannan doka ta kunshi mahimman bangarori ne guda shida, bayan gabatarwa da fassaran ma’anar kalmomin da suka shafi dokar.  Ga takaitattun bayanai kan wadannan bangori nan:

Manufa

- Adv -

Wannan doka ta kayyade tsarin ma’amala da kafafen sadarwa na zamani dai an samar da ita ne don cinma manufofi guda uku.  Na farko shi ne don samar da tsaftatacciyar ma’amala tsakanin kafafen sadarwa na zamani – irin su Facebook, da Twitter, da Youtube, da Instagram, da WhatsApp da sauransu – da ‘yan Najeriya dake da rajista a wadannan kafafe.  Manufa ta biyu, ita ce don tabbatar da hanyoyin kariya ga jama’a (‘Yan Najeriya) a wadannan kafafen sada zumunta na zamani.  Na uku kuma, don hadin gwiwa tsakanin hukumar NITDA a madadin gwamnatin tarayya, da dukkan masu ruwa da tsaki a fannin sadarwa na zamani a Najeriya, wajen tabbatar da doka da oda.

Wadannan manufofi suna kokarin cin ma kudurin sashe na 6(a) ne, dake babbar dokar da ta kafa hukumar NITDA na shekarar 2007.

Hurumi

Manyan al’amuran da wannan doka ta shagaltu dasu dai guda biyu ne: na farko shi ne ayyukan dukkan kafafen sadarwa na zamani dake Intanet, wadanda ‘yan Najeriya ke amfani dasu; suna da rajista ne, ko babu rajista.  Wadannan kafafe kuwa, kamar yadda na ayyana a baya, su ne kafafen sada zumunta, irin su Facebook, da Twitter, da Google (Youtube), da WhatsApp (Facebook/Meta), da kuma dukkan jami’ai ko wakilansu a Najeriya.  Sai abu na biyu, wato tabbatar da hanyoyin kariya ga ‘yan Najeriya da ma baki, a kafafen sadarwa na zamani.

Kafafen Sadarwa na Zamani a Najeriya

Wannan bangare ya shafi dokoki ne gamammu ga dukkan wani kamfani dake bayar da damar sadarwa ta hanyar Intanet, wanda ‘yan Najeriya ke hawa su kirkira, ko aika, ko karanta bayanai tsakaninsu. Wannan ya shafi kananan kamfanoni.  Wajibi ne suyi biyayya ga wannan doka wajen baiwa ‘yan Najeriya damar ma’amala ta sadarwa a kafafensu.  Sannan dole subi umarnin kotu a duk sadda wata hukuma ta bukaci bayanai daga gare su, kan wani bincike da take yi na miyagun laifuka dangane da wani cikin masu rajista a shafinsu.  Haka dole ne su bi umarnin kotu kan bayar da bayanai dangane da wani sako da wani ko wasu suka wallafa a shafinsu. Ko korafi daga wani dan Najeriya ko wata hukumar gwamnati don bincike da cire wani sako da wani ya wallafa.  Ko bayyana hakikanin wanda ya kirkiri wani sako ko yada shi a halin zamansa a Najeriya.  Ko   Bin diddigi don tabbatar da wani bai dora wasu bayanai da suka saba dokar kasa ba, daga cikin masu rajista dasu a shafinsu.  Sannan kuma dole ne su samar da hanyoyin aika korafi ga ‘yan Najeriya don tantance bayanan da masu rajista da su ke wallafawa.

Wadannan gamammun dokokin dake ken dukkan kamfanonin kafafen sadarwa na zamani kenan.  A daya bangaren kuma, akwai wasu kebantattun dokoki da suka shafi wasu kafafe na musamman, bayaninsu na tafe a makon gobe.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.