Tsokaci Kan Sabuwar Dokar Ta’ammali da Kafafen Sadarwa na Zamani a Najeriya (3)

Hana Yaduwar Labaran Bogi a Kafafen Sadarwa

Wannan bangare ya dora wa kamfanonin sadarwa ne wasu hakkoki, don rage yaduwa da bunkasar labarun karya da na bogi ta amfani da kafafen sadarwa da ‘yan kasa ke amfani dasu.  Mahimman dokokin dake karkashin wannan bangare dai guda shida ne. – Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 15 ga watan Yuli, 2022.

317

Matashiya

A makon jiya bayanai sun gabata kan sauran bangarorin da wannan sabuwar doka ta Kayyade Tsarin Ma’amala da Kafafen Sadarwa na Zamani ta kunsa ne, don Karin wayar da kai. Kamar yadda na fada a farkon jerin wadannan makaloli, manufar ita ce don tabbatar da mun fahimci abin da wannan doka ta kunsa, sannan sharhi da tsokaci zai biyo baya, tare da wasu shawarwari ga hukuma.  Amma kafin nan, a yau za mu Karkare bayaninmu ne da bangaren karshe na wannan doka, wanda shi ne bangare na bakwai.  Kafin sharhi da tsokaci.

Hana Yaduwar Labaran Bogi a Kafafen Sadarwa

Wannan bangare ya dora wa kamfanonin sadarwa ne wasu hakkoki, don rage yaduwa da bunkasar labarun karya da na bogi ta amfani da kafafen sadarwa da ‘yan kasa ke amfani dasu.  Mahimman dokokin dake karkashin wannan bangare dai guda shida ne.

Na farko, shi ne dole dukkan kamfanonin sadarwa da ‘yan Najeriya ke amfani da shafukansu wajen sadarwa, su yi kokarin sanin al’adun kasar nan, da kuma dukkan hanyoyin yaduwar karerayi ta kafafen sadarwa a kasar baki daya.  Na biyu, dole ne kowane kamfani ya rika gudanar da bincike ta hadin gwiwa da masana ‘yan Najeriya – malaman jami’a, da ‘yan jaridu, da masana harkar sadarwa na zamani –  kan abin da ya shafi hanyoyin yaduwar karerayi da duk wasu bayanai da ka iya haddasa tashin-tashina a kasar.  Na uku, dole wadannan kamfanoni su rika wayar da kan jama’a a kasar nan, kan hanyoyin yaduwar karerayi da labaran bogi.  Na hudu, dole ne wadannan kamfanoni masu kafafen sadarwa na zamani su yi hayar kwararru da za su rika tantance bayanan gaskiya daga na karya da ‘yan Najeriya ke dorawa a kafafensu.  Wadannan kwararru su ake kira: “Certified Fact Checkers”.

- Adv -

Aikin wadannan kwararru shi ne, duk wani labari da ka dora a kafar, za su dubi bayanan, su tantance su ta hanyar bincike mai zurfi.   Idan tuhuma ne, ko bayanai masu alaka da faruwar wasu abubuwa a baya a tarihance, ko suna da alaka da adadi na wasu abubuwa da hukuma ko wani dan siyasa ta/suka gudanar a baya.  Idan ya tabbata labarin karya ne, ko tuhumar bata tabbata ba, ko kuma Kazafi ne don cutar da wani ko mutuncinsa, ko zance ne da aka kintsa shi don Siyaya – don cusa tsanar wani ko wata ‘yar siyasa a zuciyar jama’a – to, nan take za a sauke sakon (rubutu ne ko hoto, ko bidiyo).   Manufar ita ce, don kauce wa  yada karya ko Kazafi cikin jahilci, ko shashantar da al’umma ta amfani da zantuka marasa tushe.

Doka ta biyar, dole ne wadannan kafafen sadarwa su rika kimantawa da bai wa sakonnin gaskiya mahimmanci wajen tsara labarai a shafukan jama’a.  Abin da hakan ke nufi shi ne, yin hakan ne kadai za a rage yaduwar sakonnin bogi da na karya a tsakanin ‘yan Najeriya dake ta’ammali da wadannan kafafe ko shafuka.  Sai doka ta shida kuma ta  karshe karkashin wannan bangare, shi ne, dole wadannan kafafe su samar da hanyar ganowa da hukuntawa da kuma rufe shafukan masu yayata sakonnin bogi a kafafensu.  Wadannan su ne mahimman bangarorin da wannan sabuwar doka mai take: “Dokar Kayyade Ma’amala da Kafafen Sadarwa na Zamani a Najeriya.

Hukumar NITDA dai bata ce komai kan yaushe za a rattafa hannu kan wannan sabuwar doka ba, balle ta fara aiki.  Duk da haka, masana na ganin wannan yunkuri na gwamnati wajen kayyade ayyukan kafafen sadarwa na zamani a Najeriya dai, ba ya rasa alaka da zanga-zangar da wasu matasa suka gudanar kan hukumar SARS ‘yan shekarun da suka gabata, inda suka ta amfani da kafar sadarwa musamman na Twitter wajen gudanar da gangami kan hakan, hukumar Najeriya ta fara sa ido kan tasirin wadannan kafafe na sadarwa a kasar nan.  Ana haka kuma sai takaddama ta barke tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin Twitter, bayan biyo bayan rufe shafin Shugaban Kasa Buhari da tayi.  Hakan ya haddasa rufe shafin Twitter a Najeriya na tsawon watanni.  Wannan ma na cikin manyan dalilai.

Dalili na biyu, wasu masana na ganin Karin yaduwa da yawaitar ‘yan Najeriya a wadannan kafafe, lokaci ya yi da za a samar da doka don kawo tsari dangane da yaduwar bayanai a tsakanin ‘yan Najeriya dake wadannan kafafe, da sauran kasashen duniya.  Dalili na uku, cikin mahimman dalilai, shi ne halin rashin tsaro da kasar nan ta samu kanta a ciki na tsawon shekaru.  Akwai bayanai dake nuna cewa, galibin masu aikata manyan laifuna na gama kintsawa da hada wayoyinsu ne ta wadannan kafafe, wadanda kuma gwamnati ba ta da ta cewa cikin al’amuransu.  A tare da cewa hukuma bata bayyana ba, amma wadannan na cikin manyan dalilan da suka zaburar da ita wajen samar da wannan doka.  Amma a daya bangaren kuma, galibin ‘yan jaridu da kungiyoyin rajin kare hakkin dan adam dake Najeriya na ganin, duk da wadancan ilialai masu karfi, amma dokokin sunyi tsauri.  Kuma suna tsoron kada ya zama ana son amfani dasu ne kan abokan hamayyar siyasa, musamman ganin an shiga kakar manyan zabuka na kasa.

Ko ma dai mene ne, zuwa mako mai zuwa in Allah Yaso, sharhi da tsokaci zai biyo bayan wadannan bayanai da suka gabata.  Allah hada fuskokinmu da alheri, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.