An Samar da Manhajar “BBM” Ga Wayoyi Nau’in Android

A baya babu wayar salular dake dauke da manhajar BBM sai wayar salula nau’in BlackBerry. Amma a halin yanzu bayanai na tabbatar da samuwar wannan nau’in manhaja ga masu amfani da wayoyin salula na Android. A sha karatu lafiya.

360

Ga dukkan masu amfani da wayoyin salula masu dauke da Manhajar Android (na kamfanonin Samsung, da LG, da Tecno, da SonyEricsson, da HTC) ko manhajar iOS na wayoyin salular kamfanin Apple, a yanzu an kaddamar da masarrafar hirar ga-ni-ga-ka na wayoyin Blackberry don amfanin masu wadannan nau’ukan wayoyin salula.  A safiyar talata, 22 ga watan Oktoba ne wannan manhaja ta bayyana, kuma kafin yammacin wannan yini, a kalla mutane miliyan 10 sun saukar da ita.  Tun watan jiya ake ta rade-radin wannan hadin gwiwa da kamfanin Research in Motion a daya bangare, da Google da Apple a dayan bangaren don ganin an samar da wannan manhaja ta BBM a wayoyi masu dauke da Android da iOS na kamfanin Apple.

Wannan ya faru ne sanadiyyar kasa a gwiwa da kamfanin Research in Motion da ke kera wayoyin Blackberry yayi a kasuwa, da ganin cewa idan ba haka yayi ba, to a karshe kusan kowa na iya janyewa daga kasuwarsa. Wannan dabara ce irin ta kasuwanci, ta yadda kusan galibin masu amfani da wayar salula za su ci gaba da yi da wayoyin Blackberry, cikin dabara.  Hakarsa kuma tana kan cinma ruwa a wannan lokaci.

- Adv -

A duniyar waya dai gaba daya, wayoyin salula nau’in Blackberry ne kadai ke dauke da wannan masarrafa ta BBM kuma ita ce tafi tasiri a rayuwar jama’a a duniya gaba daya, saboda gamewar mu’amala da kuma yawaitar masu amfani da wayar a yau.

Kafin wannan lokaci kamfanin Research in Motion ya bayar da dama ga masu son su zama a sahun farko wajen samun wannan manhaja daidai lokacin da aka kaddamar da samuwarta a karon farko.  Shafin Kimiyya da Kere-kere na cikin wadanda suka bayar da adireshin Imel dinsu don haka. Wannan yasa a safiyar talata kamfanin Research In Motion ya aiko min da sako mai dauke da sanarwar kaddamar da wannan masarrafa ta BBM, kasancewar ina cikin ‘yan kadan da suka yi rajista da kamfanin don neman alfarmar fara amfani da manhajar a karon farko. A halin yanzu wadanda aka musu alfarma ne kadai ke da wannan dama, sai nan gaba a hankali za a saki manhajar gaba daya. Duk da haka wannan bai hana aje shafin manhajar da ke www.bbm.com don shigar da adireshin Imel, da zarar ta zama gama-gari, za a samu sanarwa da zai nuna hakan, don samu.

Duk mai wayar salular da ke dauke da manhajar Android (version 4.0 zuwa sama) yana iya bincika cibiyar masarrafai wato: Market Place ko Google Play, ko ya ke kaje www.bbm.com, idan an saki manhajar gaba daya, don saukar da ita. Idan kana da wannan manhaja, kana iya hira da duk wanda kake da lambarsa a wayarka muddin yana da Blackberry ko wata waya mai dauke da Android, kyauta, ko da babu ko sisi a wayarka, muddin da Intanet.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.