Tsarin Samuwa da Maimaituwar Ruwa a Duniya

A kashi na biyu bincikenmu ya ta’allaka ne kan yadda ruwa ke samuwa da yadda yake maimaituwa. Wannan shi ake kira: “The Water Cycle” a kimiyyar zamanin yau. A sha karatu lafiya.

367

Samuwa da Maimaituwar Ruwa a Duniya

Duk wanda ka tambaye shi daga ina ruwa ke samuwa, amsar farko da zai fara baka ita ce: “Daga sama ne.”  Wannan amsa, duk da cewa haka take, amma ba iyakanta ba kenan.  A takaice ma dai, ruwan sama wani yanki ne ko daya ne cikin hanyoyin da ruwa ke samuwa.  Kai ba ma wannan ba, abin da mai karatu zai yi mamakin ji shi ne, ruwan sama wata hanya ce ko wani tsari ne na maimaituwar samuwan ruwa a wannan duniya da muke rayuwa a cikinta.  Abin da zai tabbatar mana da wannan bayani kuwa shi ne, idan muka yi nazarin ayoyin Kur’ani da kyau, za mu ga cewa idan ana maganar asali ne, to ma iya cewa asalin farko na ruwa shi ne tekuna, da koguna da muke da su a duniya.  Bayan Allah ya tsage wannan duniya a halittar farko aka samu sama da kasa, daga baya sai Allah ya kintsa wannan kasa tamu zuwa yanayin da zai dace da zamantakewarmu.  Wannan kintsawa kuwa ya samu ne ta hanyar baje kasar, da sanya ta ta zama mai taushi, mai saukin mu’amala, da kuma samar mana da tekuna, da koguna, da rafuka, sannan kuma aka kintsa sama – ta hanyar samar da giragizai da iska – don tabbatar da tsarin samar da ruwa ko maimaituwarsa a duniya.  Wadannan bayanai, idan mai karatu zai natsu ko ya tambaya, za a samo masa su a cikin Suratun Naazi’aat da ke Kur’ani mai girma.

Idan muka fahimci haka a karon farko, sai tambaya ta biyu ta biyo baya: shin, ruwa da muke samu daga sama, wani sabon ruwa ne ful, ko kuwa ruwan da muka sani ne yake maimaituwa?  Idan muka yi la’akari da sakamakon binciken malaman kimiyya, za mu ga cewa lallai ruwan da muke samu daga sama, ruwa ne da yake maimaituwa, a wani sabon yanayi mai cike da nishadi da sabuntawa.  Watakila mai karatu yace: “Shin, da gaske wannan magana haka take cikin Kur’ani?”  Amsar ita ce eh.  Domin a cikin Kur’ani Allah ya sanar da mu ne cewa shi ne yake saukar da ruwa daga sama, don amfaninmu da dabbobinmu da abin da muke shukawa a kasa. Ba wai yanayin ruwan yake sanar da mu ba, sai dai saukarsa, da cewa shi ne mai saukarwa.  Kuma idan ya ga dama sai ya kame ruwan, kamar yadda mun sha ganin hakan.  Kafin mu yi nisa, a nan nake ganin dacewar sanar da masu karatu wata ka’idar ilmi tsakanin binciken kimiyyar zamani, da kuma nassoshin da ke cikin Kur’ani.  Wannan zai taimaka mana matuka wajen fahimtar binciken malaman kimiyya, da kuma fahimtar nassoshin Kur’ani din.

Duk ayoyin da ke bayanin yiwuwa ko samuwa ko faruwan wasu abubuwa a duniya masu alaka ta kai-tsaye da fannin kimiyya, sakon da ayoyin ke kokarin isar mana a takaice shi ne mu san wanda ke haddasa su, ko yake da ikon sanya su faruwa, ko yake da ikon kame su don hana su tasiri.  Wannan tsarin mulki ne na Ubangiji, wanda ya taskance yadda komai ke faruwa karkashin ikonsa, da yadda yake tasarrafin abubuwa cikin mulkinsa.  Bayan wannan, har wa yau Allah ya zayyana yadda komai zai faru, da kuma dalilan da za su sa komai din ya faru. Samuwar wadannan dalilai ne ke sa mai ganin abin a fili ya ga faruwarsu, har a karshe, idan ba mai imani bane shi, ya dauka wadannan dalilan zahirin su ne kadai ke sa wannan abin ya faru.  Wannan tsari na haddasa faruwan abubuwa sanadiyyar dalilai bayyanannu, shi ake kira “Cause and Effect Theory” a kimiyyance.

Mu sani, Kur’ani ba littafin kimiyya bane, duk da cewa akwai bayanai masu alaka da kimiyya sosai a ciki.  Allah ya saukar da shi ne don shiriya, don a bauta masa, ba wai sinadaran rayuwa ba.  Wannan ne ma yasa littafin ya zo a tsarin sura-sura, ba babi-babi ba kamar yadda littattafan kimiyya suke.  Kuma kasancewar fannin kimiyya ba wani fanni bane da kowa zai iya gudanar da bincike har ya gano abin da aka fada a Kur’ani, kuma bincike a fannin kan dauki lokaci mai tsawo, sai wasu ke ganin kamar akwai cin karo tsakanin wannan fanni da abin da Kur’ani ke tabbatarwa.  Ko kadan babu.  Matsalar da ke tsakanin masu gudanar da wannan bincike da Kur’ani, itaa ce na rashin imani ko samuwarsa.  Galibinsu basu yi imani da Allah ba, don haka duk binciken da suke yi, ba su danganta sakamakon abin da suka gano ga Allah madaukakin sarki, sai dai ga dalilai na zahiri da suka haddasa abin.  Wannan kuwa ba karamin hadari bane.

To amma kowane musulmi ya san cewa Allah ne mahallicin komai, kuma shi ne yake sarrafa duniya baki daya.  A matsayinka na makarancin fannin kimiyya ko mai karanta rubuce-rubucen malaman kimiyya, dole ne ka kiyaye wannan ka’ida a kwakwalwarka, don kada ka rudu da dalilan da suke bayarwa kan cewa su ne kadai ke haddasa abin da ke faruwa, ko ke haddasa samuwar wata halitta ko wani yanayi da ke maimaituwa.  Bayan dukkan wannan, yanzu za mu shiga bayani kan yadda samuwar ruwa ke maimaituwa a duniya, abin da malaman kimiyya ke kira Water Cycle, ko Hydrologic Cycle.  Wannan bayani ne zai tabbatar mana cewa lallai ruwan sama da muke samu a duk shekara ko damina, ruwa ne da ke maimaituwa a wani yanayi.

Tsarin Maimaituwar Ruwa a Duniya (Hydrological Cycle)

Kamar yadda bayanai suka gabata a baya, ruwan da ake samu a duniya, daga na cikin teku, da wanda ke cikin kogi, da na rafi, da na karkashin kasa, da ruwan sama da muke samu, da tsaunukan kankara na cikin teku, wato Glacier, da Kankaran da ke saukowa daga sama lokacin ruwan sama, da dusar kankara (Ice Pellets, ko Snow) da ake samu a kasashe masu sanyi irin su Rasha da sauran kasashen Turai, duk abu ne guda daya da ke maimaituwa lokaci-lokaci, cikin wani tsari da Allah ya tanada, mai cike da ban mamaki ko al’ajabi.  Wannan tsari da ke samar da wadannan nau’ukan ruwa a yanayi uku – narkakken ruwa, da kankara, da tururin iska mai dauke da ruwa – shi ake kira Water Cycle ko Hydrological Cycle a kimiyyance.  Wannan tsari yana kunshe da matakai hudu ne muhimmai, masu maimaita shi a duk lokacin da dalilan da ke samar da su suka samu.  Bayan wadannan bayanai ne mai karatu zai fahimci yadda ruwan sama ke samuwa, da dalilin da ke sa tekuna da koguna suke yin ambaliya, da yadda ruwa ke taskance kansa a cikin iska cikin yanayin tururi, sannan ya haura zuwa sararin wannan duniya tamu.

Matakin Farko

- Adv -

Wannan shi ne matakin ma’adana, wato lokacin da ruwa ke taskance ko dai a cikin kogi, ko a cikin teku, ko a cikin rafi; a yanayin narkakken ruwa yake ko a yanayin kankara narkakke, wato Melting Ice, da ke cikin teku, ko daskararre. Sai kuma ruwan da ke cikin karkashin kasa mai bubbuga cikin teku.  Dukkan wannan ruwa yana cikin ma’adana ne, wanda Allah ya samar da shi don amfanin bayi, kuma shi ne matakin farko na samuwan ruwa a duniya, kamar yadda bayanai suka gabata.

An kiyasta cewa akwai ruwa a yanayin gundarin kankara wanda kauri da fadinsa ya kai nisan murabba’in kilomita 17 (17km2) a nahiyar Antaktika (Antarctica), da nahiyar Greeland.  Wadannan su ne wurare masu matukar sanyi a duniya. Malaman kimiyya sun ce ba a samun idaniyar ruwa ko ruwan karkashin kasa a wadannan nahiyoyi, saboda daskarewan ruwan a karkashin kasa.  Shekaru dubu 22 da suka wuce ne aka yi mummunar sanyi a wadannan wurare, inda har kankara ta mamaye ilahirin kasar Kanada, da Arewarin Amurka, da Arewacin Turai, da kuma Saiberiya.  Wannan kankara ta mamaye wuraren da aka kiyaska sun yi fadi da nisan murabba’in kilomita miliyan 20 (20m km2).

Daga cikin ruwan da ke karkashin kasa akwai wadanda suke cikin duwatsu. Wadanda suke cikin duwatsu masu taushi, wato Sedimentary Rocks, wadanda kuma aka kiyasta cewa sun mamaye kusan kashi 20 zuwa 40 na duwatsun da suke cikinsu.  Samuwar ruwa a wadannan ma’adanai – na kogi, da teku, da rafi, da kankara, da karkashin kasa – shi ne matakin farko da ke sawwake samuwar mataki na biyu, don haddasa tsarin maimaituwar ruwa a duniya.

Mataki Na Biyu

A yayin da ruwa ke taskance cikin wadancan ma’adanai na teku ko kogi ko rafi da dai sauransu, a kullun ruwan na raguwa, yana bin iska a yanayin tururi, har ya haura zuwa cikin wata ma’adana da ke cikin sararin wannan duniyar ta mu.  Wannan ma’adana ita ake kira Water Vapour, kamar yadda bayani ya zo a makon baya. Haka ma kankaran da ke narkewa a cikin teku, duk wannan tsari yake bi.  Wannan tsari na bacewar ruwa ta hanyar bin iska a yanayin tururi, shi ake kira Evaporation a turancin kimiyya.  Haka ruwan zai ta taruwa zuwa cikin wancan ma’adana ta sararin duniya.  Bayan wannan tururin iska da ke samuwa daga teku ko kogi, akwai wani tururin da ke fitowa daga ramukan jikin ganyayyaki da ciyayi da kuma kasa mai danshi (ko duk inda aka zubar da ruwa a kasa), yana haurawa zuwa sama shi ma.  Wannan tsari na bacewar ruwa daga jikin ganyayyaki da ciyayi don bin iska a yanayin tururi, shi ake kira Transpiration a turancin kimiyya.  Dukkan wannan tururi na ruwa da ke bin iska zuwa sama, asalin ruwa ne da ke ma’adanar da muke da su a wannan duniya – ko dai teku ko kogi ko kankara ko wanda ke jikin sauran halittu.

Malaman kimiyya suka ce a kullum ana samun adadin ruwa da yawansa ya kai 1,200 a ma’aunin kimar ruwa, wato 1,200 cubit km.  A kullum sai wannan adadi na yawan ruwa a yanayin tururi ya bi iska zuwa ma’adanar ruwa da ke sararin duniyarmu.  Don haka malaman kimiyya suka ce, da a ce za a samu tangarda har wannan adadi ya daina haurawa sama, nan da kwanaki 10 ma’adanar da ke sararin duniyarmu za ta kafe, a rasa ruwa a cikinta. Wannan ke nuna mana a fili karara cewa, Allah ya tanada wa bayinsa dukkan abin da za su dogara da shi na arziki, tare da tsarin samuwarsa. Wannan zance yana nan cikin Suratul Hijri – inda Allah ya ce dukkan wata arziki taskarta na wajensa ne, kuma ba ya saukar ta da ita ga bayinsa sai iya gwargwadon yadda zai zama maslaha a gare su.

Manyan dalilai na fili da ke sawwake wannan tsari na bacewar ruwa cikin iska a yanayin tururi da ke haurawa zuwa ma’adanar sararin duniyarmu kuwa, su ne tsananin zafin rana da haskenta, da iskar da ke bugawa – a tudu ko a saman teku – da inuwar da ke saman shuke-shuke ko ciyayi, da kuma danshin kasa ko duk inda aka zubar da wani ruwa a nan duniya inda muke rayuwa.  Wadannan dalilai ne ke haddasa samuwar wadannan yanayi guda biyu na Evaporation da kuma Transpiration. Kuma wannan mataki ne ke haifar da matakin samuwar ruwa na uku, wato abin da ake kira Precipitation.

Mataki Na Uku

Wannan mataki kuwa shi ne matakin saukar ruwa daga sama, ko Precipitation kamar yadda malaman kimiyya ke ambatonsa.  Kafin mu ci gaba, na san da yawa daga cikinmu mun sha jin cewa, a kimiyyance abin da ke haddasa ruwan sama shi ne tururin teku ko kogi da ke haurawa sama, sannan ya zubo. Sai dai da yawa daga cikinmu muna karyata wannan ka’ida ta kimiyya, amma kuma hakan shi ne abin da yake kusa da daidai.  Babban kuskuren da muke yi kuwa shi ne, muna dauka cewa ruwan da ke zubowa daga sama, yana zuba ne daga asali ko jikin bangon saman da muke gani.  Wannan kuskuren fahimta ne babba.  Domin hatta a cikin Kur’ani mai girma Allah ya ambaci jihohi guda biyu ne wajen zuban ruwan sama.  Kuma dukkan malaman tafsiri sun yarda cewa jihohin nan guda biyu da Allah ya ambata, abu ne guda daya, ko jiha daya ne yake nufi.

Allah ya ambaci cewa shi ne yake saukar da ruwa “daga sama”.  A wasu wuraren kuma ya ambaci cewa, shi ne ya ke saukar da ruwa “daga giragizai.”  Malaman tafsiri suka ce ya ambaci sama ne don nufin alaka da nasaba, dangane da inda dan adam ke zaune.  Amma asali ruwa na zuba ne daga jikin giragizai ba daga can asalin sama ba.  Amma an ambaci sama ne saboda a can giragizai suke; ma’ana a saman dan adam. Bayan nan, da yake zamani ya kawo samuwar jirgin sama, duk wanda ya taba hawa jirgin sama yayi doguwar tafiya, zai ga cewa sai jirgin ya “keta hazo” ko “giragizai” kafin ya daidaita a sama ya ci gaba da tafiya.  Abin da yin hakan ke nufi kuwa shi ne, da za a yi ruwa a duniya – a kowane bangaren duniya ne kuwa – wadanda ke cikin jirgin nan ba za su sani ba sai sun sauka.  Domin ruwan daga jikin girgije yake zuba, shi kuma jirgin ya wuce inda girgijen yake.  Idan mun fahimci wannan tsari, sai mu koma kan bayaninmu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.