Ruwa da Yanayin Samuwarsa

A yau za mu koma fannin kimiyyar sinadarai. Daga wannan mako kasidarmu za ta dubi yadda ruwa yake samuwa ne, da kuma irin sinadaran dake dauke cikinsa.

377

Ruwa Abokin Aiki

Daga cikin sinadarai masu tafiyar da rayuwa baki dayanta, wadanda kuma dan adam bai taba damuwa da sanin hakikanin yadda asali da yanayinsa yake ba, akwai ruwa.  Bahaushe kan masa kirari da cewa: Ruwa abokin aiki.  Ba komai yasa dan adam ke masa wannan kirari ba sai don saukin sha’ani da lamarinsa.  Kana iya mu’amala da shi yadda kake so.  Kana iya dafa shi.  Idan ma ya yi zafi fiye da bukatarka, kana iya sirka shi.  Kana iya sanyaya shi yadda kake so.  Idan ya yi sanyi fiye da bukatarka, kana iya sirka shi har ya salance zuwa yanayin da kake sonshi.  Kana iya hada shi da wasu sinadaran don gudanar da wasu bukatu ko ayyuka.  Kana iya cakuda shi da yashi ko siminti ko kasa don yin gini, ko don bulo, ko don gyara gida.  Kana iya hada shi da sinadaran kimiyya masu fitar da dauda don tsaftace tufafi da muhallinka.  Kana iya wanke motarka da shi.  Kana iya sha ka rayu.  Kana iya dafa abincinka, ko hada tsimi don sha.  Kana iya wanka da  shi. Kana iya yin duk wani abin da ke bukatar wankewa, ko jikawa, ko makamantansu.  Kai a takaice ma dai, duk wanda ya mutu, to da ruwa ake wanke shi, kafin a kwantar da shi cikin makwancinsa.  Ruwa abokin aiki.  Lallai wannan kirari ya dace da wanda aka yi kirarin dominsa.

Masu karatu, a yau ga mu dauke da kasida ta musamman kan ruwa, da yadda yake samuwa, da irin yanayinsa, da kuma sinadaran da ke dauke a cikinsa.  Da dama cikin masu karatu za su yi mamakin abubuwa da yawa da za su karanta cikin wannan kasida, kamar yadda ni ma na sha mamaki sosai a yayin da nake gudanar da bincike kansa.  Akwai abubuwan al’ajabi dangane da ruwa.  Akwai abubuwan mamaki dangane da tsari da yanayin ruwa.  Kai, akwai ilmi mai dimbin yawa dangane da abin da ya shafi sinadaran da ke dauke cikin ruwa.  Za mu yi bayani in Allah ya so kan samuwar ruwa.  Daga ina yake samuwa?  Da bayani kan yanayinsa.  Da bayani kan tsarin samuwarsa.  Da bayani kan sauran al’amuran da suka shafi wannan kyauta ta Ubangiji.  Wadannan bayanai za su zo ne ta mahangar kimiyya.  Duk da yake akwai ishara da za mu yi kan tsarin samuwarsa kamar yadda Allah ya sanar a Kur’ani mai girma.  Don haka wannan kasida za mu kasa ta kashi biyu ne; kashin farko kan abin da Kalmar “ruwa” ke nufi, da yadda yake samuwa, da wuraren da ake samunsa.  Sannan a kashi na biyu mu yi bayani kan nau’ukan sinadaran kimiyya da ke dauke cikin ruwa.  Sai a kasance tare da mu.

Ruwa, Daga Ina Kake?

Dan adam, duk da dadewarsa a doron wannan kasa, ya tashi ne ya samu wannan sinadari mai matukar muhimmanci a muhallinsa.  Ruwa yana samuwa ne ta manyan hanyoyi guda uku muhimmai.  Akwai ruwan sama, wanda ke zuba daga sama, bayan samuwar hadari da iska kenan.  Akwai ruwan teku, da kogi, da rafi.  Sannan akwai ruwan da ke samuwa daga karkashin kasa, tsakanin duwatsun da ke cikin kasa kenan.  Wannan bangare ne muke samu ta hanyar haka rijiyoyi ko kuma samuwar idaniyar ruwa.  Bayan haka, idan aka kasa wannan duniya tamu zuwa kashi 100%, kashi 70.9% duk ruwa ne, sauran kashi 29.1% ne kawai gundarin kasan da muke takawa, muke yin noma a kai, sannan muke gina muhallin da muke rayuwa a kai.

Alkaluman malaman kimiyya da suka samu sanadiyyar bincike da suka gudanar kan samuwar ruwa a wannan duniya tamu, sun tabbatar da cewa, kashi 1.6% cikin kashi dari na ruwan da ake da shi a wannan duniya yana karkashin kasa ne.  Wannan kaso ne suke kira “Ground Water”, kuma daga wannan adadi ne muke samun ruwan rijiya, da idaniyar ruwa masu gudana ba tare da an hako su ba.  Kashi 0.001% kuma na samuwa ne a yanayin tururi da ke sararin wannan duniya tamu, wato “Water Vapor” kenan.  Sai kashi 97% da ke samuwa daga tekunan duniya baki dayansu.  Sai kashi 2.4% da ke samuwa a yanayin tsaunukan kankara (wato Glacier kenan) da ke cikin teku, ko wanda ke makare cikin sararin samaniyar wannan duniya tamu. Sai kuma kashi 0.6% da ke samuwa daga rafuka, da koguna, da gulabe ko madatsun ruwa da muke ginawa.  Har wa yau, masana sun nuna cewa, daga cikin kason ruwan da ke wannan duniya tamu akwai kadan da ke cikin jikin halittu masu rai.  Misalin da suka bayar shi ne kan dan adam, inda suka nuna cewa kashi 50% zuwa 70% na abin da ke jikin dan adam ruwa ne.  Sauran kashi 50% ko 30% din ne jinin jikinsa.

- Adv -

Har wa yau, cikin binciken da malaman kimiyya suka gudanar akwai samuwar ruwa a wasu duniyoyin ba wacce muke rayuwa cikinta ba.  Suka ce bincikensu ya tabbatar da samuwar ruwa a yanayin ruwa kamar yadda muka sanshi ko yanayin kankara, a wasu daga cikin duniyoyin da ke makwabtaka da tamu duniyar. A duniyar Makyuri (Mercury) a misali, akwai ruwa iya kashi 3.4%.  A duniyar Benus (Venus) kuma akwai ruwa wajen kashi 0.002%.  Sai duniyarmu, wato Earth, wacce ke dauke da kashi 0.04% (cikin kashi dari na ruwan da ke duniyoyin baki daya kenan).  Sai kuma duniyar Marrik (wato Mars) wacce ke dauke da kashi 0.03% cikin dari.  A duniyar Jufita (Jupiter) kuma akwai kashi 0.0004% cikin dari.  Sai duniyar Satun (Saturn) wacce ke dauke da ruwa amma a yanayin kankara yake, saboda cikin duniyoyin da ke da tsabar sanyi.  Bayan haka, akwai kashi 91% na ruwa da ke makare cikin sararin samaniyar Tauraron Enceladus, wato Tauraron Saturn kenan.  Wannan, a takaice, shi ne kason kimar ruwa da Allah ya rarraba a duniyoyin da muka iya gano su yanzu; ko dai a yanayin ruwa kamar yadda muka saba mu’amala da shi, ko kuma a yanayin kankara. To sai dai kuma ta yiwu wani yayi tunanin cewa, in har ana samun ruwa a wasu duniyoyin, me yasa ba a iya rayuwa a sauran duniyoyin sai wannan duniyar tamu kawai?

Samuwar Ruwa da Tsarin Zamantakewa

Mai karatu zai yi mamakin jin cewa, wannan muhalli na duniya da muke rayuwa a cikinsa na iya bamu damar yin rayuwa cikin sauki ne sanadiyyar samuwar ruwa da yanayin zafin da yayi daidai da gudanuwar rayuwa.  Malaman kimiyya suka ce wannan duniya ta mu Allah ya ajiye ta ne a wani bigire matsakaici, wanda yanayinsa ke ba da damar samuwar wani yanayin zafi ko sanyi da ya dace da dabi’armu. Suka ce da a ce Allah ya ajiye duniyarmu nesa da rana ko kusa da rana da tazarar da ta kai kashi biyar 5% cikin dari daga nisan tazarar da ke tsakaninta da rana a yanzu ne, ko kwatankwacin tazarar kilomita miliyan takwas (8 Million Km) daga inda rana take, to da duniyar bata yi dadin zama ba, sannan da ba a samu yanayin ruwa da rayuwar dan adam a wannan muhalli ba.  Allah Buwayi Gagara misali!

Masana suka ce sabanin sauran duniyoyin da ke makwabtaka damu, wannan duniya ta mu tana dauke ne da maganadisun jawo abubuwa zuwa kasa, a sararinta.  Wannan dabi’a ita ake kira Force of Gravity a kimiyyance.  Idan kana son gano haka, ka dauki wani abu ka jefa shi sama, nan take za ka ga ya dawo kasa.  Hausawa ma da kansu sukan ce: “Komai nisan jifa, kasa zai dawo.”  Wannan karin magana an gina shi a bisa wannan dabi’a ta maganadisun jawo abubuwa kasa, ko Force of Gravity a kimiyyance.  Sauran duniyoyi ba su da wannan dabi’a, kuma shi yasa idan masu zuwa duniyar wata suka je, sai ka ga kamar suna yawo ne a kan iska.  Wannan maganadisu ne ke taimakawa wajen rike dukkan tururin ruwan da ke cikin sararin wannan duniya ta mu, don haifar da yanayin zafi ko sanyin da yayi daidai da rayuwar masu rayuwa a cikin duniyar.  Suka ce da a ce girman wannan duniya bai kai yadda yake ba a yanzu, to da hakan zai haifar da wani yanayi mai tsananin zafin gaske, wanda dan adam ba zai iya rayuwa a ciki ba.  Ba don tsananin zafin kadai ba, sai don yanayin ba zai ba da damar samuwar ruwa ba, balle har wata halitta mai rai ta iya rayuwa a cikin duniyan baki daya.

Ruwa a Yanayi Uku

Ruwa yana samuwa ne a yanayi guda uku a wannan duniya ta mu.  Yanayin farko shi ne narkakken yanayi, ko Liquid Form a turance.  Wato yanayin da ke bayar da damar a diba, a sha, a yi wanki dashi, ko wanka, ko duk wani tasarrafi cikin sauki.  Wannan shi ne yanayin asali da kowane dan Adam ya san ruwa dashi.  Yanayi na biyu kuma shi ne yanayin tururi, wato Gaseous Form a turance.  Ruwa a wannan yanayi ba kowa ya sanshi ba, galibi sai daliban kimiyya ko masana kimiyya.  Idan ka zuba ruwa a cikin kofi, sai ka ajiye shi a waje, inda iska ke bugawa ko rana take, nan da wasu ‘yan lokuta za ka ga yawanshi ya ragu.  Sauran ina suka bi?  Sun bi iska sun haura zuwa sararin samaniya.  A wani irin yanayi?  A yanayin tururin iska. Wannan tsari da ke baiwa ruwa daman narkewa zuwa yanayin tururin iska shi ake kira Evaporation.  Yanayi na uku kuma shi ne ruwa a yanayi daskararre, ko Solid Form a turance.  Wannan kuwa shi ne ruwa a yanayin kankara.  Wannan kowa ya sanshi.  Akwai bayanai masu gamsarwa idan muka zo yin bayani kan sinadaran da ke dauke cikin ruwa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.