Sakonnin Masu Karatu (2022) (5)

Ginshikan Fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwa na Zamani

Fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwa shi ne tsarin dake taimakawa wajen aiwatar da sadarwa mai inganci, ta amfani da na’urori da kuma hanyoyin sadarwa na zamani, don gudanar da harkokin rayuwa.  Dangane da ma’anar wannan fanni da ya gabata, za mu fahimci cewa fannin na dauke ne da manyan ginshikai guda biyu, wadanda su ne suke haduwa da juna wajen haifar da sadarwa a yanayin da muke gani kuma muke ta’ammali dashi a halin yanzu. – Jaridar AMINIYA, Jumma’a, 9 ga watan Satumba, 2022.

165

Kamar makon jiya, yau ma za mu ci gaba ne da amsa tambayoyin masu karatu.  Da fatan za a ci gaba da kasancewa tare damu yadda aka saba.

——————–

Assalamu alaikum, barka da warhaka Baban Sadik.  Ka dade kana rubutu a kan fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani, amma har yanzu na kasa fahimtar yadda wannan fanni yake; ma’ana, me da me ke haduwa don samar da wannan fanni?  Ko ince, wasu abubuwa ne cikin sauki, za su taimaka ma mutum wannan fanni ba tare da wani dogon karatu ba? Ina godiya matuka.  Ni ne mai karanta shafinka a AMINIYA da Taskar Baban Sadik:  Murtala Bala Isiya, Rano, Jihar Kano – isiyarano30@yahoo.co.uk.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Murtala.  Lallai zancenka gaskiya ne; fannin kimiyya da fasahar sadarwa fanni ne na ilmi mai fadin gaske, kuma kusan kullum ci gaba ake samu a fannin.  A takaice dai, babu fanni mai saurin habaka da ci gaba irin wannan fanni.  Musamman ganin cewa ya shafi kusan dukkan fannonin rayuwa da dan adam ke dogaro dasu don samun saukin rayuwa.  Don haka, a yau zan yi bayani dalla-dalla dangane da bangarorin wannan fanni, don samun gamsasshiyar fahimta.

Da farko dai, fannin Kimiyya da Fasahar Sadarwa shi ne tsarin dake taimakawa wajen aiwatar da sadarwa mai inganci, ta amfani da na’urori da kuma hanyoyin sadarwa na zamani, don gudanar da harkokin rayuwa.  Dangane da ma’anar wannan fanni da ya gabata, za mu fahimci cewa fannin na dauke ne da manyan ginshikai guda biyu, wadanda su ne suke haduwa da juna wajen haifar da sadarwa a yanayin da muke gani kuma muke ta’ammali dashi a halin yanzu.  Ga takaitattun bayanai nan kan wadannan ginshikai.

Na’urorin Sadarwa

Na’urorin sadarwa su ne na’urorin da ake amfani dasu wajen aiwatar da sadarwa.  Kuma su ne suke dauke da dayan ginshiki ko rukunin, kamar yadda bayani zai biyo baya.  Wadannan na’urori dai su ne:

Kwamfuta da Dukkan Nau’ukanta:  kwamfuta ita ce na’ura ta farko, kuma uwa wajen samar da ci gaban da muke gani a yanzu.  Kwamfuta ce ke dauke da ka’idojin sadarwa dake taimakawa wajen aikawa da kuma karban sakonni cikin sauki.  Wadannan ka’idoji dai su ake kira: “Protocols” a harshen turancin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani.  Bayan kwamfuta nau’in gama-gari da muka sani, akwai kwamfutoci na musamman da ake kerawa wajen taskancewa da adana bayanai ta hanyar Intanet.

Wayar Salula da Dukkan Nau’ukanta:  Wayar salula na’ura ce mai amfani da siginar rediyo, dauke da katin SIM, don aiwatar da sadarwa ta hanyar sauti.  Sannan ana amfani da ita wajen ta’ammali da hanyoyin sadarwa na zamani.  Wannan na’ura ita ce ginshiki na biyu bayan kwamfuta, wajen haddasa ci gaba a fanni sadarwa na zamani.

- Adv -

Tauraron Dan Adam:  Bayan kwamfuta da wayar salula da dukkan nau’ukansu, tauraron dan adam ne ginshiki na gaba wajen aiwatar da sadarwa.  Da wannan na’ura, wacce ake cillawa cikin sararin samaniya, ake aiwatar da sadarwa a bangaren yada labaru, da binciken yanayi, da tantance bingire ta amfani da manhajar taswira.

Na’urori Masu Fasaha (Smart Devices/IoTs):  wadannan na’urori dai asali ba a kera su don amfani da Intanet ko wata hanya ta sadarwa ba, amma daga baya ne aka tsofa musu tsarin fahimta don yin hakan.  Ire-iren wadannan na’urori sun hada da na’ukan agogon zamani da ake iya aiwatar da sadarwa dasu (Smart watch), da motoci marasa direba (Driverless cars), da dai sauransu.  Wadannan na’urori dai daga baya ne aka fara amfani dasu, kuma ana ci gaba da kera su yanzu, don sawwake tsarin sadarwa.

Hanyoyin Sadarwa

Bayan na’urorin sadarwa, wadanda su ne ginshikin farko, sai hanyoyin sadarwa, wato hanyoyin sadarwa kenan.  Wadancan na’urori dai su ne suke dauke da hanyoyin sadarwa.  Hanyoyin sadarwa suna da yawa, saboda a kullum kara samun fasaha ake wajen samar dasu.  Wadanda suka fi shahara kuma suka zama ginshikai, su ne kamar haka:

Fasahar Intanet:  wannan ita ce uwa kuma turba a tsarin sadarwa na zamani.  Duk wata hanyar sadarwa na zamani a yau tana dogaro ne da fasahar Intanet; ko dai kai tsaye, a kaikaice.  Intanet dai tsari ne dake baiwa kwamfutoci ko wayoyin salula ko wata na’urar sadarwa, damar Magana da ‘yar uwarta wajen aikawa ko karban bayanai.  Duk sadda ka bude manhajar whatsapp ko facebook a wayarka, don ganin sakonnin da aka aiko maka, to, wayarka ta yi tattaki ne zuwa kwamfutar kamfanin dake dauke da manhajar (Facebook, ko Meta, misali), ta nemi a bata wadannan bayanai, sannan, bayan an tantanceta, aka miko mata, ita kuma ta bayyana maka su a shafin wayarka.  Komai na rayuwa a halin yanzu ya koma giza-gizan sadarwa na duniya, wato: “World Wide Web”; asalin tsarin dake dauke da Intanet kenan.

Fasahar Imel:  Imel hanya ce ta sadarwa don aika sakonni tsakanin mutane.  Tana amfani ne da ka’idar sadarwa mai suna: “Simple Mail Transfer Protocol” (SMTP), wanda aka gina shi a jikin waya ko kwamfuta ko na’urar sadarwa. Imel nau’i biyu ne; akwai mai amfani da Intanet, irin su Gmail, da Yahoo kenan misali.  Su wadannan su ake kira: “Web mail application”.  Akwai kuma wadanda ba sa bukatar Intanet wajen aikawa da karban sakonni daga gare su. Su wadannan sun hada da Microsoft Exchange, da Outlook da dai sauran makamantansu.

Kafafen Sada Zumunta (Social Media):  Wadannan su ne shafukan sada zumunta da muka sani, na wayar salula – irin su WhatsApp, da Instagram – da wadanda ake amfani dasu ta kwamfuta da waya – irin su Facebook, da Youtube, da Pinterest, da LinkedIn da sauran ire-irensu.  Wadannan kafafe suna bai wa mutane damar aiwatar da sadarwa ne cikin sauki, ta amfani da rubutattun sakonni, da hotuna, da bidiyo, da kuma sauti.

Mudawwanai:  Mudawwana ita ce Blog a harshen fasahar sadarwa na zamani.  Shafi ne da ake budewa a matsayin gidan yanar sadarwa, don wallafa ra’ayoyi da sharhi kan fannonin rayuwa.  Masu wannan kafa za ka samu kwararru ne – Malaman Jami’a, da ‘Yan Jaridu, da ‘Yan Siyasa, da sauran makamantansu.  Wannan hanya ce ta bayyana ra’ayi, da kuma musayar fahimta tsakanin masu wallafa ra’ayoyinsu da masu karantawa.

Kamar yadda na sanar a baya, hanyoyin sadarwa suna da yawa, shi yasa na takaitu ga wadannan.  A takaice dai, duk wata manhaja ko shafi na gidan yanar sadarwa dake bai wa jama’a damar musayar ra’ayoyi da fahimta da bayanai, to, hanya ce ta sadarwa. Da fatan ka gamsu da wadannan takaitattun bayanai.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.