Rayuwata a Duniyar Sadarwa (4)

Takaitaccen tarihina ne wannan kan irin gwagwarmayar da na sha a fannin bincike kan kimiyya da fasahar sadarwa na zamani. Wannan kashi na hudu kenan. A sha karatu lafiya.

448
Bayan dogon bincike a Intanet da dabi’ar kwakwa wajen kwakule-kwakulen gangar-jikin kwamfuta da na koya, da iya sarrafa ta cikin sauki a wajen aiki, abu na gaba da ya kara agaza mini, cikin dacewar Ubangiji, shi ne rubuce-rubuce da na shiga yi.

Jaridar AMINIYA

Mustapha Mu’azu abokin aikina ne kuma tsohon ma’aikacin kamfanin Media Turst ne, wato kamfanin dake buga jaridar Weekly Trust, da Daily Trust, da kuma AMINIYA kenan.  Shugaban kamfanin shi ne Kabiru Yusuf.  Cikin watan Oktoba na shekarar 2006 da aka fara buga jaridar AMINIYA da Daily Trust, sai Mustapha yace mini: “Me zai hana ka rika yi wa jaridar AMINIYA rubutu kan harkar Intanet din nan?” Mustapha ya mini wannan tambaya ne ta la’akari da wata doguwar kasida mai take: “Intanet da Rayuwar Hausawa” da na taba rubutawa aka buga a jaridar At-Tajdid da ke Kano, wacce Malam Bello Sharada da su Bashir Sa’ad Abdullah (na BBC yanzu) ke bugawa a duk ranakun jumu’a. Su kuma masu jaridar At-Tajdid, wanda ya hada ni dasu shi ne amini na, wato (Dr.) Muhammad Jameel Yusha’u, wanda a halin yanzu yake karantarwa a wata Jami’a da ke Ingila.   Wannan kasida, duk da cewa ba ita kadai na rubuta a jaridar At-Tajdid ba, amma ita ce kasidar farko kan harkar sadarwa da Intanet, da ta haddasa duk wani rubutu da nake yi a halin yanzu kan harkar sadarwa. A halin yanzu shekaru na 8 ina rubutu a jaridar AMINIYA.  Sadda na fara rubutu, a ma’adanar Floppy Disk nake taskancewa ina aika musu, a duk mako.  Mustapha ne ke karba, ya baiwa Malam Abubakar AbdurRahman (Dodo), wanda shi ne ke lura da shafin nawa, kafin zuwan Ahmed Garba.  Daga baya suka rubuto mini takarda ta musamman don yaba kokarina, sannan suka shigar dani cikin masu yi wa jaridar hidima.  Wannan ya faru ne bayan watanni kamar shida da fara wannan aiki na kashin kai.

Fa’ida Ga Masu Karatu

Tsawon wannan shekaru da nayi, na rubuta kasidu da makaloli sama da 300!  Na kuma karu da ilimi mai dimbin yawa, da darussa na rayuwa da ake koya sanadiyyar ta’ammali da jama’a mabambanta, mai girman gaske.  Darasin da na koya da ilimin da na karu dashi, ya fi wanda aka koya daga gare ni.  Duk da cewa shafin ya shajja’a (zaburar) matasa matuka.  Akwai da yawa wadanda sanadiyyar darussan shafin suka koma makaranta, na sansu.   Akwai wadanda sanadiyyar darussan suka canja maudu’in karatu zuwa harkar kwamfuta, akwai wadanda suka samu shedar karatu kan ilimin kwamfuta ban san iyakansu ba.  Bayan wadannan, akwai wadanda kuma suka mayar da maudu’in bincikensu na karasa karatu (Academic Project) a fannin harshen Hausa zuwa bangaren kwamfuta.  Na kuma gamsar dasu da kasidun da suke bukata har suka gama.  Wadanda suka karbi kasidun da niyyar binciken ilimi kuwa Allah kadai ya san yawansu.

Dandalin Facebook

Cikin shekarar 2009 na shiga Dandalin Facebook, na bude shafi, sannan na ci gaba da cilla kasidun da nake rubutawa.  Duk da cewa kafin nan, na bude Mudawwana (Blog) inda nake zuba kasidun, tun shekarar 2007.  A nan ne wasu ke samun kasidun suna karantawa, musamman wadanda suke wajen kasar.   Tsawon shekarun da nayi a Dandalin Facebook ya bani damar mu’amala da masu karatu kut-da-kut, sannan ta hanyar ce na samu haduwa da tashar Sunnah TV, wacce suka killace shiri na musamman mai suna: “Kimiyya da Fasahar Sadarwa” don gayyata na ina bayani a lafazance, kan abin da Allah ya hore mini.  Bayan haka akwai tarurruka da aka gayyace ni inda na gabatar da makaloli kan harkar kimiyya da fasahar sadarwa a Najeriya.

Darasi

Jama’a, wannan kadan ne cikin kadan na abin da ya shafi rayuwata a wannan fanni.  Manyan darussan da na koya kuwa su ne: hakuri da juriya kan kai mutum ga gaci, duk dadewa.  Sannan sanin ilimin addini tun yarinta kan taimaka wa mutum wajen neman kowane irin ilimi ne halastacce na gwagwarmayar rayuwa.  Galibin abin da ke bambance rubutu na da na wasu da suka yi kan wannan maudu’i shi ne, ina kokarin gwama wannan ilimi da tarbiyyar addini; wajen halacci ko haramci. Na kuma fahimci cewa, iya shahararka iya yadda za ka fuskanci matsalolin jama’a mabambanta.  Akwai wadanda ba su da sana’a a kullum sai dai su yi ta mini filashin. Tun ina fada a lafazance, na koma rubutawa a jarida, a karshe sai hakura nayi.   Idan ka mini filashin sai in kira ka, in ka dauka mu gaisa, idan kaki dauka in hakura.  Akwai wanda ya dauki tsawon wata guda yana mini filashin a duk rana, idan na kira shi kuma yaki dauka.  Akwai masu kira su kunduma mini zagi, musamman kan bayanin da nayi na cewa akwai masu yada hadisan karya kan watan rajab, ta hanyar tes.   Akwai wanda ya min filashin na kira shi, ya min tambaya kan masu fim na hausa, nace “wrong number,” sai ya kunduma mini zagi, nace na gode.  Duk wadannan abubuwa ba abin da suka kara mini sai kwarin gwiwa, da jajircewa, da kuma kara sanin hakikanin dan adam a aikace.

Yaba Kyauta…

A karshe, mutanen da na hadu dasu, da abubuwan da na ci karo dasu na alheri, sun ninka duk wata matsala da naci karo da ita.  Don haka nake mika godiya tsarkakakkiya ga Ubangiji Allah da ya bani wannan ni’ima, ina rokonsa ya bani dama da ruhin sauke nauyin dake kaina na yaba wa ni’ima.

- Adv -

You might also like
6 Comments
 1. Ibrahim A Ahmad says

  Allah ya kara ilmi, muna godiya kwarai da gaske

 2. Usman muazu says

  Allah ya kara daukaka da illimi mu kam sai godia saboda shafinka tun 2017 nake sayen aminiya duk sati.

 3. Mansur Kajuru says

  Allah ya saka da alkhairi ya kuma baka tsawon rayuwa Malam.Muna godiya koda yaushe.

 4. Hassan Muhammad sani says

  Allah ya sakawa mallam damn database kana cikin koshin lafiya.

 5. Muryar Hausa24 Online Media says

  MASHA ALLAH

  LALLAI RAYUWAR MALAM CIKE TAKE DA DARUSSA MASU MUHIMMANCI, NA KARU DA ABUBUWA MASU YAWA A WANNAN MAKALA.

  KANA DAYA DAGA CIKIN WADANDA SUKA JA RA’AYI NA ZUWA DUNIYAR SADARWA, DOMIN NI MA NA BAYAR DA GUDUNMAWA TA.

  ALHAMDULILLAH!

  ALLAH YA KARA MANA HAKURI DA JURIYA A CIKIN DUK AL’AMURAN MU NA YAU DA KULLUM🙏🏻

 6. Auwalu Adamu says

  Alhamdulillah,
  Hakika tsakanin mu da kai sai addu`ar Allah ya kara lafiya ya ci gaba karfafar gwiwarka, ya kuma kara juriyar hakurin da jama`a.
  Muna godiya Allah ya bar zumunci.

Leave A Reply

Your email address will not be published.