Tsarin Amfani da Wayar Salula (9)

Kashi na 34 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

282

Wanka da Wanki

Wayar salula na bukatar wanka da wanki.  Amma fa ba irin wanka da wankin da Malam Bahaushe ya sani ba.  Ana nufin tsaftacewa ta amfani da kayan wankewa da tsaftacewa.  Idan kana da sinadarin Spirit, kana iya kwance wayarka, ka wanke murafenta da burosh, sannan ka goggoge inji da kyau, don kawar da dukkan kuran da ke ciki.  Bayan haka, kada ka bari ruwa ya rika shiga cikin wayar, za ta sume har da sandare, in ma ba a yi sa’a ba ta haukace; sai an mata sabon zubin rai ta hanyar filashin da kwamfuta. Idan ba za ka iya ba, ka kai wa mai gyaran waya ya wanke maka (ko sabis, kamar yadda suke cewa), ka biya ladan aiki.

Wannan na cikin abin da zai dada taimakawa wajen kara mata kuzari da tagomashi.  Kada ka bari sai ta fara baka matsala ka nemi wurin mai gyara.  Watakila ma kura ne yayi mata yawa, sabis kawai take so, amma tunda baka sani ba, kana kaiwa sai yace ai sai an sake kaza da kaza, kana tafiya ya mata sabis shikenan.  Ka ganta garau.  Sai a kiyaye.

Wayar salula da Lafiyarka

Bayan aiwatar da kira da karban kira, da sauran amfanoni da mai waya ke samu daga wayar salula, yana da kyau kuma a daya bangaren ya fahimci cewa, amfani da wayar salula ba tare da ka’ida ba na haifar da cutarwa ga lafiyar jiki.  Wannan na samuwa musamman hatta a lokutan bacci, da kuma tasirin yawan kallo da yawan sauraro na tsawon lokaci.

Lokacin Bacci

Galibin jama’a kan bar wayoyin salularsu a kunne a lokacin da za su kwanta, ko su sa a caji, ko su kashe, ko su kashe amon wayar, ko su sa ta a tsarin girgiza (Vibrating).  Wani yanayi ne yafi dacewa ga mai mu’amala?  Idan aka baiwa jama’a damar tattauna wannan zance, kowa zai fadi abin da yafi sha’awa ne, ko tsarin da ya saba da shi.  Amma a hakikanin gaskiya, idan muka yi la’akari da lafiyar jiki, kashe amon wayar shi ne abin da yafi dacewa a lokutan bacci, ko da kuwa kai kadai kake kwanciya a dakin.  Domin idan ka barta a kunne da amonta, a duk lokacin da aka kira ka cikin talatainin dare kana iya ji musamman idan kai ba mai zurfin bacci bane irin Baban Sadik. To, sai dai kuma hakan na iya firgita ka, ka tashi a firgice.  Watakila kiran ba wani mai mahimmanci bane.  Haka idan kana kwanciya daki daya ne da iyalinka, yana iya firgita ta, ko da kai ba ka tasirantuwa da sautin.  Balle a ce akwai jariri ko karamin yaro ko yara a inda kuke.  Don haka, ko dai ka kashe amon wayar ne yayin kwanciya, ko kuma ka rage ta yadda kai kadai za ka iya ji.

Wasu kan ce ai barin amon waya cikin dare yana da amfani, domin idan wata ‘yar gagggawa ta gitta ana iya nemanka ka tashi nan take, don kawo dauki.  Sai dai kuma abin da za a lura shi ne, sau nawa hakan ke faruwa cikin ranaku?  Bayan haka, duk wanda zai kira ka cikin dare idan ba kai bane kace ya kira ka, ya san ba lokacin da ya dace  bane a kira mutum a cikinsa.  Don haka ko da ya ji ba a daga ba, bai kamata ya damu ba.

- Adv -

Har wa yau kuma duk da cewa ba a son kwana da amon waya a kunne saboda guje wa samun firgici ga mai waya ko wanda ke dakin, haka kuma bai kamata mutum ya rika kashe wayarsa ba gaba daya cikin dare, sai in babu caji.  Domin gwamma a kira baka ji amon waya ba, da a ce an kira wayar a kashe.  Domin idan ka farka ka ga kiran da aka maka, nan take za ka so kira; musamman idan kira ne da ba a saba tsammanin shigowarsa cikin dare ba.  Sannan, barin waya a tsarin girgiza (Vibration), shi ma yana iya mummunar tasiri wajen firgitar da mutum, sai ga wanda ya saba.  Domin idan aka yi rashin sa’a mutum na halin mummunar mafarki sadda wayar ke girgiza, hakan na iya mummunar tasiri ga lafiyarsa, don a firgice zai farka.

Abu na karshe shi ne, in da hali, kafin mutum ya kwanta ya kamata ya tabbatar akwai kudi a katin wayarsa, domin hakan zai iya taimaka masa wajen sadar da kira cikin dare idan bukatar hakan ta taso.  Bayan samuwar kudi a wayar, ya zama kuma akwai caji.  Sannan kuskure ne a sanya waya a caji a kwanta barci. Domin idan aka yi rashin sa’a batirin da ke wayar jabu ne ba ingantacce ba, kuma wayar ta gama caji ba a cire ta ba, tana iya fashewa ta kama da wuta.  Haka ma kwamfutar tafi-da-gidanka.  Muddin aka sa a caji, to a rika lura, da zarar caji ya cika, a cire.  Shi ne zaman lafiya. Da hasara, inji Bahaushe, gwamma kauyanci.

Sauraro da Kallo

Wadannan dabi’un dukkan mai mu’amala da wayar salula ne, musamman a kasashen Turai da Asiya.  Galibin kallace-kallace da sauraron kide-kide da wake-wake duk sun koma ta wayar salula yanzu.  A halin tafiya ne ko a halin zaman gida; a wajen aiki ne ko a kan titi ne; duk inda ka dubi jama’a za ka gansu a shagalce suke da wayoyin salularsu.  A kasashe masu tasowa irin namu, musamman da bayyanar wayoyin salula na kasar Sin masu saukin kudi da dan karen kara. Galibin jama’a a yanzu sun samu sauki wajen kallon abin kallo na bidiyo, da sauraron dukkan wani abin da suke sha’awan sauraro, cikin sauki.  Akwai wadanda aikinsa kawai shi ne loda wa wayoyin salula wakoki na sauti ko na bidiyo, musamman fina-finan Hausa da na Indiya da dai sauransu, cikin farashi mai rahusa.

A yayin da hakan ya zama sauki, yana da kyau kuma mu fahimci hadarinsa da tasirinsa ga lafiyar jiki.  Yawan kallon fina-finai ko abin kallo a wayoyin salula musamman masu kananan fuska (Screen), kuma a cikin duhu ko cikin dare a inda babu haske, yana haifar da wani irin radadi a cikin ido, da radadi a goshi, wadanda samuwarsu ke nuna matukar gajiya irin ta kwakwalwa.  Irin wannan dabi’a na tasiri matuka wajen haddasa mantuwa musamman ga mutumin da yake hadda. Ba kuma zai samu natsuwa ba a galibin lokutansa.  Idan wannan ya zama dabi’a a gare shi, zai yi wahala ya iya jure zama don karanta wani abu daga littafi. Saboda ya saba da kallo.  Don haka kwakwalwarsa ba ta iya jure komai in ba kallo ba.  Sai a kiyaye.

Dangane da sauti mai karfi ko mai kara kuma, ya kamata mu fadaka.  Ba kowane dan adam bane dodon kunnensa ke iya jure sauti mai karfi.  Ya danganci tsari da kintsin halittarsa, da karanci ko yawan shekarunsa.  A takaice dai, duk yadda mutum ya kai da iya jure sauti mai karfi a kunnensa, tsawon lokaci a cikin irin wannan yanayi na iya sa masa kurumtaka na wucin gadi.  Za a wayi gari ba ya jin sautin wanda ke kusa da shi balle na nesa; sai an daga murya sosai.  Shi kanshi yawan jin kide-kide da wake-wake mara kangado na sangartar da kwakwalwar mutum, tare da soyar masa da yawan shantakewa.  Sai a kiyaye.  Duk abin da za a yi, a rika yinsa daidai ruwa daidai gari. Kada a wuce gona da iri.

Wasu Jita-jita

Dangane da abin da ya shafi amsa kira ta wayar salula, akwai jita-jita da wasu ke yadawa cewa, tururin sinadaran maganadisun rediyon lantarki (Radioactive Waves) da ke fita daga jikin wayar salula a yayin da ake aiwatar da sadarwa, wai yana haddasa cutar sankarar kwakwalwa, wato “Brain Cancer.”  Wannan magana ko kadan ba haka take ba.  An sha aiko tambayoyi kan haka.  Ganin haka yasa na leka duniyar gizo don nemo tabbaci, amma babu abin da na samu ingantacce; sai jita-jita irin wadda ke yaduwa a kasashenmu.  Tabbas akwai abin da ke fita daga jikin wayar salula idan mai waya na amsa kira ko aiwatar da kira, amma babu wani tabbataccen dalili ko bayani mai nuna cewa wannan tururi na maganadisun rediyon lantarki (Radioactive Waves) na haifar da wata cuta mummuna kamar yadda ake riyawa. In ma akwai, to har yanzu bincike bai gano ko ba.

Sai dai, kamar yadda na sha fada ne, duk abin da mutum zai yi a rayuwa, ba wajen mu’amala da wayar salula kadai ba, to ya yishi daidai ruwa daidai gari.   Idan abu ne mai kyau, zai samu nishadi a yayin da yake yinsa, kuma zai dauki tsawon lokaci yana yi bai gaji ba. Idan kuma mara kyau ne, Allah sawwake, zai yi wahala yayi mummunar sabo da shi, balle ya kasa barinsa.  Allah sa mu dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.