Tsarin Amfani da Wayar Salula (8)

Kashi na 33 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

316

Tsarin Lura da Wayar Salula

Wayar salula kamar sauran kayayyakin amfani ne na gida ko na wajen aiki; suna bukatar a rika lura da su, in kuwa ba haka ba, sai su rasa tagomashi da kimarsu, ko su salwanta tun lokacin salwantarsu bai yi ba.  Abin da wannan sashe zai duba ya kunshi tsarin kunna wayar salula, da kashe wayar salula, da adanawa a yayin da mai wayar ke yin wani abu daban, da sanya wayar a caji don tabbatar da ci gaban karfinta wajen ba mai ita damar sarrafa ta ba tare da matsala ba.  Sauran al’amuran sun shafi tsarin shigarwa da mika bayanai, da kuma wanka da wanki, don tabbatar da tsafta da tsawon rayuwa. Lafiya, in ji Hausawa, uwar jiki ce.  Haka lamarin yake a bangaren mu’amala da sarrafa wayar salula.

Kunnawa da Kashewa

A duk sadda mai karatu ya sayi wayar salula sabuwa kar, abu na farko da ya kamata ya fara koyo daga gare ta shi ne yadda ake kunnawa da kashe wayar, domin abubuwan da za su fi maimaituwa a gare shi kenan yayin mu’amala da wayar.  Bin ka’ida wajen kunnawa da kashe waya na daga cikin abubuwan da ke kara mata dogon kwana a hannunka.  Tsarin kunna waya shi ne ka matsa maballin da ake kunna ta da shi, wanda bayanai suka tabbatar da cewa shi ne maballin da ake kunna ta da shi. Kana iya ganin bayanan karara a cikin kundin da wayar ta zo da shi, wato Phone Manual.  Galibinmu bamu cika damuwa da dubawa ko karanta wannan kundi ba, amma yana da amfani.  A ciki ne za ka ga yadda ake kunnawa, da kuma maballin da ake matsawa don kunnawa.  Haka idan kashewa ne, duk a ciki za ka gani.

Idan ka matsa maballin kunna wayar salula, sai ka jira har sai ta gama kunna kanta tukun.  Za ka iya gane haka ta hanyar kulle kanta, idan ka sa mata makulli, wato Auto Lock kenan.  Idan ba ka sa mata kowane irin kariya ba, za ka iya gane ta gama kunna kanta idan dukkan tambarin manhajojin da ke fuskar wayar suka gama bayyana.  Misali, tambarin yanayin sadarwar, da tambarin harbawan batir, da tambarin agogo, da tambarin kamfanin sadarwa da dai sauransu.  Sai duk sun gama bayyana sannan sai ka fara amfani da wayar; idan kira za ka yi, sai ka nemo lambar wanda kake son kira.  Idan kuma ba kira za ka yi ba sai ka sa a aljihu ko jaka, misali.

Amma kafin nan, zai dace ka tabbatar ta kulle kanta kamar yadda ta saba yi kafin ka sa a aljihu. In kuwa ba haka ba, cikin kuskure kana iya dannawa ko matsa maballin kira alhali tana bude, a lokacin da ka jefa cikin aljhu, kuma nan take sai ta fara kiran wanda ka matsa lambarsa cikin kuskure, har ya dauka yayi ta halo, halo, baka sani ba.

Idan ka tashi kashe wayar salula zai dace ka rufe dukkan masarrafai ko manhajar da ka bude tukun.  Misali, idan ka budo masarrafan rubuta sakonnin tes ne, kada kace za ka kashe wayar bayan baka rufe manhajar da ke bude ba.  Wannan kuskure ne.  Haka idan wakoki kake saurare, ka rufe manhajar kidin tukun, sannan kayi kokarin kashe wayar.  Idan babbar waya ce wacce ake iya bude manhajoji sama da daya a lokaci daya, kamar wayoyin salula nau’in Smartphones, zai dace ka je Menu, ka tabbata kowace manhaja a rufe take.

Duk manhajar da ba a rufe take ba za ga alama a saman tambarinta.  Sai ka bude, ka matsa Exit daga hannun dama, don rufewa. Sai ka tabbatar kowace manhaja a rufe take, sannan sai ka kashe wayar, ta hanyar matsa maballin da aka tanada don kashewa. In kuwa ba haka ba, akwai manhajojin da za su iya samun matsala a sadda ka kashe wayar suna kunne. Haka kwamfuta ita ma, muddin kana yawan kashewa ba tare da ka rufe masarrafan da ke bude ba, nan take suna iya samun matsala, kuma nan gaba idan ka tashi amfani da su za ka fahimci hakan.  Don haka sai a kiyaye.

Adana Wayar Salula

- Adv -

Adana wayar salula yana da kyau, tunda abin amfani ne kuma da kudi aka saya.  A nan ina nufin inda ya kamata ka ajiye wayar salularka a sadda ba ka amfani da ita, ko kuma kake sauraren wani abu daga jikin wayar.  Idan a ofis kake inda da’iman kana zaune ne a saman kujera, zai dace ka ajiye ta a saman teburin da kake, don duk wanda ya kira za ka ji kuma za gani.  Idan tafiya kake zai dace ka sa a aljihu, muddin ba wangalallen aljihu bane, in kuwa ba haka ba, rikewa a hannu shi yafi.  Idan a kwance kake kana iya ajiyewa a inda kake ganin ya fi dacewa.  Kada ka ajiye wayarka a inda ba ka da tabbacin tsaro, musamman idan bako ne kai.

Kada a ajiye a inda danshi zai iya samunta.  Kada ka ajiye a inda kwazayin rana zai mata illa, ko inda raba zai iya zuba a kanta.  Kada ka ajiye a inda kura zai iya shigewa cikinta.  Kada ka ajiye a inda za ta iya zama fitina ga wasu, musamman idan mai tsada ce.  Ka zama mai kaffa-kaffa da ita a duk inda kaje ko kake.  Bayan haka, idan kana cikin jama’a ne, zai dace ka sa wayar  a yanayin da za ka iya fahimtar an kira ko tes ya shigo, ba tare da ka takura wa wadanda kake tare da su ba.

Tsarin Cajin Wayar Salula

Abu ne sananne ga dukkan masu mu’amala da wayar salula cewa dole ne a rika sa wayar a caji don karin tagomashi da makamashin da za a dogara gare shi wajen aiwatar da ayyukan wayar.  Idan sabuwa ce ka siya, ana son ka sa ta a caji har sai ta cika, sannan ka kunna. Haka aka fi so.  Har wa yau, kada ka rika sa wayarka a caji sai idan cajin yayi kasa sosai.  Wannan na daga cikin abin da ke tabbatar mata da tsawon rayuwa ta bangaren karkon batirin.  Amma na san da yawa daga cikinmu kan sa waya a caji ko da akwai caji a ciki, musamman saboda tsoron dauke wuta.  Sai a gaskiya hakan na rage wa batirin karko.  Kamar dan adam ne, bai kamata ya bukaci abinci ba sai yunta ta kama shi.  Haka ruwan sha, sai kishi ya kama shi.  Domin a lokacin ne abincin da abin shan za su fi masa aiki a jikinsa.  Saboda ya ci ko sha su a lokacin da jikinsa ke da bukata.  Don haka, yawan sanya waya a caji ba tare da cajin ya kare ba, kuskure ne.  A bari sai caji yayi kasa, sai a sa.

A duk sadda za ka sa wayarka a caji a cikin jama’a, to, ya zama kana kusa.  Kada ka bar wayar a kunne, tana caji, a kira ba ka kusa tayi ta damun jama’a.  Wannan kuskure ne.  Sannan idan ma kashewa kayi, kada ka tafi ka bar wayar, musamman idan baka aminta da yanayin wurin ba.  In kuwa ba haka ba, za ka dawo ka tarar da na’urar caji kadai a sagale.  Haka idan za ka bayar ne a wajen masu caji, kamar yadda galibi ake yi yanzu saboda matsalar wutar lantarki a kasar namu, to, zai dace ka kashe wayar, sannan ka bayar.  Idan kuwa ba haka ba, za ayi ta kiranka alhali ba ka kusa.  Wannan na iya sa mai cajin ya rika daga maka waya, wadanda ke kiranka kuma ba lalai bane su ji dadi, tunda kai suke son jib a wani ba.  Kada a sa waya a caji, a bari har ta gama caji ba a cire ba.

Idan kayi rashin sa a aka dauke wuta, nan take cajin da ka yi a baya zai zuke, musamman idan wayar a kashe take.  Sannan kuskure ne idan wayarka na caji, ka amsa kira ba tare da ka cire a jikin wayar cajin ba.  Akwai matsala yin hakan. Duk sadda ka san za ka sa wayarka a caji musamman cikin dare, ta yadda ba za ka san sadda wayar za ta cika ba, to, ka kashe sautin wayar, sai ka barta a kunne.  Ko da an dauke wuta misali, hakan ba zai cutar ba sosai.  Amma idan a kashe take, nan take cajin zai zuke.  Sai a kiyaye.

Tsarin Karba da Mika Bayanai

Ta hanyar wayar salula, kamar yadda mai karatu ya sani, yana iya karban bayanai (rubutattu, da sauti, da bidiyo, da hotuna), sannan yana iya mika wa wasu, duk ta hanyoyin da aka killace don yin hakan.  Akwai fasahar Bluetooth da Infra-red, kamar yadda bayanai suka gabata, sannan akwai amfani da tsarin GPRS, musamman a bangaren hotuna da mu’amala da fasahar Intanet.  Abin da ake son mai waya ya kiyaye shi ne, ya san cewa akwai kwayoyin cutar wayar salula (Virus) da ke shawagi a wayoyin salula.  Idan kayi rashin sa’a wanda ya turo maka bayanai daga wayarsa na dauke da kwayoyin cuta, to, nan take naka wayar za ta kamu.  Idan kuwa ta kamu ba za ka iya ganewa da wuri ba, musamman idan kadan ne, har sai sun hayayyafa, sun fara tasiri a jikin wayar sannan za ta fara nunawa.

Daga cikin alamomin da ke nuna waya ta kamu da kwayoyin cuta kuwa akwai yawan saibi da nawa wajen kunnawa da kashewa.  Akwai matsalar taskance bayanai. Misali, idan ka zo adana hotuna ko bidiyo a ma’adanar waya ko ma’adanar katin waya, sai a ce maka “Memory is Full,” alhali akwai sauran ma’adana a wayar ko katin wayar; duk wannan na cikin alamomin da ke nuna akwai matsala da babbar manhajar waya sanadiyyar kwayoyin cuta.  Har wa yau, akwai matsalar yawan sandarewa da sumewa (Hanging).  Duk sadda ka ga wayarka na yawan sandarewa ko sumewa idan kana mu’amala da ita, to, ka san akwai matsala mai girma tare da ita.  Musamman idan ya zama ba ka iya kashewa sai ka cire batir sannan take mutuwa.  Har wa yau daga cikin manyan alamu shi ne, waya za ta rika kashe kanta tana kunna kanta.

Duk sadda ka samu haka, to, lallai akwai matsala.  Abu na karshe da zan iya hararowa shi ne hasarar bayanai daga ma’adanar waya ko ma’adanar katin waya.  Ma’ana haka kawai ka nemi bayanan da ka taskance a waya ka rasa.  Wadannan su ne kadan daga cikin matsalolin da ke samuwa idan wayar salula ta kamu da kwayoyin cuta.  Hakan kuma ya fi samuwa ta hanyar musayar bayanai ta amfani da fasahar Bluetooth ko Infra-red ko kuma karbar ma’adanar katin wayar wani ka sa a wayarka.  Sai a rika kiyayewa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.