Hanyoyin da Kafofin Sada Zumunta Ke Samun Kudaden Shiga (3)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 30 ga watan Yuli, 2021.

180

Kamfanin Facebook

Kamar kamfanin Google, kamfanin Facebook ma babbar hajar da yake tallatawa ita ce karban talla daga kamfanoni, da dillacin tallace-tallace ga wasu daga cikin shahararrun mutane a dandalin nasa.  Babbar cibiyar karba da sarrafa tallace-tallace a Dandalin Facebook ita ce manhajar: “Facebook Ad Manager”.  A halin yanzu Dandalin Facebook na da maziyarta da masu rajista sama da biliyan 2.7 a duniya.  Kuma injin dake sarrafa bayanan da masu shafukan Facebook ke wallafa ita ce: “Facebook Algorithm”.  Bayan wadannan magudanan sarrafa bayanai, Dandalin Facebook na da cibiyar gina manhajojin da ake iya amfani dasu a Dandalin, mai suna: “Facebook Developer”.  A wannan mahalli ana baiwa masa gina manhajar kwamfuta da wayar salula ne damar gina manhajo, don bai wa masu ta’ammali a dandalin damar amfani dasu.  Su kansu manhajojin ana tsofa tallace-tallace a cikinsu.

Kamfanin Facebook na da tsarin tallace-tallace kala-kala, ko ince nau’i-nau’i.  Akwai nau’ukan tallar da kamfanin ke tsofawa a tsakanin sakonnin masu shafuka a dandalin.  Ire-iren wadannan sakonni na talla suna dauke ne da  rubutu da kuma hotuna, ko bidiyo.  Kuma a samansu ta bangaren dama, za ka ga an rubuta: “Ad”, kamar yadda kamfanin Google ke yi shi ma.  Bayan wannan, akwai nau’ukan tallar da kamfanin ke sanyawa a cikin manhajojin da mutane ke amfani dasu, musamman mahajojin wasa (Facebook Games).  Sannan akwai nau’in tallar da kamfanoni kance a dora musu su a kan manhajar Facebook ne wayar salula, wato: “Facebook Mobile App”.  Iren-iren wadannan tallace-tallace ba za ka gansu ba idan ka hau Dandalin Facebook ta kwamfuta, ko kayi amfani da manhajar “Browser”.

- Adv -

Daga cikin nau’ukan tallace-tallacen kamfanin Facebook akwai tallar shafi, wato: “Facebook Page Ads”, da kuma “Sponsored Page”.  Wannan nau’in talla ne da Facebook keyi ga shafukan mutane ko kamfanoni.  Misali, idan ka bude shafi don tallata wata haja ko wani mutum shahararre, kuma kana son shafin ya isa ga jama’a da dama dake wani bangare na duniya, sai ka biya Facebook kudi su rika nuna wa mutanen da kake son su gani shafin, ko da kuwa basu matsala alamar “Like” a shafin ba.  Wannan ke sa ka ta cin karo da wasu shafuka (Pages) da baka san masu su ba, amma kaga ana bijiro maka dasu.  Idan ka lura, a kasan sakon dake tallata maka shafin, za ka ga an rubuta: “Sponsored Page”.  Idan ka matsa kaje shafin, kamfanin Facebook zai samu kudi.  Irin wannan talla taimaka wa ‘yan siyasa da masu kananan sana’o’i ko kamfani wajen tallata hajarsu ko dan takararsu cikin kudi kankani.  Domin suna iya maka tallar mako guda, ko wata guda, ko kuma shekara; iya kudinka iya shagalinka.

A daya bangaren kuma, hatta sako da ka rubuta a shafinka, wato: “Facebook Page Post”, kamfanin Facebook na iya tallaka maka shi.  Misali, idan kana son sakonka ya riski wani adadi na mutane dake wani bangaren duniya, idan ka biya kudi, ana iya tallata maka rubutun shi kadai.  Wannan ke sa kaga rubutun wani wanda ba abokinka bane, kuma ba ka da wata alaka dashi, ana bijiro maka.  Ire-iren wadannan sakonni a karkashinsu za ka ga an rubuta: “Recommended Post”.  Da zarar ka matsa wadannan nau’ukan sakonni, za a zarce dakai ne kai tsaye zuwa shafin dake dauke da asalin rubutun.  An ci kudinsa kenan.  Sai wani jikon.

Zuwa karshen shekarar 2020, kamfanin Facebook ya samu kudaden shiga ta hanyar tallace-tallace da ya kai dalar Amurka biliyan 84.16 ($84.16), kwatankwacin naira tiriliyon 34.60 (N34.60 tr) a Nairan Najeriya kenan.  A daya bangaren kuma, kamfanin Facebook ya samu kudaden shiga ta hanyar manhajar WhatsApp a shekarar da ta gabata da ya kai dalar Amurka biliyan 5.5 ($5.5 bil), kwatankwacin naira tiriliyon 2.30 (N2.30 tr) kenan a nairan Najeriya.  A tare da cewa masu karatu ba su ganin wata alamar talla a manhajar WhatsApp da suke amfani da ita a wayar salula, wannan ba ya nufin kamfanin ba ya samun kudaden shiga ta wannan manhaja.  Akwai nau’in WhatsApp mai suna: “WhatsApp Business” wanda mutane ke amfani da ita wajen tallata hajojinsu, da karban kudin cinikayya a tsakaninsu da masu sayan hajojinsu.  Ta wannan hanya kamfanin Facebook na samun kudaden shiga, kamar yadda muka gani.  A halin yanzu akwai masu amfani da manhajar WhatsAppa sama da mutum biliyan 2 a duniya.  Kuma yanzu da kamfanin Facebook ya ayyana cewa zai rika musayar bayanai tsakanin manhajar WhatsApp da ta Facebook, ana sa ran nan gaba kudaden shigan da yake samu daga wannan bangare zai karu sosai.  Domin bayanan da zai rika musayansu za su samar da damammakin samun kudaden shiga ta bangarori da dama.  Duk da cewa ya ambaci a sabuwar kundin ka’idar mu’amala tsakaninsa da masu rajista, sai dai hanyoyin basu takaita ga haka ba.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Hussaini Abba Dambam says

    Masha Allah da wannan shafi

Leave A Reply

Your email address will not be published.