Tasirin Ci Gaban Kimiyya da Fasaha Ga Rayuwa da Zamantakewar Dan Adam a Duniya (5)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 31 ga watan Janairu, 2020.

331

Kundin “DNA” da Kojarin Magance Cututtuka

Bayan hada wancan rumbun bayanan xabi’u da siffofin halittar xan adam da aka yi a baya, nan take malaman kimiyyar a vangaren likitanci da xabi’un xan adam suka shiga dakin bincike don tantance dalilan dake sa wasu iyaye ke gadar da wa ‘ya’yansu cututtukan da suke dasu, musamman cututtuka irin su ciwon siga (Diabetics), da hawan jini mai kaiwa ga ciwon zuciya (High Blood Pressure/Hypertension) da sauransu. Wannan it ace manufar asali da ta sabbaba samar da wani fanni na musamman mai suna: “Genetic Engineering”, wato fannin sauya siffofi da xabi’un halittar xan adam don samar da waraka ga cututtuka marasa jin magani.

Wannan yunkuri ya taimaka sosai wajen gano vangaren qwayar halittar dake dauke da wasu halayya ko siffofi dake iya gadar da cuta daga mahaifi ko mahaifiya zuwa zuri’arsu.  Hakan ya kai ga qoqarin neman hanya ko hanyoyin da za a iya amfani dasu wajen sauya waxannan bayanai masu bayar da siffofi ko dabi’ar dake gadar da cut aga ‘ya’ya.  Da farko dai wannan aiki na sauya waxannan bayanai ya ci tura. Sabo da aiki ne mai dauke da haxari sosai.  Fahimtar yadda waxannan bayanai suke zai taimaka wajen gano haxarin dake tattare da wannan aiki.

- Adv -

Kowane xan adam dai Allah ya halicceshi ne da vangarori guda biyu mahimmai.  Vangaren gangar-jiki da ake iya gani, da kuma vangaren ruhi, wanda har yanzu babu wanda yasan hakikaninsa da yanayin gudanuwarsa sai Allah Mahalicci.  Amma vangaren gangar-jiki Allah ya baiwa xan adam wata qudura ta ilimi da zai iya gano abubuwa da yanayin gudanuwarta.  Wannan yasa muke da likitocin ido, da na makogoro, da na hanta, da na kwakwalwa, da na hakori da dai sauransu.  Amma yadda gangar-jikin kowace halitta – ba ma xan adam kadai ba – ke gudanuwa shi ne, akwai qwayoyin halitta (Cell) masu dinbin yawa dake gudanar da kowane vangaren jikin xan adam.  Misali, a kwakwalwa kadai akwai qwayoyin halitta birjik.  Haka cikin jinin xan adam, da zuciyarsa, da idanunsa da sauran vangarori.  Waxannan qwayoyin halitta su ne ke dauke da hakikanin bayanan yadda dukkan vangaren jikin dan dam ke gudanuwa.  Kuma ba komai bane illa bayanai ne da Allah ya zuba a ciki, waxanda ke baiwa vangarorin jikin xan adam umarnin su kasance yadda Allah ke so su kasance.  Tirkashi!

Misali, kowace qwayar halitta a cikinta akwai vangaren DNA, wanda bayaninsa ya gabatar a kashi na uku.  Wannan bangare ne ke dauke da bayanan yadda vangarorin jikin xan adam ke gudanuwa.  Waxannan bayanai dai kamar wani kundi ne na tsare-tsare da ke baiwa vangarorin jiki umarnin su bayyana ko dabi’antu da wasu siffofi ko halayya.  Misali, qwayar halittar dake lura da launin fatan jikin xan adam na dauke ne da waxannan bayanai.  Idan aka samu isa ga wannan bangare na DNA, za a ci karo da waxannan bayanai da yadda suke bayyana hakikanin launin fatan xan adam. Ka dauka DNA wani littafi ne mai haruffa biliyan shida, kuma mai dauke da babuka daban-daban.  Su kuma qwayoyin xabi’un halitta dake gudanar da rayuwar xan adam (Genes), su ne babukan dake littafin.  Don haka, idan kana son ganin bayanan dake siffata tsayi ko gajartar xan adam, sai kaje babin dake dauke da qwayar dabi’ar halittar dake wannan aiki.  Ba rubutattun bayanai bane irin wanda kake gani a kan takarda.  Wasu bayanai ne da masana kimiyya ke iya fahimtarsu a tsarin da suke, ta amfani da manyan na’urorin kimiyyar hango abubuwa qanana da ido ba ya iya gani.

Don haka, duk abin da aka sauya daga cikin jerin waxannan bayanai dake bayyana ko siffata gudanuwar wani bangare na jikin xan adam, to, nan take yanayin aikinsa zai canza.  Haka idan aka yi kuskuren cirewa ko goge wani vangaren bayani ba yadda ya kamata ba, to, nan ma za a samu matsala mai girma wanda zai iya shafan kusan dukkan jikin xan adam.  Wannan yasa a baya a aikin sauya waxannan bayanai ya zama da tsauri, domin da zarar anyi kuskure, rayuwar xan adam na cikin haxari, in ma bai mutu ba kenan.

A mako mai zuwa in Allah Yaso za mu dubi wani sabon tsari da wasu masana suka gano wanda ke sawwaqe hanyoyin sauya bayanan dake cikin sinadaran xabi’u da siffofin halitta, sannan in da hali mu fara bayani kan tasirin wannan hanya, da irin abubuwan mamaki da al’ajabi da ake sa ran nan gaba zasu samu sanadiyyar buduwar wannan sabuwar kofa ta bincike da aikin kimiyyar halitta da xabi’u.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.