Sakonnin Masu Karatu (2017) (20)

A yau ga mu dauke da wasu daga cikin sakonnin da na samu ta wayar salula da kuma Imel.  Ina kara kira ga masu aiko sakonni cewa a rika hadawa da cikakken suna da kuma adireshi; ko kuwa a ta wayar salula aka aiko.  Nan gaba duk sakon da aka aiko babu cikakken suna ko adireshin mai aikowa, ba za a buga ba.  Da fatan za a kiyaye.

88

Assalamu alaikum Baban Sadik.  Yaya aiki?  Don Allah ta yaya zan iya tallata makaranta ta a Intanet, ta yadda kowa zai ganta?   Allah ya yi maka jagora.  Abba Adam Ja’en

Wa alaikumus salam, Malam Abba Ja’en barka ka dai.  Tallata makarantarka ta Intanet ba abu bane mai wahala idan kabi matakan da suka kamata.  Da farko dai ya kamata ka san cewa akwai hanyoyi da dama da za ka iya amfani dasu wajen yin hakan.  Wadannan hanyoyi dai sun danganci bukatunka ne, da aljihunka, da lokacinka, da kuma ra’ayinka.

Hanyar farko dai, kana iya amfani da shafukan sada zumunta, irin su Facebook da Whatsapp da kuma Twitter, ta amfani da yaren wadanda kake son su sani.  Idan da Hausa ne, ya zama galibin abokanka dake dandalin Hausawa ne ko a kalla suna jin harshen Hausa.  Wannan hanya ba ta da wahala ko kadan; abin da kake bukata shi ne shafi na musamman, da kuma lokacin da za ka zauna don rika yada bayanan da suka shafi makarantarka.

Hanya ta biyu kana iya amfani da gidan yanar sadarwa na kanka, wato ka gina shafi na musamman a Intanet, dauke da bayanai kan abin da makarantar ta kunsa, da tsarin daukan dalibai da kuma nau’ukan darussan da ake koyarwa a makarantar.  Wannan hanya ce mai kyau.

Wadannan kadan ne daga cikin hanyoyin da za ka iya amfani dasu wajen tallata makarantarka a Intanet. Da fatan ka gamsu.


Salamun alaikum Baban Sadik, bayan gaisuwa, shin, wayar GSM za a iya amfani da ita wajen tura sakon Fax?  Kuma wane layi ne a cikin layukan nan yafi inganci wajen tura Fax?   Daga Kabiru Kurnawee Kano

Wa alaikumus salam, Malam Kabiru.  Lallai akwai wayoyin salula da za a iya amfani dasu wajen aikawa da sakon Fax.  Da farko dai, sakon Fax nau’i ne na hanyar aikawa da sakonni ta amfani da siginar rediyo dake jikin na’urorin sadarwa, musamman tarho irin ta da, wa kuma wasu daga cikin wayoyin salula na zamanin yau.   Hakan na yiwuwa ne ta hanyar dora takarda ko wasikar da ake son aikawa da ita, a kan na’urar Fax da a asali ake amfani da ita wajen aikawa da sakon, sai a shigar da lambar wayar wanda zai karbi sako, wato wanda za a aika masa kenan, sannan a tura.  Da zarar an aika, wannan takarda za ta shiga cikin wannan na’ura sannan ta fito ta can baya, tare da sakon shedar aika sako, wato “Acknowledgement Copy” kenan.

A tsarin wayar salula kuma, kana iya saukar da manhajar aikawa da sakon Fax a wayarka mai dauke da babbar manhajar Android ko Ios na kamfanin Apple kenan.  Idan ka bincika, muddin akwai wanda ya dace da nau’in wayarka, nan take za ka gani, sai ka saukar.  Amma wadannan manhajoji na kyauta suna da nakasa, ma’ana bai wuce ka iya aikawa da sako sau daya ko sau biyu a lokaci daya.  Idan kana bukatar wacce za ka iya aika kowane adadin sakonni ne, sai ka sayi manhajar tukun. 

Da fatan ka gamsu da wannan gajeren bayani.


- Adv -

Assalamu alaikum, muna nan biye da Baban Sadik a kowane mako, kuma muna kara mika godiya ta musamman a gareka akan wannan shafi na Kimiyya da Kere-kere.  Fatanmu Allah ya kara tsawon kwana, ya kara maka kwarin gwiwa, amin summa amin.  Daga Abdullahi Bello Anka – 08060809091

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Abdullahi.  Ina godiya matuka , kuma Allah saka da alheri.  Na gode.  Na gode.


Assalamu alaikum, da fatan Baban Sadik yana nan lafiya. Tambayata ita ce: don Allah Malam a taimakeni da hanyoyin da zan bi in fahimci “Programming” cikin sauki.  Na gode.  Daga Iro Manu:  ikhalyl@gmail.com

Wa alaikumus salam, Malam Iro.  Kalmar “Programming” na ishara ne ga iliin gina manhajar kwamfuta ko na wayar salula.  Kamar sauran nau’ukan ilimi, yana bukatar sha’awa, wato ya zama kana son abin a ranka, wannan zai taimaka wajen sa ka sadaukar da lokacinka wajen koyo, tare da hakuri da jajircewa.  Wadannan duk dabi’u ne da dole ka sifatu dasu idan kana bukatar kwarewa a wannan fanni.  Bayan haka, idan baka taba mu’amala da kwamfuta ba, ma’ana baka iya sarrafata ba, dole ne ka fara koyon wannan bangare tukun, kafin kaje bangaren “Programming.”  Domin idan baka san matakin farko ba, ba ka tsallakawa zuwa matakin karshe. 

Ilimin “Programming” ilimi ne mai matukar fadi, da kuma sarkakiya.  Daga cikin abin da ke taimakawa wajen sawwake tsauri da sarkakiyarsa shi ne ya zama kana da matakin farko na ilimin kwamfuta a aikace.  Wato ya zama ka iya sarrafa kwamfuta; wajen kunnawa, da kashewa, da iya sarrafa manhajoji daban-daban a kanta.  Daga cikin abubuwan da suka fi komai mahimmanci wajen koyon ilimin kwamfuta a matakin farko shi ne, ka iya sarrafa kwamfuta wajen rubutu.  Ma’ana ya zama ka iya amfani da kwamfuta wajen rubutu sosai.  Domin duk wani fanni na ilimin kwamfuta da za ka koya ko kware a kansa daga baya, ya ta’allaka ne kan wannan bangare na matakin farko, wato” iya rubutu.

Wadannan kadan ne cikin abin da zan iya rubutawa.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum, dan Allah Baban Sadik ina da tambaya, da fatan za a bani amsarta. Tambayar itace: ina da waya kirar “Infinix Hot 4-Lite.”  Idan ina so in tura wa wani bidiyo yaya zan yi? Ba wai na tura yaje “Home” ba.  Daga Dalibinka Suraj Idriss, kasar Ghana

Wa alaikumus salam, Malam Suraj barka ka dai.  Aikawa da bidiyo ta amfani da wayar salula nau’in “Infinix Hot 4-Lite” na wahala.  Idan kaje manhajar dake dauke da dukkan sakonninka na bidiyo, kana iya latsa wanda kake son aikawa dashi, sai ka latsa ka rike na tsawon dakika daya zuwa biyu, sai ka daga yatsanka.  Da zarar ka daga, za ka ga wayar ta sanya wa bidiyon alamar maki kore, karami.  A can kasa kuma daga bangaren bangaren hagu, za ka ga tambayar yada sakonni mai suna: “Share”.  Kana matsawa za a budo maka hanyoyin da za ka iya aikawa da wannan sako na bidiyo kai tsaye. 

Idan kana da manhajar Imel na Gmail, ko manhajar Whatsapp, ko manhajar sakon tes (Message), ko manhajar Twitter, duk za ka gansu a wurin.  Sai ka zabi manhajar da kake son amfani da ita wajen aikawa da bidiyo din, kai tsaye za a aika.  Sannan za ka ga manhajar fasahar “Bluetooth” a cikinsu; ita ma duk kana iya amfani da ita wajen aikawa da sakon bidiyon din.  Sai dai dole ne ka lura, idan manhajar da ka zabi amfani da ita wajen aika sakon bidiyon tana amfani ne da fasahar Intanet, to a nan kam dole ne ka tabbatar  ka kunna “data” din wayarka, don samun siginar Intanet kafin aikawa da sakon.

Wannan shi ne bayani a gajarce, kan yadda za ka iya amfani da wannan waya wajen aikawa da sakon bidiyo, ta la’akari da irin manhaja ko fasahar dake dauke kan wayarka.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. Hamisu says

    Assalamu Alaikum,dafatan Kana Lafiya Don Allah Meye Aykin Hanta Kahuta Lafiya,daga Hamisu Dake Zaria,hamisuusman757@gmail.Com

Leave A Reply

Your email address will not be published.