Tasirin Ci Gaban Kimiyya da Fasaha Ga Rayuwa da Zamantakewar Dan Adam a Duniya (4)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 24 ga watan Janairu, 2020.

306

Matashiya

A kasidu ukun farko da suka gabata cikin makonni hudu da suka shuxe, idan mai karatu bai mance ba, mun fara yin shimfida ne kan tasirin ci gaban da ake samu a duniyar yau a fannin kimiyya da fasahar sadarwa na zamani da xabi’u, ga ilahirin rayuwar xan adam a duniyar yau.  Mun nuna cewa akwai fanno kamar fannin tsari da xabi’un halittar xan adam, wato: “Genetics”, da fannin kimiyyar sadarwa na zamani, wato: “Information Technology”, da fannin kimiyyar kwakwalwa da halayya da dai sauransu. Ci gaba a waxannan fannoni ne, tare da ci gaban kere-keren na’urorin zamani, suke taka rawa wajen samar da wata sabuwar rayuwa da yanayin zamantakewa a duniyar yau.

Manufar wannan bincike namu dai ita ce, yunkurin gano tasirin waxannan sauye-sauye ga al’adu, da addini, da siyasa da kuma zamantakewar xan adam a ko ina yake a duniya.  Ma’ana, ta la’akari da waxannan sauye-sauye da mai karatu zai karanta a jerin waxannan maqalu da za su biyo baya, wani irin shugabancin siyasa za a samu nan gaba?  Wani irin kalubale ne Malaman addinai, musamman na musulunci, za su fuskanta wajen qoqarin fahimtar wannan sabuwar duniya, tare da samar da fatawowin da za su baiwa sababbin tsare-tsaren nan da hukunci na musamman, wajen halacci, ko haramci, ko wajabci, ko karhanci da dai sauransu?

Muna kuma bibiyar xaya daga cikin masana  a fannin kimiyyar zamantakewa da halayyar rayuwar siyasa ne a duniyar yau, wato: Professor Francis Fukuyama, musamman cikin littafinsa mai suna: “Our Posthuman Future: Consequences of the Biotechnology Revolution,” da wani littafinsa har wa yau mai take: “The Great Disruption: Human Nature and the Reconstitution of Social Order”.  Bayan waxannan littafai, za mu bibiyi sakamakon binciken malaman kimiyyar zamanin yau kan waxannan fannoni da suka kunshi wannan sauye-sauye da ake samu.  Da hirarrakin da ake yi dasu a kafafen yaxa labarai na yau.

Kafin mu ci gaba, zan so mai karatu ya fahimci cewa, dukkan bayanan da zai ci karo dasu a wannan shafi kan waxannan sauye-sauye da ake samu a rayuwa wajen xabi’u da kere-kere da kimiyya, hakaitowa ne zan rika yi, ba wai hukuncin halaccinsu ko haramcinsu a addinin musulunci zan yi ba.  Domin mai karatu zai ji abubuwa ne masu ban al’ajabi, waxanda a zahirin al’adar bahaushe da addininsa, sun saba matuka.  Wasu ma basu yi kama da hankali ba.  Kada mai karatu ya dauka don na yarda da halaccin waxannan sauye-sauye ne yasa na kawo su.  A karshen bayanan zan rika kawo tasirin da waxannan sauye-sauye za su yi ko suke yi a wasu kasashe, wajen canza halayyar xan adam, da siyasar kasashe, da kuma tsarin sadarwa da kimiyyar halitta.

- Adv -

The Human Genome (Rumbun Bayanan Dabi’u da Siffofin Halitta)

Ga wanda ya saba karanta wannan shafi, musamman shekaru kusan takwas da suka gabata, a jerin makalolin da muka kawo masu take: “Tsarin Xabi’u da Siffofin Halitta”, wanda a harshen Turanci ake kira: “Genetics”, mun yi bayani kan cewa tuni malaman kimiyyar halitta na wannan zamani suka kididdige yawan bayanan dake dauke da xabi’u da siffofi da halayyar xan adam gaba xaya, kamar yadda Allah ya samar dasu a cikin qwayar halitta, wato: “Human Cell”.  Wannan bincike mai suna: “The Human Genome Prohect”, wanda aka gama shi kusan shekaru 15 zuwa 20 da suka gabata, ya tantance bayanai sama da biliyan shida dake siffatawa ko bayyana yanayin halitta da dabi’ar xan adam a jikinsa.

Misali, launin qwayar idon xan adam, da launin gashin kansa, da launin fatar jikinsa, da dabi’ar kyauta, ko rowa, ko hakuri, ko juriya ko wadatuwar zuci; duk waxannan halayya da siffofi, bayanai ne da Allah ya zuba su a cikin wannan qwayar halitta, wacce ke dauke dasu kuma take fassara hakikanin xan adam da yadda Allah Ya halicce shi, yayin da yake raye yake gudanar da rayuwarsa.  Daga cikin waxannan bayanai har wa yau kwai waxanda ke kunshe da irin cututtukan da Allah ya tsofa a cikin dabi’ar jini ko jikinsa, wanda kuma yake gadar wa ‘ya’yansa da jikokinsa har zuwa tattaba kunnensa ma.

Babban dalilin samar da wannan rumbun bayanai dai shi ne don fuskantar manyan kalubalen da ke fuskantar rayuwa da lafiyar xan adam, musamman kan cututtukan da suka addabi jinsin bil’adama irin su ciwon sankarar jini, wato: “Sickle Cell Anaemia”, da cutar AIDS, da sauran cututtuka makamantansu da magungunan zamani suka kasa magance su.  Wannan yasa aka fara amfani da hanyoyin kere-kere da kimiyyar zamani wajen samar da na’urorin da ake iya amfani dasu wajen tantance dukkan wani bangare na jikin xan adam dake iya kamuwa da wata cuta kuma har ya harbi wani vangaren jikinsa ko zuriyarsa.

Fahimtar waxannan abubuwa ne zai taimaka wajen samar da hakikanin waraka ga waxannan cututtuka.  Tunda jikin xan adam na gudanuwa ne cikin wani tsari mara misaltuwa.  Allah, wanda shi ne mahaliccin halittu, shi ne kadai wanda yasan hakikanin yadda tsari yake.

A mako mai zuwa za mu tabo bayani kan asalin kudin dake dauke da bayanan xabi’u da siffofin halitta gaba xaya, da yadda masana suka nemo hanyar sauya bayanan dake tafiyar da waxannan halayya cikin sauqi.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.