Hira da Edward Snowden (1)

Shahararren dan jarida Peter Taylor, wanda tsohon ma’aikacin BBC ne, ya samu daman hira da Edward Snowden, matashin nan dan kasar Amurka da ya hankado irin badakalar da ke kunshe shirin cibiyar tsaron kasar amurka na satar bayanan mutane da aiwatar da leken asiri cikin rayuwarsu, da sunan yaki da ta’addanci. Wannan kashi na daya ne.

398

Da yawa cikin masu karatu sun ta turo sako cewa suna son in basu tarihin Edward Snowden, matashin nan dan kasar Amurka, wanda ya hankado shirin hukumar tsaron kasar, wato NSA, na leken asirin bayanan jama’a ta hanyar wayar salula da kwamfuta.  Snowden dai matashi ne dan shekaru 31, kwararre kan ilimin kwamfuta da harkar sadarwa, kuma kafin faruwar wannan al’amari, yana aiki ne da daya daga cikin kamfanonin da hukumar NSA ta dauka suna mata wannan aiki na tatsar bayanan jama’a a boye, ba tare da saninsu ba. 

Bayan tsawon lokaci yana ganin irin wannan badakala da hukuma ke yi wanda hakan ya saba wa dokar kasar Amurka, sai ya nemi iznin tafiya kasar Hong Kong don ganin likita, domin a cewarsa, ba shi da lafiya.  Kafin wannan lokaci daman ya dade yana kwasan wadannan bayanai yana adanawa a matsayin sheda.  Daga nan ya kwashi komatsensa sai kasar Hong Kong, inda ya hadu da ‘yan jaridu daga kamfanonin The Guardian ta kasar Ingila da wasu, ya kuma basu wadannan bayanai da a karshe suka buga a shafukansu.  Wannan lamari ya faru ne cikin shekarar 2013.  Kuma nan take gwamnatin Amurka ta soke fasgo dinsa na tafiya.  A karshe dai kotuna a kasar Amurka sun tabbatar da cewa lallai wannan shiri na NSA haramtaccen shiri ne, kuma nan take aka tsayar dashi.

A halin yanzu Snowden yana gudun hijira a kasar Rasha, inda kwararren dan jarida Peter Taylor, wanda ma’aikacin BBC ne, yayi hira dashi a watan Okotoba na shekarar 2015.  A cikin hirar ne ya bayyana dalilansa da kuma munin da wannan shiri yake tattare dashi.  Na dauki wannan hira da sashen Turanci na BBC suka watsa, na rubuce tare da fassara shi gaba daya, daga farko har karshe.  Duk abin da masu karatu ke bukata kan wannan lamari, yana kunshe cikin wannan hira.  Da farko dai, ga bayani daga Peter Taylor, kan yadda aka yi har ya samu daman hira da Snowden a birnin Mosko.


A cewar masu sukarsa, Edward Sowden ne ke da alhakin tonon silili mafi girma a tarihi, wanda ya shafi bayanan sirrin kasar Amurka da na Burtaniya, wadanda galibi suka samo asali daga rumbun bayanan Hukumar Tsaron Amurka, wato NSA.  A wajen wasu kuma, Snowden wani gwarzo ne wanda ya jawo hankalin al’umma gaba daya zuwa ga gamammen tsarin hukuma na leken asirin da take yi akanmu ba tare da saninmu ba.  Sunana Peter Taylor, kuma shekaruna 35 ina aiki da hukumar BBC a fannin Tsaro da Bayanan Sirri (Intelligence and Security). 

Na san samun hira da Edward Snowden (a yanayin da yake ciki yanzu) wani abu ne mai matukar wahala, amma duk da haka dai nace bari in gwada in gani ko zan dace.  Sai da na dauki tsawon watanni uku ina neman yadda zan iya haduwa dashi.  Tsawon wannan lokaci dai ina ta musayar bayanai ne da wasu ‘yan-tsakani, ta hanyar sakonnin Imel a wani yanayi mai cike da tsaro da kariya.  Ban taba samun damar magana dashi ba kai tsaye.  A karshe dai aka umarceni da inje birnin Masko (Moscow, Russia), in kama daki a Otal, sannan in aike da lambar dakina ga wata lambar wayar salula da aka bani.  Da zarar nayi haka, zai zo ya sameni a inda nake.

- Adv -

Alhamdulillahi!  Aikewa da lambar ke da wuya, sai kawai naji ana kwankwasa mini kofa.  In bude, sai ga shi.  Kwamfa!

A cikin wannan shiri na musamman da na shirya wa BBC,  za ku ji irin hirar da nayi dashi.  Tambayar farko da na masa ita ce:


Peter Taylor: Me yasa kayi abin da kayi?

Snowden:  A duk sadda na samu kaina a zaune a ofishina, ina aiki da hanyoyi da na’urorin leken asirin bayanan jama’a a kullum, sai inga akwai tufka da warwara cikin  zancen jami’an gwamnati kan abin da ya shafi sirrin jama’a da kuma hakikinin abin da ke faruwa (ta bayan fage) a aikace a duniya baki daya.  A nan ba Magana muke yi kan wadanda ake tuhuma da zargin ta’addanci ba.  Kusan dukkan bayananmu da muke aikewa dasu, a kullum ana tatsansu ne, cikin kowane lokaci, ba tare da dalili na zargin aikata mummunan aiki ko ta’addanci ba.  Kuma wannan abu yana faruwa ne ba tare da saninmu ba, ba tare da yardarmu ba, kuma ba tare da wani tsari da hukuma ta samar don sanar da al’umma ba a bangaren shugabanci.  A duk sadda na kalli dokokin kasarmu, sai inga karara, wannan shiri na gwamnati (da ya kunshi satar bayanan jama’a) abu ne haramtacce.  A yayin da na fara tunanin abin da zan iya yi don fadakar da al’ummarmu su ma su san halin da ake ciki, wanda wannan ne zai iya basu damar tofa albarkacin bakinsu cikin lamarin, nakan yi tunanin irin matsalolin da zan iya fuskanta; na rasa aikina, da irin hadarin dake tattare da hakan.  Wannan ba karamin lamari bane.

To amma ana cikin haka, sai kuma naga jami’i mafi girma a bangaren tsaron kasa, wato Daraktan Hukumar Tsaron Kasa, a majalisa, ya daga yatsunsa sama yana rantsuwa akan zai fadi gaskiya, a bainar jama’a a cikin majalisar kasa, ga ‘yan jaridu a gabansa.  Nan take sai wasu daga cikin ‘yan majalisar kasa da suka san hakikanin abin da ke faruwa suka masa tambaya: “Shin, da gaske ne gwamnatin Amurka na satar bayanan miliyoyin daruruwan Amurkawa ta hanyar leken asiri ba tare da saninsu ba?”  Sai yace: “Sam ko kadan!”  Alhali abin da ya fada ba gaskiya bane.

Ni kaina akwai wata dama ta musamman da aka bani mai take: “Priv Ac”, wato: “Privilege Access,” wadda ke baiwa gama-garin mutane damar neman iznin ta’ammali da wadannan bayanai (da muke tatsa).  Ina iya mu’amala da dukkan bayanan, sanadiyyar yanayin aikina.  Kuma sun kunshi nau’ukan bayanai daga gwamnatin Burtaniya…

- Adv -

You might also like
1 Comment
  1. yahya Garba Al-yolawi says

    Masha Allah. Allah ya saka da alheri

Leave A Reply

Your email address will not be published.