Ka’idojin Mu’amala da “Password” (8)

Ga kashi na takwas cikin jerin kasidun dake nazari kan “Kalmar Sirri”, wato “Password” da mahimmancinsa ga mai mu’amala a shafin Intanet. A sha karatu lafiya.

103

Makon Jiya

A makon jiya masu karatu sun ga bayanai kan wasu daga cikin hanyoyin da ‘Yan Dandatsa ke bi don satar “Password” wadanda, kamar yadda na sanar a makon, hanyoyi ne na gama-gari.  Abin da wannan ke nufi kuwa shi ne, ba su bukatar wata kwarewa ta musamman.  Da kirdado, da tunani, da tsabar naci, da leke ko hangen abin da mai shigar wa da “Password” ke shigarwa, duk hanyoyi ne masu sauki da barayin “Password” ke bi wajen sacewa.  A yau cikin yardar Allah za mu ci gaba da bayani kan ragowar hanyoyin da suke bi, amma wadanda ke bukatar kwarewa ta musamman, ba kamar wadanda suka gabata ba.  Mu je zuwa, wai mahaukaci ya hau kura:

Amfani da Na’urar “Wi-Fi”

Daga cikin hanyoyin mu’amala da fasahar Intanet ta amfani da wayar salula ko kwamfuta ko sauran na’urorin sadarwa (irin su iPad da sauransu), akwai na’urar Wi-Fi.  Wannan na’urar aikinta shi ne yada yanayin sadarwa a iya kadadar sadarwar da aka kera ta akai.  Akwai wadda ke iya mamaye unguwa guda.  Akwai mai iya mamaye iya hekta guda.  Akwai mai iya mamaye iya fadin gida da harabarsa.  Akwai mai iya mamaye iya dakunan dake madaidaicin gida guda.  Akwai wanda kuma a iya falo ko dakin kwana kawai take iya yada yanayin sadarwar.  Suna nan kala-kala.

Idan aka girke wannan na’ura a wuri, ana iya jona dukkan na’urorin sadarwar da ake dasu a wurin.  Misali, idan a gidanka kana da kwamfuta guda daya, matanka uku kowacce na da wayar salula guda daya, ‘ya’yanka biyar kowannensu na da kwamfutarsa guda daya, sannan ga taka wayar salular; duk kana iya jona su a jikin wannan na’ura don aiwatar da sadarwa a tsakanin dukkan na’urorin.  Hakan zai yiwu ne idan aka mayar da daya daga cikin kwamfutocin ta zama Uwar garke, wato “Server” kenan.  A tsakanin wannan Uwar garke dole ne a samu wata na’ura mai suna “Router,” wacce aikinta shi ne dillancin hada alaka tsakanin uwar garken da sauran na’urorin dake wannan zango na sadarwa.  Na’urar Router ce za ta baiwa kowace na’ura (kwamfuta ce ko wayar salula) dake makale a zangon lambobi na musamman masu suna: IP Address.

Da zarar ka kayi kokarin aiwatar da sadarwa tsakanin wayarka ko kwamfutarka a wannan gida ta amfani da wannan na’ura ta Wi-Fi, nan take za a tantance wayarka ta cikin na’urar Router, ta zarce ta Uwar garke, sannan ka shiga Intanet.  Haka abin yake.

- Adv -

Inda masu satar “Password” ke shigowa shi ne wajen na’urar Router.  Na’urar Router ce ke iya gani da sanin bayanan da dukkan na’urorin sadarwar ke karba ko aikawa a wannan Zango, domin ta cikinta suke bi tana tantance su kafin hakan ya faru.  A ka’idar sadarwa kuwa, duk na’urar dake jone a wannan zangon sadarwa, wacce ke amfani da na’urar Wi-Fi don shiga Intanet ta hanyar bin Router da Uwar garke, idan aka yi amfani da wata manhaja ko masarrafa ta musamman, za su iya ganin hakikanin bayanan da wayarka ko kwamfutarka ke karba ko aikawata tsakaninta da shafin da kake mu’amala ko nazari a cikinsu a lokacin da kake yi.

Manhajar “Wi-Fi Sniffer” manhaja ce da ake amfani da ita wajen iya hangowa ko ganin irin bayanan da na’urorin sadarwa ke aikawa ko karba a tsakaninsu da wasu na’urorin dake wata uwa duniya.  Idan aka yi rashin sa’a wanda ke lura da wannan Zango na sadarwa bai sanya matakan tsaro ta hanyar hana kowace na’ura iya jonuwa da zangon sai da izini ba, to, barawon “Password” na iya zuwa da na’urarsa mai dauke da manhajar “Wi-Fi Sniffer” don jonuwa da zangon sadarwar, tare da tace dukkan bayanan da na’urorin ke aikawa ko karba a tsakaninsu.  Bayanan kuwa sun hada da: adireshin shafukan da suke shiga ko suka shiga a baya, da suna (username) da kalmar izinin shiga (password), da adireshin Imel, da kalmomin sirrin wayar salular da ake amfani da ita wajen wannan sadarwar da dai sauran bayanai.

Ire-iren wuraren da ake iya samun zangon sadarwa ta na’urar Wi-Fi dai suna da yawa.  Galibi wurare ne da mutane ke yawan taruwa don jira ko aiwatar da wani abu.  Misali, kamar dakin jira a filayen jirgin sama, da dakunan shan shayi a galibin kasashen nahiyar Turai da Amurka (Coffee Café), da wurare na musamman da hukuma ko wani kamfanin sadarwa ke kebancewa don fa’idar jama’a (misali, irin su Millennium Park dake birnin Abuja), da makarantu, da filayen kwallon kafa da dai sauransu.  A wadannan wurare ba a sanya matakan tsaro a na’urorin dake sadar da wayoyi ko kwamfutoci masu jonuwa da zangon sadarwar.  Domin wuri ne budadde; kowa yazo ya shiga.  Hadarin dake ciki kuma kai kasan yadda za ka kare kanka.  Don haka idan ka samu kanka a wuri irin wannan, sai kasan yadda za kayi taku.  Bayanai kan yadda za kare kai daga barayin “Password” na nan tafe.

Amsar “Tambayar Sirri”

Hanyar satar “Password” ta amfani da Amsar Tambayar Sirri (Security Question Answer) galibi takan shafi wadanda aka sace musu “Password” dinsu ne, har aka zuba a Intanet wani ya sace, ko kuma wanda ya sace ta hanyar “Zamba cikin aminci” da bayaninsa ya gabata.  Idan barawon kwararre ne, a ka’ida yakan yi nazarin mahallin da ya samu shiga da “Password” din da ya sace ne.  Idan akwatin Imel ne misali, akwai Tambayoyin Sirri (Security Question) da mai shafin yayi wa kansa kuma ya bayar da amsar.  Dukkan amsoshin da ya bayar ana iya ganinsu ware-wake idan aka shiga bangaren tsare-tsaren akwatin Imel din, wato: Settings.  Idan barawon yasan wadannan amsoshi, to, ko daga baya ka canza “Password” dinka, yana iya kokarin iya sake shiga, idan aka ce masa an canza “Password” din, zai nemi ya sake canzawa.

A yayin da yazo wajen canzawa kawai za a tambaye shi amsoshin wadancan tambayoyin sirri ne, kuma ya sani.  Da zarar ya amsa tambayoyin shikenan, sai a bashi damar sake canza “Password” din.  Ka ga shafinka ya rasa ‘yancinsa kenan.  Ga ka da gida, amma wani yana rike da mabudin gidan, kuma barawo ne, kuma baka sanshi ba.  Duk da cewa a halin yanzu shafukan Imel dake Intanet sun daina amfani da wannan kalma ta amsoshin tambayar sirri ita kadai, musamman kamfanin Google a manhajarsa ta Gmail.  Amma kada mai karatu ya sake, a rika canza “Password” lokaci zuwa lokaci.  Akwai masu “Password” din da tun budewa shafinsu basu taba canzawa ba.  Wannan kuskure ne mai girman gaske.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.