Sakonnin Masu Karatu (2019) (4)

Hanyoyin Kwarewa a Fannin "Networking"

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Fabrairu, 2019.

133

Assalamu alaikum.  Don Allah nima ina son a aiko mini cikakken bayani a kan Tsibirin Bermuda da tekunan dake zagaye dashi ta: abbansix78@gmail.com.  Khalid Tukur.

Wa alaikumus salam, Malam Khalid barka dai.  Bayani kan wadannan wurare da ka ambata ya riga ya gabata, ba sau daya ba, ba ma sau biyu ba, a wannan shafi mai albarka.  Kamar yadda na fada a baya, babu kasidar da ta shahara fiye wacce na rubuta kan tsibirin bamuda.  A halin yanzu na taskance wadannan kasidu a cikin shafin Intanet na musamman da na tanada.  Don haka, sai a garzaya can don samun damar karanta wannan kasida.  Ga adireshin da zai kaika kai tsaye zuwa fannin dake dauke da kasidar ko kadisun nan: https://babansadik.com/category/teku.  Allah sa a dace, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kai da Sadik duk kuna cikin koshin lafiya Amin.  Tambayata itace: don Allah yaya ake dauko bidiyo a bangaren Utube; domin nayi kokarin daukowa amma na kasa.  Allah ya kara basira, fahimta, ilimi, amin.

Wa alaikumus salam, barka dai.  Da fatan ana lafiya.  Yadda ake dauke sakon bidiyo daga Youtube zuwa kan wayar salula, a farko abu ne mai wahala, ko ince ba ya yiwuwa.  Amma da tafiya tayi nisa sai aka samu manhaja ta musamman, wacce ke baka damar saukar da duk bidiyon da kake bukata daga shafin Youtube zuwa kan wayarka, ka iya kallo ko sauraro a duk sadda kaga dama, ko da kuwa babu Intanet a wayarka, wato: “Offline” kenan.

- Adv -

Kamfanoni ko mutane da dama sun gina manhajojin wayar salula da dama dake taimakawa wajen yin hakan.  Amma wanda nake amfani da ita cikin sauki, ita ce wadda kamfanin Google, mamallakin shafin Youtube, ya gina da kansa, don baiwa masu kallo damar saukar da bidiyon da ya burge su.  Wannan manhaja na iya amfani da bidiyon dake shafin cikin yanayi mai sauki, kuma ko da ba ka da “data” mai yawa, hakan bazai zama matsala ba.  Idan kana bukata kaje cibiyar “Play Store” ka nemi wannan manhaja mai suna: “Youtube Go”.  Allah sa a dace, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik, da fatan kana lafiya.  Don Allah wasu hanyoyi zan bi domin zama kwararre a fannin “Networking”?  Da fatan zan samu kyakyawar amsa.  Na gode.  Daga Adda’u Yahaya Tsangaya.

Wa alaikumus salam, Malam Adda’u barka dai.  Hanyoyin zama kwararre a fannin “Networking” bai wuce zuwa makaranta ta kwarewa a fannin.  Fannin “Networking” dai yana da matakai da dama, da kuma nau’ukan fannoni da dama.  Amma a takaice, akwai matakai biyu shahararru wanda kamfanin Cisco dake kasar Amurka ke bayar da takardun sheda a kansu idan aka koye su daga makarantu ko cibiyoyin dake da rajista dasu.

Matakin farko shi ne: “Certified Cisco Networking Associate”, wato: “CCNA” kenan.  Wannan a matakin Difloma ake mallakarsa.  Hatta cibiyar karantar da ilimin kwamfuta na jami’ar Bayero dake Kano, tana karantar da wannan fanni a wannan mataki.  Mataki na biyu kuma shi ne: “Certified Cisco Networking Professional”, wato:  “CCNP”.  Wannan shi ne mataki na sama, a kan na farko da bayaninsa ya tabbata.  Kuma da zarar ka gama samun horarwa, sai a maka rajista da asalin cibiyar Cisco dake kasar Amurka, da baka damar rubuta jarabawar kwarewa, wato: “Certification” kenan.  Da wannan takardar sheda, duk ma’aikata ko hukumar dake neman kwararre a wannan fanni za ta kalleka, kuma ta dauke ka, in Allah Yaso.

Bayan jami’ar Bayero dake karantar da wannan fanni, akwai cibiyoyin karantar ilimin kwamfuta irin su APTECH, da NIIT, su ma suna karantarwa, tare da shirya maka jarabawar kwarewa ta karshe.  Na kuma tabbata duk akwai su a birnin Kano, da Abuja, da Legas, da Fatakwal, da Kaduna.  Allah sa a dace, ya kuma ba da ilimi mai amfani, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.