Hira da BBC Hausa kan Bikin Ranar Tsaftace Intanet a Duniya (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 14 ga watan Fabrairu, 2020.

200

Sabanin yadda muka saba kwararo bayanai kan maudu’in da muke Magana a kai na tasirin ci gaban kimiyya da fasahar sadarwa kan rayuwa da dabi’u da addinin jinsin dan adam a duniya, a yau ina tafe ne da wani guzuri da na mana daga zauren gabatar da shirye-shirye na sashin Hausa na BBC dake nan Abuja.  Wannan hira ce da aka yi da ni don fito da mahimmancin ranar bikin Tsaftace Fasahar Intanet, wato: “World Safer-Internet Day”, na shekarar 2020, wanda ake gudanarwa a duk sanar 11 ga watan Fabrairun kowace shekara.  Manufar samar da wannan rana dai shi ne don wayar da kan jama’a kan hadarori da matsalolin da ke tattare da fasahar Intanet, tare da samar da hanyoyin kariya musamman ga kananan yara da matasa.

Sashen Hausa na BBC dake nan Abuja, kamar yadda ya saba, ya gayyaceni don hira ta musamman kan mahimmancin wannan rana, da kuma shawarwari ga iyaye, da matasa da dukkan masu ruwa da tsaki wajen mu’amala a fasahar Intanet.  An sanya wannan hira ne a shirin rana (karfe 3 na yamma) na ranar litinin, 10 ga watan Fabrairu.  Kasancewar ba dukkan hiran ake sanyawa ba saboda karancin lokaci, naga dacewar rubuce hirar baki dayanta, don baiwa masu karatu musamman wadanda basu saurari shirin ba, damar amfana da abubuwan da hirar ta kunsa.  A sha karatu lafiya.

———-

BBC Hausa: To, da farko zamu so muji me wannan rana ta kunsa, da kuma mahimmancinta?

Baban Sadik: Wannan rana ta “World Safer-Internet Day” dai, kamar yadda aka ji sunan ko taken a turance, rana ce da ake kokarin wayar da kan jama’a don samar da mahallin Intanet tsaftatacce a ilahirin duniyar Intanet baki daya, ta yadda zai zama duk wanda ke mu’amala ko ta’ammali da wannan fasaha ya yi mu’amala da ita ba tare da wani cutarwa ba; yana mai samun bayanan da yake bukata, ta hanyoyin da yake bukata.  Mahimmancin wannan rana dai zai bayyana mana ne idan muka yi la’akari da cewa samun mahalli mai dauke da lumana a Intanet shi ne zai taimaka wa dukkan wani mai gudanar da kasuwanci ko binciken ilimi ko karatu ta hanyar zai samu damar yin hakan ba tare da fuskantar wata cutarwa ba ko wata fargaba.

- Adv -

BBC Hausa:  Kamar wasu matakai kake ganin iyaye ko ‘yan uwa za su rika bibiyar shafukan da ‘ya’yansu ko kuma wadanda suke karkashinsu suke ziyarta musamman ta la’akari da shafukan da basu kamata ba a wannan zamani?

Baban Sadik:  Wato iyaye ko ‘yan uwa su bibiyi ‘ya’yansu ko ‘yan uwansu misali, don tabbatar da cewa basu afka cikin matsala a wannan mahalli ba, abu ne mai wahala matuka, a tare da cewa abu ne mai yiwuwa.  Idan muka yi lura, a yau galibin kayayyaki da hanyoyin sadarwa na zamani da wayoyin salula suna zuwa ne da wani bangare da ake kira: “Parental Control”.  Wannan bangare na “Parental Control” an samar dashi ne a na’urorin sadarwa don bai wa iyaye damar aiwatar da wani aiki da malaman fasahar sadarwa da aikin jarida ke kira da suna: “Gatekeeping”.  Shi tsarin “Gatekeeping” shi ne, ya zamanto a matsayinka na uba, ko uwa, ko malami, ko kuma mai tarbiyya, ka iya tantance hanyoyin da wanda kake tarbiyya ko lura dashi zai iya cutuwa daga gare su, da tanadar hanyoyin kariya gare shi ba tare da hakan ya hana shi mallakar abin da yake bukata ba ko kasancewa a wani mahalli ba, muddin lalura ta kama ya kasance a mahallin ko ya mallaki abin.

Wannan tsari na “Gatekeeping” yana da mahimmanci matuka, kuma aiwatar dashi abu ne mai sauki a galibin kasashe da suka ci gaba.  Domin kwamfutocin sun yawaita, kuma ‘ya’yansu na amfani dasu ne galibi ko dai a gidajen wasan kwamfuta (Computer Game Centers) ko kuma a gidajensu.  Inda ma ta hanyar wayoyin salula ne, suna da hanyoyi da dama da suke iya bibiyarsu don tabbatar da abinda suke ciki.  Amma a nan, wato a kasashe masu tasowa, musamman mahalli kamar Najeriya ko arewacin Najeriya, za ka samu da yawa cikin yara da matasa suna amfani da wayoyin salula ne musamman wajen ma’amala da fasahar Intanet.  Kuma kokarin tantance wani shafi ko shafuka yaro ke shiga, yana bukatar sai ka dauki wayar ka rike, ka dudduba lokaci-lokaci, musamman.  Idan kuma yana goge shafukan da yake shiga, ka ga akwai matsala (gane hakan zai yi wahala).

Don haka, hanya mafi sauki ita ce, iyaye suyi kokarin ilimantar da ‘ya’yansu kan munanan hanyoyin da wannan fasaha ta Intanet ta kunsa.  Akwai abubuwa da dama da suke miyagu ne; kamar dai rayuwar da muka saba yi ne a Zahiri.  Idan ba ka da ilimi kan (munin) abu, za ka iya fadawa cikin matsala.  Don haka abu na farko dai shi ne fadakar dasu cewa akwai abubuwa masu hadari a wannan mahalli.  In so samu ne ma suna iya bayyana musu hakikanin wadanna wurare (idan sun sansu kenan), su rika musu lacca sosai lokaci-lokaci.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.