Sakonnin Masu Karatu (2019) (6)

Hanyoyin Kwarewa a Fannin "Cyber Security"

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Maris, 2019.

237

Assalamu alaikum Baban Sadik, don Allah shawara nake nema da karin haske akan karatu a fannin “Cyber Security” da kuma damammakin aiki da yake dasu.  Saboda na samu gurbin karatu ne a mataki na biyu a Jami’ar Bayero, Kano.  Daga dalibinka Shamsu S. Maidawa, Malumfashi.  Nagode.   Shamsusmaidawa@gmail.com.

Wa alaikumus salam, Malam Shamsu barka ka dai, kuma ina maka fatan alheri.  Yadda ka fara lafiya, Allah s aka gama lafiya, ka samu fitowa da sakamako mai kyau wanda zai amfaneka da al’umma baki daya, amin.  Hakika nakan yi farin ciki a duk sadda naga matasa na samun gurabe don karantar da fannoni irin wadannan, wanda a duk duniya yanzu dasu ake tinkaho.  Ina son sanar dakai cewa, shekaru sama da goma da bayyanar wannan shafi, ya zaburar da matasa da dama wadanda suka nuna kansu na sansu, kan karantar ilimi da kwarewa a fagage masu alaka da kimiyyar fasahar sadarwa na zamani.  Kai ma ina maka barka da zuwa wannan fage.

Dangane da tambayarka cewa wasu damammaki ne wannan fanni na “Cyber Security” yake dauke dasu kan batun aiki kenan, bayan an kware.  To, da farko dai wannan fanni na “Cyber Security”, kamar yadda ka sani, fannin da ke karantar da dalibai hanyoyin kare bayanai ta hanyar kayayyaki da na’urorin sadarwa a Intanet.  Ma’ana, yadda sojojin kasa da na ruwa da sama ke kare kasa a zahirin rayuwa, inda ido ke ganin ido, wannan na bayar da kariya ne a giza-gizan sadarwa na duniya.  Shi yasa kalmar “Cyber” tazo cikin sunan fannin. Sabanin zamanin baya da galibin hanyoyin tsaro na zahiri ne kadai ake la’akari da kuma tanadi gare su don kare dukiya da rayuwar al’umma, a yanzu yaki ya koma giza-gizan sadarwa na duniya.  Yadda ake kai hari ta teku, ko sararin samaniya, ko bodar wata kasa, haka ake kai ma kasashe hari a yanzu ta hanyar Intanet.  To, wannan fanni na karantar da masu koyonsa ne yadda ake kare kwamfutoci, da wayoyin salula, da bayanai na mutane ko na hukuma, da kwamfutocin dake dauke da manhajojin dake sarrafa wasu kayayyakin sadarwar da kasar ke amfani dasu.

Shekaru kusan shida da suka gabata na gabatar da kasida da aka buga a wannan shafi mai albarka, mai take: “Dandatsanci: Wani Sabon Salon Yaki Tsakanin Kasashe a Duniya”, inda na zayyana ire-iren hare-haren da kasashe ke kai wa wasu kasashe da suke zaman doya da manja dasu, ta hanyar Intanet.  Na kuma nuna cewa babu wata kasa da ta kubuta daga irin wannan aiki, domin ya zama ruwan dare, gama duniya.  Wadanda ake jin nasu kawai su ne kasashen Amurka da Sin, da Koriya ta Arewa, da Isra’ila da Iran; kowacce na zargin ‘yar uwarta cewa ta kai mata hari na dandantsanci ga wasu kwamfutocin dake dauke da bayanan kasarta.  Wasu kan yi haka ne ta amfani da kwararrun da suka tanada, wasu kasashen kuma suna yin hakan ne ta hanyar sojan gona.  Akwai ‘yan Dandatsa na haya da dama dake zauna, suna jiran wanda zai yi hayansu ne kawai su masa aiki ya biya su.  Don haka, a wanann fanni na “Cyber Security”, za a koya maka yadda za ka kalubalanci ire-iren wadannan nau’ukan ayyukan ta’addanci ne dake yaduwa a Intanet.  Sai dai sabanin yadda misalai na suka rinjayar, wannan fanni bai takaitu ga hukumomin kasashe kadai ba, hatta manyan kamfanonin kasuwanci da na sadarwa – irin su tarho da kwamfuta da saye-saye da sayarwa – duk suna da bukatuwa zuwa ga masu kwarewa a wannan fanni.

- Adv -

Don haka, idan har ka kware a wannan fanni, hukumomin tsaron Najeriya na iya daukanka aiki, domin a halin yanzu ma hukumar sojin kasan Najieriya ta kaddamar da cibiyar tsaron kasa ta hanyar giza-gizan sadarwa a shekarar da ta gabata, don bibiyar hanyoyin da kasarmu ke samun barazana a wannan bangare.  Bayan haka, hukumar yaki da ta’ammali da kudaden haram ta kasa wacce aka fi sani da “Economic and Financial Crimes Commission”, ko EFCC a gajarce, tana iya daukanka aiki.  Domin hukumar na da cibiya ko sashe na musamman dake lura da kafafofin sadarwa na zamani wajen aiwatar da laifukan da suka shafi sace kudade da wasu ke yi.  Har wa yau, hukumar ‘yan sanda ma na da bukatuwa ga wannan ilimi, da sauran hukumomin tsaro irin su Kwastam, da Magireshon, da ICPC, da babban bankin Najeriya, wato CBN, duk suna daukan kwararru a wannan fanni.

A daya bangaren kuma, zamani ya canza sosai, ba wai sai hukumomin gwamnati ba kadai, akwai kamfanoni masu zaman kansu, wadanda ke ta’ammali da bayanai masi dimbin yawa, kamar kamfanonin sadarwar wayar salula, irin su: MTN, da 9Mobile, da Airtel, da Glo, duk suna daukan masu kwarewa a wannan fanni sosai.  Idan muka koma bangaren kamfanonin kasuwanci ma haka abin yake.  Ba nan kadai ba, idan Allah yasa ka dace, har kasashen waje kana iya samun aiki, musamman a manyan kamfanonin sadarwa na duniya masu rassa a Najeriya, irin su Google, da Microsoft, da IBM da sauransu, duk suna iya daukanka aiki.

Shawarar da zan baka a nan ita ce, idan Allah yasa ka gama lafiya ko kuma kafin ka kamala karatun, kayi kokari ka kware a daya daga cikin fannonin gina manhajar kwamfuta, irin su Java, ko Python, ko JavaScript da CSS da HTML, ko kuma wani ilimi dake da alaka da wadannan.  Wannan zai taimaka maka matuka wajen sanin aiki cikin sauki.

A karshe ina maka fatan alheri da gamawa lafiya.  Allah maka jagora, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.