Alakar Wayar Salula da Sauran Kayayyakin Sadarwa

Kashi na 21 cikin jerin kasidun dake nazari na musamman kan wayar salula da dukkan abin da ya shafeta. A sha karatu lafiya.

168

Matashiya

A baya mun kwararo bayanai kan abin da ya shafi Ayyukan Wayar Salula; wato dukkan abin da wayar salula za ta iya maka na aiki ko hidima wajen taskance bayanai, ko yin kira, ko karbar kira, ko karbar bayanai na bidiyo ko hotuna daskararru ko sauti da dai sauransu.  Dukkan wadannan kasidu suna cikin jerin bayanan da muke ta kawowa ne kan abin da ya shafi wayar salula gaba dayanta, tun shekarar da ta gabata.  Bayanan suna zuwa ne, kuma za su ci gaba da zuwa kan tsarin wayar salula, da yanayin sadarwa, da ruhinta, da manhajojinta, da masarrafanta, da tsarin gudanarwarta, da nau’ukanta, da kamfanonin kera wayoyin salula, da ayyukan wayar salula, da alakarta da sauran kayayyakin sadarwa, da matsalolin wayar salula, da tasirin wayar salula cikin al’umma da daidaikun mutane, da kuma tasirinta wajen canza dabi’a – zuwa gyara ko barna – da dai sauransu.

A yau za mu ci gaba da kawo ire-iren wadannan bayanai, inda za mu yi bayani kan Alakar Wayar Salula da Sauran Kayayyakin Sadarwa.  Kasidarmu ta yau za ta kasu ne zuwa kashi uku: na farko kan Tsarin Sadarwa da ke taimakawa wajen hada alakar, na biyu kan Hanyoyin Sadarwa da ake da su a wayar salula, na ukun kuma shi ne kayayyakin da ke sawwake sadarwar a tsakaninta da sauran kayayyakin sadarwa.

Wayar salula na iya aiwatar da sadarwa a tsakaninta da ‘yar uwarta.  Tana iya aiwatar da sadarwa tsakaninta da kwamfuta, da talabijin, da na’urar dabba’a bayanai, wato Printer, sannan tana iya aiwatar da sadarwa a tsakaninta da duk wata na’urar sadarwa mai tsarin aikawa da karban bayanai irin nata.

Tsarin Sadarwa

Tsarin sadarwa a wayar salula ya kasu kashi biyu ne; ma’ana tsarin da ke sawwakewa ko haddasa sadarwa tsakaninta da sauran kayayyakin sadarwa. Ba wai wayar salula kadai ba, duk wata na’urar sadarwa mai iya mu’amala da wata na’urar na yin haka ne ita ma ta hanyoyi guda biyu.  Hanya ta farko ita ce ta hanyar masarrafar da ke ruhinta.  Wadannan masarrafai masu sawwake sadarwa a tsakanin na’urar sadarwa da wata na’urar, su ake kira Drivers.  Ba su da wani aiki sai hada alaka a tsakanin na’ura da duk wata na’urar da ke kokarin neman bayanai daga gare ta.

Misali, idan kana bukatar karbar bayanai daga wayar salular wani abokinka ta hanyar tsarin Bluetooth, da zarar ya kunna wayarsa don neman wayarka kafin alaka ta kasance, wadannan masarrafai masu suna Bluetooth Drivers ne za su aiwatar da wannan aiki mai muhimmanci.  Su ne za su nemo wayarka, su baiwa wayarsa daman “Magana” ko “zance” da wayarka, ta hanyar kafofin sadarwa da za su bude, sannan idan sun tabbatar da tsari da shirin wayarka wajen karba, sai wayarsa ta yi yunkurin turo maka su nan take.  Kai kuma a naka bangaren, wadannan masarrafai ne za su taimaka wajen karban bakoncin wayar abokinka, da amincewa wajen aiwatar da sadarwa, daga nan sai ka karbi bayanan.  Dukkan wadannan masarrafai ido ba ya ganinsu, sai dai ya ga aikin da suke yi, a yayin da suke aikin.

Hanya ta biyu ita ce ta hanyar sadarwar gangar-jiki.  Wannan shi ya kunshi duk wani abin da za a makala a jikin wayarka, don zukowa ko debo bayanai zuwa wata na’ura ko ma’adanar bayanai.  Wannan hanya dai a bayyane take, ido na iya ganinta.  Kuma duk sadda ka sayi sabuwar wayar salula, tana zuwa ne da kayayyakin da ke sawwake aiwatar da irin wannan sadarwa.  Ma’ana za ka ga wata waya ‘yar gajeriya, mai kai biyu.  Haka idan ka dubi wayar salularka za ka ga tana dauke ne da wasu kafofin sadarwa a gindinta, ko a gejen jikinta, ko a samanta, inda za ka iya makala wanann waya don aiwatar da sadarwa.

Wani abin da ya kamata mai karatu ya sani shi ne, wannan tsarin sadarwa ba ya yiwuwa sai da taimakon tsarin farko.  Ma’ana, duk sadda ka makala wa wayar salularka wayar sadarwa don debo bayanai, sai wadancan masarrafai sun dasa kansu a cikin na’urar da aka jona mata wayar, sun zauna daran-dakam, sannan sadarwa ya yiwu.  Wadannan hanyoyi su ne hanyoyin guda biyu, a takaice.

Hanyoyin Sadarwa

- Adv -

Hanyoyin da ke taimaka wa wayar salula ta aiwatar da sadarwa sun kasu kashi uku ne.  Wadannan hanyoyi suna girke ne cikin tsarin sadarwa nau’i biyu. Da tsarin sadarwa ta wayar iska (Wireless Communication), da kuma tsarin sadarwa ta gangar-jiki, wanda mai mu’amala da wayar ke iya yi ta hanyar jona wayar da wata na’ura ko wani abin da ke wakilatar na’urar.

Hanyar sadarwa ta farko ita ce ta amfani da fasahar Bluetooth, wato tsarin aikawa da sakonni tsakanin wayar salula da wasu kayayyaki ko na’urorin sadarwa ko ma’adanar bayanai masu dauke da wannan fasaha, ta amfani da yanayin sadarwa ta wayar iska.  Bayani kan wannan tsari ya sha bayyana a wannan shafi a baya.  Kuma na san da yawa cikinmu duk mun iya amfani da wannan tsarin sadarwa ta fasahar Bluetooth.  Illa abin da mai karatu zai so sani shi ne, ba wayoyin salula bane kadai ke dauke da wannan fasaha ta Bluetooth, akwai talabijin masu dauke da fasahar Bluetooth, da rediyoyin zamani masu dauke da fasahar Bluetooth, da na’urar dabba’a bayanai (wato Printer) masu dauke da fasahar Bluetooth, da na’urorin motoci masu dauke da fasahar Bluetooth, da na’urar dumama abinci (wato Microwave) masu dauke da fasahar Bluetooth, ga kuma na’urar kwamfuta, wacce ita ma a halin yanzu ke zuwa da wannan fasaha ta Bluetooth, da dai sauran na’urorin sadarwa ko mika bayanai.  Wannan hanya ta farko kenan.  Da wayar salularka, kana iya mu’amala da kowace na’ura ce, ko ma’adanar bayanai, muddin akwai wannan fasaha ta Bluetooth a tare da ita.

Hanyar sadarwa ta biyu ita ce ta amfani da fasahar Infra-red, wanda shi ma bayani ya gabata a kansa tun shekaru biyu da suka wuce.  Bayan haka, wannan fasaha ta Infra-red an kusan daina yayinta ma yanzu. To amma duk da haka, daya ce daga cikin hanyoyin da ake amfani da su wajen aikawa da karbar sakonni ta hanyar wayar salula da dukkan wata na’ura mai dauke da fasahar.  Da wannan tsari na Infra-red da na Bluetooth, duk suna amfani ne da tsarin sadarwa ta wayar iska.

Sai hanya ta uku, wacce ake amfani da wayar Universal Serial Bus (USB Cable).  Wannan ita ce wayar da ke zuwa cikin jerin kayayyakin da wayoyin salula ke zuwa da su sababbi.  Wannan waya dai tana dauke ne da kai biyu; da bangaren da ake jona wa wayar, da kuma bangaren da ake jona wa kwamfuta ko duk wata na’ura mai dauke da ramin aika bayanai na USB.  Da wannan hanya za ka iya aikawa da bayanai daga wayar salularka zuwa kwamfutarka; hotuna ne, ko sauti, ko bidiyo. Wannan waya ta USB Cable tana da fa’ida ne ta hanyoyi biyu.  Hanyar farko ita ce, za ta baka damar ganin bayanan da ke cikin ma’adar wayar salularka mai suna Memory Card.  Sannan kana iya zuba bayanai a cikinsa, ko ka goge wanda ke ciki, ko kara musu yawa.

Sannan kana iya mu’amala da masarrafar wayar baki daya, musamman wajen ganin sakonnin tes da aka turo maka kuma suke dauke cikin wayar, kana iya ganin lambobin mutane da ke cikin wayar, kana iya amfani da wayar wajen jona wayar salularka ta zama makalutun sadarwar Intanet (wato Internet Modem), don samun damar mu’amala da fasahar Intanet.  Ba nan kadai ba, duk sadda wayarka ta yi doguwar suma (Hanging), ko kwayoyin cutar kwamfuta (Virus) suka kama ta, da wannan waya ko wanin makamanshinsa za a yi amfani don kara mata tagomashi, da samar mata da wani sabon ruhi, wato Flashing kenan a takaice.  Wannan hanya ta uku kenan.

Hanya ta karshe kuma ita ce ta yin amfani da ma’adanar adana bayanai irin na wayar salula, wato Multimedia Memory Card (MMC), don loda bayanai a ciki, da kuma dora su cikin kwamfuta, ta hanyar ramin mu’amala da katin ma’adanar kwamfuta mai suna Card Reader Slot.  Ba kowa ya cika amfani da wannan hanya ba, saboda wadanda suka gabace ta sun fi saukin mu’amala, da kuma samar da fa’ida nan take.  Wadannan, a takaice, su ne hanyoyin da wayar salula ke iya amfani da su don aiwatar da sadarwa ko alaka a tsakaninta da wasu na’urorin sadarwa ko ma’adanar bayanai.

Kayayyakin Sadarwa

Kayayyakin sadarwa da wayar salula ke amfani da su don aiwatar da sadarwa guda biyu ne rak; wadanda idanu ke iya gani kenan.  Idan muka hada da masarrafar wayar salula mai taimakawa wajen aiwatar da sadarwar (wato Drivers), sai su zama uku kenan.  Amma abin da ido ke iya gani, guda biyu ne rak.  Na farko shi ne wayar da ake amfani da ita wajen aiwatar da sadarwar.  Wannan waya kuwa ita ce ake kira Universal Serial Bus Cable (USB Cable a gajarce), kamar yadda bayani ya gabata a baya. Wannan waya ce ke daukar dukkan bayanan da ake son aikawa da su ta hanyar siginar lantarki, don aika su zuwa ga na’urar da ke bukatarsu.

Sai na biyu, wato ma’adanar bayanai ta wayar salula, wadda aka fi sani da Multimedia Memory Card a Turance, ko kuma MMC a gajarce.  Wannan ma’adana ce ba na’urar sadarwa bace.  Amma ita ma tana taimakawa wajen aiwatar da sadarwa a tsakanin wayar salula da sauran kayayyakin sadarwa, irinsu kwamfuta, da wasu wayoyin da dai sauransu.

Kammalawa

Dangane da bayanan da suka gabata, za mu fahimci cewa shi aiwatar da alaka ko sadarwa a tsakanin wayar salula da wasu kayayyakin sadarwa na dauke ne da matakai guda uku.  Matakin farko shi ne tsarin sadarwar.  Mataki na biyu kuma shi ne hanyoyin sadarwar. Sai mataki na karshe, wanda ke dauke da kayayyakin sadarwar. A kasida ta gaba in Allah ya so, za mu kawo bayanai kan matsalolin wayar salula.  A ci gaba da kasancewa tare da mu.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.