Hira da BBC Hausa kan Bikin Ranar Tsaftace Intanet a Duniya (4)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 6 ga watan Maris, 2020.

267

Kamar yadda muka fara kawowa a makonni uku da suka wuce, yau ma za mu ci gaba da hirar da sashen BBC Hausa yayi dani don bikin Ranar Tsaftace Intanet a Duniya na shekara ta 2020, wanda ya gabata a ranar talata, 11 ga watan Fabrairu.  Wannan kashin karshe kenan na hirar.  A sha karatu lafiya.

—————-

BBC Hausa:  Tambaya ta karshe ita ce, taken shirin na bana shi ne: “Hada Hannu Don Samar da Tsaftatacciyar Fasahar Intanet a Duniya”.  Wace irin gudummawa kake ganin kowa zai iya bayarwa don tabbatar da hakan?

Baban Sadik:  Masu ruwa da tsaki cikin lamarin fasahar Intanet a duniya sun hada da iyaye, da ‘ya’yansu, da ‘yan uwa, da hukumomin gwamnati, da kungiyoyi masu zaman kansu, da wadanda suke da alhakin zuba bayanai a kafafen dake wannan fasaha mai matukar tasiri.  Wadannan su ake kira: “Stakeholders” a harshen turanci.  Ma’ana wadanda suke da ruwa da tsaki wajen gudanuwa da kuma aiwatar da ma’amala ko harkoki a wannan mahalli na Intanet a duniyar yau.

- Adv -

Su iyaye dole ne su lura da ‘ya’yansu, su kuma basu tarbiyya, wanda shi ne abin da yake da mahimmanci na farko.  Sannan idan suka fara amfani da wadannan na’urori da kafafen sadarwa na zamani, zama mai gansu ba – kada suce ai mun riga mun basu tarbiyya shikenan.  Dole su rika lura dasu.  Idan suka fahimci abin da suke gudanarwa mai amfani ne, to, sai suci gaba da basu shawarwari kan hanyoyin da zasu taimaka musu wajen samun Karin fa’ida da amfani.

Su kuma matasa da ke mu’amala da wadannan kafafe na sadarwa kuma suji tsoron Allah; su rika gaya wa kansu gaskiya.  Duk abin da wani ja zuwa gare shi, wanda ya saba wa irin tarbiyyar da iyayensu suka basu, to, suyi kokari su nisance shi. Su sani, wannan shi ne zaman lafiya gare su.  Duk mutumin da bai bi maganar iyayensa ba yaci ga da kutse-kutse, to, watarana zai kutsa wani wurin da idan ya shiga, bazai iya fitowa ba.  Akwai abin da ake kira da suna: “Internet Blackhole”.  Wannan kalma ta “Internet Blackhole” na ishara ne ga wani wuri mafi muni dake giza-gizan sadarwa ta Intanet.  Ba wai wani wuri bane takamaime, balle kace idan ka san wurin shikenan zaka guje masa.  Wuri ne da yafi kowane wuri hadari a Intanet.  Muddin mutum ya sake ya fada cikinsa, kuma yayi mummunar sabo da wannan wuri, to, bazai taba iya fitowa daga ciki ba har tsufa ko karshen rayuwarsa.  Kamar yadda idan mutum ya fada rijiya mai gaba dubu misali, bazai iya fitowa daga cikinta ba.  Ire-iren wadannan wurare dai sun hada da shafuka ko gidajen yanar sadarwa na batsa, da shafukan caca, da wuraren da ake ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma shafukan da ake koyon duk wani nau’i wato na zamba-cikin-aminci (“Internet scam” ko “419”) a Intanet.  Wurare ne da suka fi kowane wuri hadari a Intanet.

A bangaren hukuma kuma dole ne a ci gaba da wayar da kan jama’a, kamar yadda na zayyana a baya.  Hukuma tasan cewa al’umma fa amana ne a hannunta.  Sannan idan jama’a kansu ya waye kan wannan fasaha, za su san meye mummuna da abubuwan da suke masu amfani a wannan mahalli.  Idan haka ya samu kuwa, in Allah Yaso, yawan laifuffukan da ake aikatawa ta hanyar Intanet, irin su zamba-cikin-aminci musamman, zai ragu cikin al’umma.  Wanda daman wannan matsala na cikin abin da ke ci ma gwamnatin Najeriya tuwo a kwarya, kamar yadda tsohon Shugaban Majalisan Dattawan Najeriya, wato Bukola Saraki ya taba ayyanawa da aka gayyace shi wani taro kan samar da hanyoyin tsaron kasa a kafafen sadarwa na zamani, shekaru kusan hudu da suka gabata.  Yace Najeriya na hasaran biliyoyin naira sanadiyyar masu zamba-cikin-aminci ta hanyar Intanet a Najeriya a duk shekara.   Idan hukuma taci gaba da wayar da kan jama’a in Allah Yaso wannan zai ragu.

Sannan bayan nan har wa yau, galibin kamfanonin dake kera na’urorin sadarwa, musamman kwamfuta da wayoyin salula, kan sanya wani bangare da suke kira: “Parental Control”, wato tsarin dake baiwa iyaye damar toshe duk wata kafa da za ta iya jefa rayuwar kananan yara cikin hadari a na’urorin sadarwa.  Idan iyaye suka tsara na’urorin sadarwar da suka saya wa ‘ya’yansu gabanin su mika musu, hakan zai taimaka musu.  Su ma yara za su iya taimaka wa kansu ta amfani da wannan tsari ko wasu tsare-tsare dake dauka kan wayar salula da kwamfuta, musamman bangaren dake lura da kalmomin hani a yayin mu’amala da manhajar nemo bayanai a Intanet.  Suna iya bai wa wayar ko kwamfutar umarnin cewa duk sadda wani ko su da kansu suka shigar da wata kalma mai suna kaza, misali, kada a budo musu.  Duk da na san wannan ba abu bane mai sauki.

Idan aka bi wadannan hanyoyi da ma wasu da ban ambata ba in Allah Yaso, za a samu sauki kuma a tsira daga matsala a wadannan kafafe na sadarwa.  Allah mana jagora, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.