Sakonnin Masu Karatu (2019) (2)

Bayani Kan Yadda Za a Tsare Shafin Facebook Daga 'Yan Dandatsa.

Ci gaban sakonnin masu karatu da na samu a wannan shekara. An buga wannan bayani ne a jaridar AMINIYA na watan Fabrairu, 2019.

108

Assalamu alaikum Abban Sadik, da fatan kana lafiya.  Filinka yana daga cikin filin da nake fara karantawa a jaridar Aminiya.  Allah ya kara maka ilmi, yasa albarka a cikin al’amuranka, yasa sadik ya fi ka hazaka wajen irin wannan aikin alheri.  Ya kuma kara mana irinku a cikin al’umma, amin.  Daga Sha’aibu Garba Gurunga.

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Shu’aibu.  Ina godiya matuka da wadannan addu’o’i naka masu yawa da albarka.  Ina rokon Allah ya amsa irin wannan addu’a gareka kai ma, ya inganta iyalinka da rayuwarka baki daya.  Na gode.  Na gode.  Na gode.

Asslamu alaikum Baban Sadik, ni mabiyin shafinka ne a jaridar Aminiya.  Barka da warhaka da fatan kana cikin koshin lafiya. Don Allah ina da tambaya:  wai idan ‘yan dandatsa (Hackers) suka yi wa mutum kutse a shafinsa na Facebook suka canja masa sunan shafi, yaya za ayi ya mayar da sunan shafinsa na asali? Na gode.  Sako daga Mansur Haliru Dandin-mahe, Sokoto 09066749533 mansurhaliru@yahoo.com.

- Adv -

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Mansur.  Da farko dai ya danganci wani irin kutse suka maka?  Shin, sun kwace shafin ne gaba daya; ba ka iya hawa don ganin abin da ke gudana?  Ko kuma a a, sun hau shafin ne, suka canza sunanka, amma kuma basu canza Kalmar sirrin da kake amfani dashi ba wajen hawa?  Ko kuma sun kwace ne, amma daga baya aka dawo maka da shafin bayan sun canza sunan?  In har ba ka iya isa ga shafin saboda kwacewa da suka yi, to, a nan ka ga abu na farko shi ne a dawo da shafin ma tukun daga hannunsu kafin ayi zancen yadda za a bashi kariya nan gaba.  Idan kuma basu kwace shafin ba, sai dai sun hau sunyi aika-aika a ciki, ko kuma sun kwace amma daga baya aka dawo da shafin da karfin tuwo.  A nan ne za a yi zancen hanyoyin kariya daga sake aukuwar hakan nan gaba.

Da farko dai sai ka canza Kalmar sirrinka, wato: “Password”.  Kana iya amfani da hadakar lambobi, da haruffa, da kuma alamomi.  Kada kayi amfani da lambar wayarka musamman wanda jama’a suka sanka da ita, ko wacce ka lika a shafinka na Facebook.  Da yawa cikin mutane kan sanya Kalmar sirrinsu ta zama lambar wayar da suka yi rajistar shafin da shi.  Wannan kuskure ne mai girma.  Kwace shafi mai dauke da Kalmar sirri irin wannan bashi da wahala ko kadan.  Kamar ka gina gida ne, ka sanya masa makulli mai kyau da inganci, amma sai kaje jikin kofar gidan ka rubuta cewa, ga yadda ake bude gidan nan, cikin sauki.  Bayan ka canza Kalmar sirrinka, sai kuma ka canza sunanka.

Dukkan wadannan abubuwa za ka yi su ne a bangaren tsare-tsare, wato:  “Settings”.  Idan a kan wayar salula kake hawa shafin naka, da zarar ka hau, sai kaje bangaren dama daga sama, za ka ga wasu alamun layuka guda uku.  Idan ka matsa za a zarce dakai jerin bayanai daga sama zuwa kasa.  Daga cikin bayanan za ka ga “Settings”.  A nan ne za ka asalin sunan da aka sa.  Sai ka latsa wajen ka canza zuwa sunan da kake so.  A gefen hagu kuma za ka ga bangaren “Password”, sai ka shiga don canzawa.

Wannan shi ne dan abin da zan iya cewa.  Allah sa a dace, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.