Tasirin Killace Jama’a Sanadiyyar Cutar COVID-19 Ga Kamfanoni da Kafofin Sadarwa na Zamani a Duniya (1)

An buga wannan makala ne a Jaridar AMINIYA ta ranar Jumma’a, 29 ga watan Mayu, 2020.

88

Sabuwar Duniya

Daga cikin abubuwan da suke hakika kuma ba su canzawa dangane da rayuwar wannan duniya dai shi ne, rashin tabbatarta akan yanayi daya.  Tun sadda cutar COVID-19 ta fara yaduwa daga kasar Sin cikin watan Disamba, 2019, tsari da kintsin duniya suka canza baki daya. Hakan ya canza tsarin alakoki tsakanin mutane, da kasashe, da kuma abokan hulda.  Wannan ya haddasa samuwar dokikin hana fita karkashin yanayi daban-daban; ya danganci kasar da ka samu kanka a ciki.  Mafi girman tasirin yaduwar wannan cuta dai yana bayyana ne a manyan bangarori guda biyu.  Bangaren farko shi ne bangaren kasuwanci.  Inda da yawa cikin kamfanonin kasuwanci da masana’anta da kananan sana’o’i suka dibga, kuma suke kan dibga hasara sanadiyyar karancin ciniki da abokan hulda, da kuma yadda hankalin kowa ya koma kan abubuwan masarufi – abinci, da abin sha, magani da wurin zama.

Da dama cikin kamfanoni sun kwamfuta dama; ba za su kara farfadowa ba ko bayan gushewar wannan cuta.  Wasu kuma za su hade ne, su dunkule wuri daya.  A yayin da wasu kuma suka kara samun kuzari da yaukin aljihu.  Hausawa na cewa: faduwar wani tashin wani.  A wannan mako in Allah Yaso, za mu dubi tasirin wannan cuta da abin da ya haddasa na zaman gida, ga wasu daga cikin manyan kamfanoni da kafofin sadarwa na zamani.  Shin, riba suka ci, ko faduwa?  Meye dalili?  Kuma yaya tasirin wannan yanayi da aka shiga zai kasance nan gaba, musamman ganin cewa har yanzu ana fama da yakar wannan cuta a kasashe da dama.

Alphabet Inc. (Google)

- Adv -

Daga cikin manyan kamfanonin sadarwa na zamani a duniya akwai kamfanin Alphabet Inc, wanda muka fi sani da “Google”.  Wannan kamfani ya mallaki hajojin kasuwanci a fannin sadarwa da dama.  Kama daga manhajar neman bayanai (Google Search), da manhaja kuma gidan yanar sadarwar bidiyo (Youtube), da babbar manhajar wayar salula mai suna Android da sauran makamantansu.  Bayanan kasuwanci a marhalar  farko na wannan shekara (First Quarter) sun nuna kamfanin ya samu karuwan kudaden shiga da kashi 13 (13%), inda yayi cinikin dalar Amurka biliyan arba’in da daya da miliyan dari biyu ($41.2bn), ya kuma ci ribar dala biliyan shida da miliyan dari takwas ($6.8bn).  bangarorin da kamfanin yafi samun ciniki dai sune: Youtube, inda ya samu dala biliyan hudu ($4.4bn) wanda ya haura cinikinsa na 2019 da kashi 33%, da manhajar ma’adanar tafi-da-gidanka (Cloud service), inda ya samu karuwan kwastoma sama da kashi 55%.  A manhajar Google Meet, wanda manhaja ce da ake amfani da ita wajen hirar bidiyo da shirya tarurruka daga nesa, kamfanin yana samun karuwar masu rajista sama da miliyan 3 a duk yini.  Wannan ke nuna tasirin zaman gida da jama’a ke yi kan wannan manhaja, inda suke yawaita amfani da ita wajen sadarwa tsakaninsu da ‘yanwa da kuma abokan huldar kasuwanci.

Duk da cewa shafin Google kamfani ne na kasuwanci tallace-tallace (advertising company), wanda kuma ta nan ne yafi samun ciniki da riba, amma a wannan karo, sanadiyyar shiga wannan yanayi, cinikinsa ya ragu matuka, idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.  Dalili kuwa shi ne, galibin kamfanoni da masana’antu sun kulle, musamman a kasashen Turai da Amurka.  Don haka babu tallace-tallace da suke bayarwa.  Su ma sunyi hakan ne don rage hasara.  Domin bincike da aka gudanar ya nuna cewa galibin kamfanoni da masana’antu sun rage kudaden da suke kashewa wajen tallace-tallace a intanet da kashi 33%, yayin da suka rage wanda suke kashewa a tallace-tallace a kafafen sadarwa na zahirin rayuwa da kashi 39% cikin 100.  Wannan yasa kamfanin Google yace zai dakatar da daukan ma’aikata har sai abin da hali yayi.

Microsoft Inc.

A nasa bangaren, kamfanin Microsoft ya samu karuwar ciniki da kashi 15, sama da na kamfanin Google kenan.  Hajar da tafi samun karuwar kwastoma ita ce manhajar ma’adanar tafi-da-gidanka, wato: Microsoft Cloud Service, wacce ta kunshi masarrafai irin su: “Azure”, inda aka samu Karin kashi 59% na kimar ciniki a wannan marhalar kasuwanci.  Sauran hajojin da aka samu Karin ciniki dai sun hada da “Office 365” – hadakar manhajojin rubutu da sarrafa bayanai (Office Word, Excel, PowerPoint dsr), inda aka samu kari da kashi 25%.  Sai manhajar LinkedIn, da aka samu Karin kashi 21% da kuma tsarin ma’adanar tafi-da-gidanka, wacce ka cafko dala biliyan goma sha uku ($13bn).  Wannan adadi na kudi dai kari ne kan cinikin da kamfanin yayi a marhalar kasuwanci na shekarar 2019 da kashi 39.  Daga cikin manhajojin da suka samu tagomashi dai akwai Microsoft Teams, manhajar hirar bidiyo da shirya taruka ne.  Wannan yanayi na zaman gida aka shiga yayi tasiri wajen yawaita amfani da ire-iren manhaja, musamman a tsakanin malaman jami’a da kananan kamfanoni da masana’antu.  Hatta ni ma nakan yi amfani da ita wajen halartar tarurrukan wayar da kai na ilimi.  Misali, a makon jiya na halarci taro na musamman don kaddamar da littafi kan tasirin annobar Corona ga tattalin arzikin kasar kasashen hadin kan musulmi na duniya, wanda ya gudana a kasar Malesiya.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.